BABI NA TALATIN DA SHIDDA

10K 975 322
                                    

Doctor Hamza tare da wasu abokan aikin su, da wasun su ke a zaune wasu na tsaye daga cikin ofishin shugaban su kuma tsohon malamin wasu daga cikin su a zamanin karatu , Professor Talba Garkiɗa,

A zahiri a nutse yake ya bada hankalin sa da ƙululun idanun sa bisa kan Prof wanda ya dilmiye sosai cikin yin bayanai game da cutar da take damun matar dake cikin mawuyacin hali a ICU da jagorancin duba ta ke a hannun mutane huɗu daga cikin su .

Sai dai a baɗini cikin hankalin sa sam babu nutsuwa , babu jin daɗi bare kwanciyar hankali a tun jiya da ya amsa ƙiran prof .

Nisawa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke ƙara ƙuntata , wai shikenan domin Ubangiji Allah yayi umarni 'ya'ya su bi iyayen su sai kuma su iyayen suyi amfani da wannan dama wajen cusgunawa 'ya'yan su ?

Ah cusgunawa mana , idan ba dai Baba ya so sanya shi a tsaka me wuya tare da damal-mala masa ginin tsarin rayuwar da ya riga ya tsarawa kan sa ba wanne dalili ne zai sa shi ya ɓaɓ-ɓako masa da maganar ƙarin aure ?? Wai fa ƙarin aure ? Shi lamarin ma har kawo yanzu mamaki yake bashi , yana tantamar anya ma kunnuwan sa sun ji zancen a dai-dai ?

Idan ya tuno da yadda kalaman suka fito daki-daki tare da sake jaddadawa akan babu shakka umarni yake ba shi har ma kuma ya riga ya sama masa matar , sai ya ji wani mololon baƙin ciki ya tokare shi , shi fa ba yaro bane yanzu.

Shi kenan haka zai yi rayuwar sa tare da mata har biyu da ba zaɓin sa ba a matsayin matan sa ? Safiyya da kan ta ba zaɓin sa ba ce , aure ne mai kama da na dole aka liƙa masa shi kuma ya sa hannu dole ya amsa daɗi da ƙarawa lokacin yana a tsakiya da jin takaicin ɗiya mace , domin haka yasa shi gaza musantawa .

Yanzu kuma da yake ɗan lallabawa da Safiyyan da daɗi ba daɗi suna zaman su tana faran ta masa dai-dai gwargwado shine kuma za'a sake bijiro masa da wani auren ? To a dalili da me ? Shi a tsarin rayuwar sa babu saki ba kuma gurbin mata biyu .

Mace ɗaya tal ta ishe shi ,shiyasa ma ya bada kai yana lallabawa da wacce ta zama ƙaddarar sa , rabon sa duk kuwa da cewa ba zaɓin sa bace .

to yayi yaya da mata biyu ? Jera su zai yi yana kallo ? Ko kuwa a wuya zai rataya su yana yawo da su suna reto ? Ɗan tsaki ya saki a hankali .

Lokacin da ya fahimci professor Garkiɗa ya kammala jawabin sa ba tare da shi ya fahimci kome ba , alhalin kuma musamman yayi tattaki ya zo domin ya saurari koyarwar duk da cewa kusan abunda ya riga ya sani ne zai sake sanar da su , to amma shi ai maye ne akan neman ilmi kome ƙanƙantar sa , hakan ya sa shi yin zarra a cikin abokan aikin sa masu matsayin karatu irin nasa ,

Ai ga irin ta nan tun kafin a je ko'ina ya fara sururucewa akan tunanin rayuwa da mata biyu , anya kuwa zai iya ?

Miƙewa yayi yana jin takaicin rashin saurarar koyarwar da prof yayi musu .

Bayan fitowar su daga ofishin suka tsaya shi da abokin aikin sa suna tattaunawa .

Mata biyu ne suka doso wajen hannuwan su riƙe da kayayyaki , kondunan zuba abinci da wasu tarkace ,

Karaf idanun sa suka sauka akan matar rannan ,

Tun a ɗan nesa yake nacewa kallon kamannin ta da ke kamanceceniya sosai da na Khaalty Rahima , ba su da wata maraba , sai tsabar tsufa da wani irin duhu da wannan tayi marar kyaun gani,

tabbas ko da khaalty Rahima na raye bai ci ba ace tayi wannan tsufan, dududu shekaru biyar zuwa shidda ta ba shi ,

Bai farga ba suka gota shi , da sauri ya bi bayan su ba tare da yayi sallama da Abokin sa ba
Yana son sanin wacece ita , ?

Sallama ya dunga rangaɗa musu har baki biyu babu wacce ta juyo a tsakanin su sai da yayi ta uku ,

Ɗayar kakkaurar matar baƙa gajera ta juyo ,
" Au nan ne ? Da mu ne ? Ca nake a iska nake ji ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now