BABI NA ASHIRIN : INA MAFITA

8.9K 538 95
                                    

Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa'ar samun kofar ɗakin ta a buɗe kai tsaye ta danna kai cikin ɗakin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ,"

Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci .

Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ," 

Da sauri ta zo ta kama ta

Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ?

Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,
  Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,"ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,"ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ," INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI,"

Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,"

   Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati biyun ce har kananan ƴan iskan nan da nake raba ki da su suka samu damar hure miki kunne ,ah lalle fa ga ki kuwa kin sauya kin yi lumui lumui kin cika kin yi clean , hala saurayin naki mai ɗan gwaɓi-gwaɓi ne naga ya wanke min ke , ah toh ai babu laifi tun da mai maiƙo ne ,"
      shi ya baki wannan kuɗaɗen kenan ? ," ta furta hakan tana mai bin kuɗaɗen da kallo , " idanun ta suka sauƙa kan ɗan wani hoton fasfo wanda ga alama daga tsakanin kuɗin ya fito , ta kai hannu gami da ɗaukar hoton ,
      Hoton sa ne sanye da kakin sa na soji daga kirjin sa zuwa fuskar sa ," kallon hoton tayi da kyau tabbas ta san shi abokin saurayin ta nuhu ne ,'bata manta ba nuhu ya bata ɗan takaitatcen tarihin sa a wani yammaci da taje bariki wurin nuhu ta tarad da youssouf ɗin , bayan tafiyar sa take tambayar nuhu  yaya ta ga launin uniform ɗin su ya banbanta ? Nan ya shaida mata youssouf sojin niger ne , ya ɗora da bata labarin sa kar ki gan shi haka anan fitattace ne a ƙasar su ɗan sarki ne , yarima ne mai jiran gadon birnin maraɗi ,babbar masarauta ce a niger ,"

     Yaks wanene wannan ?? Ko shine masoyin naki ?

Da sauri yakaka ta ɗago kan ta domin ta ga wanda samy baby take kira da masoyin ta ,
    Idon ta ya sauka akan ƙaramin hoton biyamuradi , da sauri ta kaiwa hoton chafka !
     Shine wallahi shine , ina son shi dan Allah anty idan kin san shi , ki kai ni wurin sa ,"

   Cikin mamaki samy take yi mata kallon kan ki ɗaya ?
   Ke yaks wannan ne saurayin ki ? Kar ki min ƙarya , gaya min ta yaya ya zama saurayin ki ?

    Yakaka bata boye mata kome ba daga ranar haɗuwar su ta farko da youssouf zuwa yau ,"
       Jinjina kai samy bby tayi bayan ta gama jin bayanin yakaka da ta tabbatar ba ƙarya bane ,! Domin ta san goge yaks a ɗan ƙaramin lokaci ta zama fes yadda ta gan ta sai mai kuɗi ,

Idan kuwa hakane babu shakka tayi farincikin ƙulluwar alaƙar sa da yakaka , daman irin namijin da take mata hange kenan wanda zasu tatsi arziki daga jikin sa  !tab , ai batun yace ya rabu da yakaka ma zancen iska ne , wasa tsakanin sa da yakaka yanzu aka fara , zata yi duk yadda zata yi taga mu'amalar sa da yaks ta ɗore , har sai ya gama wanke yaks ya zamar da ita mace mai aji yadda baza ta yi wahala ba wurin samun irin sa ko ma wanda ya fi shi koh da shi ya zo ya bar ta , ! Ai da ruwan ciki akan jaa na rijiya ,' idan yaks bata wanku ba ina zata samo masu attajirai irin wanda take buri???

      Share hawayen ki yaks idan wannan ne na san shi abokin saurayi na ne , duk inda yake sai na nemo miki shi , kin ji ? Bai isa ba ya wurgar da ke bayan ya morewa ƙuruciyar ki , dole ya zo ya ƙarasa aikin da ya fara ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now