BABI NA ARBA'IN DA HUƊU

6.9K 736 163
                                    

Cikin motar ƙirar Golf 2 Wagon da take shilla gudu akan titin da zai sadu da jahar Tahoua .

Falmata ce a zaune daga kujerar da take daura da Direban da bakinsa yake cike da goro ,  yana ta bin wakar Sa'adu bori mai taken 'soyayya abun yi ce ,da take tashi ta cikin sifikun motar kamar zai fasa mata dodon kunne ,  ta  kare fiye da rabin fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar jikinta da ta sanya hijabi a madadin sa

Ita ɗaya ce ƙwal mace a cikin motar sauran mazauna gidan baya na motar duk maza ne matasa majiya ƙarfi

***

Lokacin da ta samu isa tashar mota na birnin Niamey da misalin ƙarfe biyar da rabi na asubahi , babu yawaitar mutane a tashar da kyar ta samu wani dattijon ɗan kamasho inda ta shida masa Maidugurin Jahar Bornon Nigeria take son zuwa ,

A mamakance dattijon yake kallon ta , kafin yace mata ,

"kai tsaye Borno zaki tai dagga nan yarinya ?ko dai Sokoton Nigeria zaki tai dagga nan , a can kuma ki tai Borno ?

"Maiduguri zan tafi daga nan Baba, dan Allah ka kaini motar da zata tafi can .

ta bashi amsa tana share ƙwallar da taƙi tsayawa a idanunta ,

Da sauri ya tare ta da cewa ,

"a ah yarinya batun ba na kuka bane kin ga itta motar Borno dagga nan ai wahala take batta samuwa haka a sauƙaƙe , sabadda Borno daga nan tahiya ce miƙaƙaƙƙa ya ta mai yada shege , sai kin tai zouwa zender dagga nan ki shiga ta diffa kafin ki tsallaka boda ki shiga yankin Mobar ta jahar Bornon Nigeria , anya yarinya kina mace budurwa ɗanya shakaf kya iya wagga tahiya ta mazaje ?

" zan iya Baba , Allah zan iya , zan tafi ga taimaka min .

Tace , zuciyarta na sake haƙaƙewa kan tafiyar ita ce kaɗai mafita a gareta ,

" to babu laifi , bara shi malam Amadou gayu ya isso domin shi ɗai yake wannan dagon zagon Allah sa dai ƴan tangaran basu riga sun kama kujerun motar ba , dawo dagga nan ki zauna , nan ba da jimawa ba ike isowa ,

A ɗarare ta zauna akan wani ɗan dandamali ba dan ranta ya so ba domin a matse take ƙwarai da ta bar yankin ,

Zaman mintoci goma kawai tayi sai ga motar Ahmadou gayu , wata wankakkiyar golf wagon ce da ta ci uban dilken da ake yiwa tsoffin motocin da ake son tada musu da komaɗa tare da ɓoye musu tsufan su .

Tayi zaton za ta ga wani matashin saurayi jin ana masa inkiya da "gayu , sai ta ga wani dattijon da ya tasamma shekaru sittin amma ya ƙi sarewa daga yin gayu domin kuwa a tsuke yake cikin ƙananun kayan da suka ɗau guga , ya ci zanzaro ,  kan nan nasa da sanƙo ya cinye rabi rabin kuma gashi ne a tare himili guda da aka yiwa shamfo a taje tsaf-tsaf yana sheƙin Mai .

Da fitowar sa gurin ya ɗau ƙamshin ƙaƙƙarfan turarensa na 999 for male .

Bai jinkirta ba ya fara goge jikin motar da a zahiri babu wani datti sai ƴar ƙura da ba'a rasa ba ,

Ɗan kamashon nan shi yayi sauri ya samar mata wajen zama domin kuwa , kamar yadda yayi zato har an riga an kama kujeru huɗu na bayan motar ,wajen mutum ɗaya tak ya rage ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now