BABI NA SHA HUƊU

6.6K 497 25
                                    



Babban Barikin soja dake tsakiyar birnin maiduguri nan direban youssouf ya dakata ,

Karo na uku biyamuradi youssouf yana yunkurin faɗawa takwaran aikin sa kuma sabon aboki agare shi wanda ya kasance babban sojan nigeria mai matsayi irin na biyamuradi ( colonel ) amma sai ya ji ya kasa , saboda shi da kan sa yana jin kunyar mummunar ɗabi'ar sa duk da cewa kusan hakan ba bakon abu bane wurin su soji , amma yadda yake da kamala da nutsuwa a zahiri ,uwa uba kasantuwar sa ɗan nasaba da akan san su da kyaun tarbiyyah , tashin farko zai yi wuya ayi hasashen yana kurɓar burkutu ,"

Sake ƙutawa yayi a karo na barkatai yana me jin duk ya gundura da hirarrakin da abokin nasa mai suna "colonel nuhu " yake yi masa , ya kai ɗan yatsan sa ɗaya gami da sosa ƙeyar sa .

Taɓo sa nuhu yayi lokacin da ya lura baki ɗaya youssouf ɗin bai bashi amsar hirar da yake yi masa tamkar ma hankalin sa bai tare da shi yayi zurfi cikin tunani .

   Abokina yaya dai ?
   Meye yake damun ka haka da har ka zurfafa cikin tunani ?

Ɗan ƙaramin tsaki youssouf ɗin yayi kafin ya ce

Bari kawai abokina akwai abun da nake bukata ne ,

Wani shu'umin murmushi nuhu yayi domin shi tun tuni ya harbo jirgin youssouf ɗin duba da yadda duk yake a birkice ga fuskar sa da take bayyana matsanancin halin da yake ciki ," amma dan ya sake tabbatarwa tare da son ya tsokani youssouf ɗin ganin kamar yana son boye masa cikin sa , ba tare da ya san shi da shi dukkanin su ƙwaryar sama da ta ƙasa ne ( duk kanwar jaa ce )

Me kake bukata haka abokina ??

Ɗago kan sa yayi da yake a sunkuye ya wara idanun sa da suka sauya launi zuwa jaa yana jin yadda nawin da ya tokare shi a kirji akan rashin samun kurbar burkutun yana sake ƙaruwa ta yadda yake jin tamkar matse masa jikin sa ake da dukkanin hanyoƴin jinin sa ," cikin wata irin sarƙaƙƙiyar murya yace ,"

   Burkutu ," Burkutu zan sha nuhu ,' dan Allah ka taimaka ka kaini inda zan samu burkut da farko , zan yi maka bayani daga baya ," 

Wata shu'umar dariya nuhu ya kwashe da ita ,'

haba abokina ai ba ma sai ka min wani bayani daga baya ba duk su biyun za'a tanadar maka a lokaci guda , kaga daga ka gama kora ruwa sai kuma a faɗa harka ,"

Shi dai biyamuradi youssouf bai ce kome ba hasalima bai kai gano ba cikin kalaman nuhu illah kawai ya ji ya fara samun nutsuwa tun da nuhu ya ce zai samar masa da abun da yake muradi ,"

Direban sa yayi niyyar kira amma sai youssouf ɗin ya dakatar da shi tare da faɗa masa shi yana bukatar sirri ne dan haka so yake su tafi su biyu kawai ', a cikin ran sa yana ƙudurtawa zai sanya ido sosai ya gane hanyar domin duk lokacin da ya bukata kawai ya tafi shi ɗaya ya shaa abar sa ba tare da rakiyar kowa ba , ba kuma tare da kowa ya sani ba. ( mai kowa me kome ya sani kuma yana ganin ka youssouf amm )

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now