BABI NA ISHIRIN DA DAYA

6.6K 569 148
                                    

A tsorace suka juyo , yakaka tayi arba da wani mutum jikin sa sanye da shuɗin kaya hannun sa ɗaya rike da wani ƙaton kulki , gefen sa kuwa wannan mutumin da take zaton sun yi masauƙi a bakin shagon sa ne

Nan take ran ta ya aina mata , ", ya ƙira musu jami'in tsaro ne ," dan haka ta matso falmata gami da sake riƙe hannun ta ƙam-ƙam ,

Daga chan inda yake tsaye yace !
Su waye ku ?
Kuma daga ina kuke ?
Meye kuma kuke tafe da shi a baccon hannu ku ?kuyi gaggawar sanar da mu kafin naje na kira sojoji .

Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .

Mu mune su falmata kuma mu ƴan gudun hijira ne daga ƙauyen mairambiri , kayan mu ne a cikin bacco .
Falmata ta amsa musu cikin dakiya .

Wanne irin kayan ?

Kayan sawar mu .
Suka haɗa baki wurin amsa masa !

Ku buɗe mu gani ?

filla-filla suka yi da suturun nasu , ba tare da gardama ba .

Meyasa kuke yawo da kaya ? Ina ne sansanin ku ? Bai kamata kuna yawo da jakar bacco ba saboda kun san halin da gari yake ciki ba'a yadda da duk wani mutum da aka gan shi da kaya niƙi-niƙi kuma yana nuƙu-nuƙu a cikin taron jama'a bare ma ku yara mata ga kuma irin yanayin ku , kowa ya gan ku dole zai zarge ku har ma ya tsora ta , saboda yadda mafi yawancin lokaci ake amfani da ku ta hanyar rataya muku nakiyar bam ku shiga taro ku tayar ,

Ku godewa Allah ma lokacin da na gan ku a bakin shago na ba jami'an soja ko na ɗan sanda na kira ba mai gadin kasuwa ne , da ace ɗaya daga cikin jimi'an tsaro ne da sai sun hukunta ku dan haka nake baku shawara da ku koma sansanin ku , ku ajiye wannan jakar kayan naku sannan idan ma zaku shigo gari harkokin ku sai ku shigo , yawon ku a haka hatsari ne ga rayuwar ku ,!

Duk wannan dogon bayanin da mutumin nan yake musu yakaka ta zurfafa cikin tunani , jin ya ambaci komawar su sansanin ƴan gudun hijira ,"
Cikin ran ta ta ƙudurce baza su koma sansanin su ba , saboda tun bata tare da ciki ma ƙuƙaƙƙiyar wahala ce zaman sansani ƴan gudun hijira , sanan ga tozarci uwa uba fyaɗe da ake yi wa mata , to bare fa yanzu da take ɗauke da cikin da bashi da uba , ta koma sansanin su a gan ta da ciki ,? Tace aina ta samo shi ? Alhalin duk wanda ya san ta ya san ta ne a matsayin budurwa wacce bata taɓa aure ba ,

ai ta tabbatar fanne baza ta bar ta ta kurɓi ruwa ba zagi da aibatawar da zasu dunga mata sai ya samar mata da cuta , dan haka gara sun hakura da zaman sansanin sun nemi wani wurin fakewar ,"

Da wannan tunanin ta ɗago kan ta ta dubi mutumin , da taji falmata na bashi amsa da cewa

Sun ɓata ne sun kuma manta sunan sansanin su .

Malam dan girman Allah ka taimaka mana ka samar mana da wurin da zamu dunga kwana , " bamu da kowa a garin nan mamar mu da ƙannen mu sun ɓata tun a ƙyauyen mu baban mu ya mutu , mijina ma ba'a san inda yake ba ,"
Ta ƙarasa zancen tana mai sunkui da kai domin gujewa kallon rashin yadda da wannan mutumin yake jifan ta da shi ," cikin ranta kuwa kunyar sabuwar ƙaryar da ta gilla take yi ,

Saitin inda take jin tashin sautin muryar yakaka , falmata ta maida fuskar ta , cikin ran ta tana mamakin yaushe su duka suka koyi ƙarya ? ?

Shiru yayi yana nazari , kwarai zai so ya taimakawa yaran ko dan kasancewar su mata , duk da cewa cikin ran sa ba wai ya gama aminta da zantukan su bane gaba ɗaya ,

toh amma shi ya san ba ƙaramar fitina zai tadawa kan sa ba muddin ya ɗauki yaran nan ya kai su gidan sa ya jefa su tsakanin matan sa uku ," yana da tabbacin sai an dafa su da ran su , shi kan sa ruwan gidan sai ya gagare shi shaa da kwanciyar hankali , dan haka da muguwar rawa gamma ƙin tashi .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now