BABI NA SHA BIYU

5.2K 539 52
                                    

Cikin hanzari ya raba ta da cikin jikin sa ya sauya mata matsaya zuwa bayan sa lokaci guda ya sa kafa ya kaiwa bakin "karyar" duka ,a dai-dai lokacin da tayi nufin kaiwa ledar hannun yakaka wawura ,wanda hakan ya sa yakaka ta sake riƙe bayan rigar sa tamau tana me sake mannewa da jikin sa cikin karkarwa tare da runtse idanun ta ,batare da tayi la'akari da kyau gami da hasken lallausan yadin jikin sa ba ,

Ke dallah Sakar min riga koh bakya gani karnukan sun gudu ne ??

Cikin hanzari yakaka ta buɗe idanun ta da suke runtse tare da sakar mishi riga gami da matsawa daga jikin sa kunnuwanta suna jiye mata kamar ta san muryar sa .

Ba tare da ya waiwayo ta ba ya cigaba da takun sa da nufin cigaba da tafiya inda ya nufa ,

Bayan sa ta bi da kallo bakin ta na son furta masa kalaman godiyar taimakon da yayi mata ,

idanun ta suka sauka a dai-dai inda ta kama a jikin rigar sa har zuwa ƙasa baki ɗaya ya baci da jar miyar da tasha gumurzu da karnai akan ta ,"

Zaro idanuwan ta tayi lokaci guda ta buɗe ƴar muryar ta ,"
Malam , malam
Ta kira sa
Waiwayowa yayi yana me sake tamke fuskar sa ,
Karaf suka haɗa ido , kallon-kallo suka yi yayin da idanun su suka sarƙe cikin na juna a karo na biyu ,

Kowannen su zuciyar sa ta buga da mabanbanta yanayi.,"

Yakaka tayi saurin janye ƙwarar idanun ta lokaci guda mabayyanin bacin rai yana samun matsuguni akan ƴar fuskar ta a saboda hoton cin zarafin da yayi musu ita da kanwar ta da ya gifta ta cikin zuciyar ta a take ,"
Haɗiye kalaman godiya da ban hakurin bata masa riga da tayi niyyar yi tayi ,domin a ganin ta wannan mutumin bai dace da samun tattausan kalamai daga gare ta ba .

Cikin sauri ta taho kan ta a sunkuye ta kewaye shi , cikin dakewar zuciya ta sake nufar hanyar da ta billo daga kan ta ba tare da ta sake yadda ta dubi sashin da yake tsaye ba .

Tare da wani irin yanayi da yake ji daga ƙarƙashin zuciyar sa wanda ya kasa tantance wanne iri ne , ya bita da kallo , chan ƙasan zuciyar sa wani ƙaramin sashi yana mararin sake duban cikin ƙwarar idanun ta ,

wanda a zahiri bayan ƙwarar idanun nata da suke da wani irin maganaɗisu a gareshi babu wani abu da zai iya ɗorarwa na daga kammanni koh suffar yarinyar illa ma , ƙyama da haushin ta da yake ji tun a ranar da ya fara yin tozali da ita ,dan haka yanzu ma sashi mafi rinjaye na zuciyar sa danasanin taimakon ta da yayi yake , har ma yake kitsimawa cikin ransa da ace ya san ita ce da ya bar karnukan nan sun chasaa ta yadda ya kamata ,"bagidajiyar wofi ƴar ƙauye " ya karasa tunanin sa yana mai fidda sautin dogon tsaki ,"mtsww"

Cikin taka tsan-tsan tare da taraddadin sake gamuwar ta da rundunar karnuka take ratsa layukan da nufin komawa kan hanyar ta da ta biyo domin ta samu damar nufar wurin da ta bar falmata ,

sai dai abun da ya firgita ta shine bacewar da tayi ta gagara gane hanyar da ta biyo .

Bulayi ta dunga yi ,ta bulla ta chan ta bullo ta nan gabakidaya kan ta ya juye ta samu makuwa ,

Cikin rishin kuka ta ɗaga kai tana kallon ruwan saman da ya fara sauka da matuƙar karfi , yayin da mutane kowa ya fara neman mafaka .

Share hawayen ta tayi tana me ƙanƙame jikinta saboda dukan da ruwan ya fara yi mata ,

sake mikawa tayi ta nausa inda take tunanin zai sada ta da bakin hanya ,idanun ta koh gani sosai basa yi saboda ruwan hawaye da karfin ruwan saman da yake sauka bisa fuskar ta .

Dai-daita tsayuwar motar sa yayi a gefen hanya saboda karfin ruwan da yayi yawa tare da ƙuncin da ya cika masa zuciya sun haɗu sun hana shi samun damar da zai jaa motar sa ya ƙarasa barin unguwar da yake ƙi fiye da kowanne bigire cikin duniya wanda kuma shigar sa unguwar ya zamar masa dole saboda dalili mai karfi .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now