BABI NA ARBA'IN DA UKU

8.3K 794 329
                                    

Ƙiran wayar Youssouf da aka yi ƙarar ita ta ratsa shiru mai ɗauke da tashin hankalin da ya biyo bayan martanin Yakaka ,

Baya cikin nutsuwar sa ya dubi fuskar wayar da take riƙe a hannunsa , ganin wacce take ƙiransa ya sa zuciyar sa ta tsinke ,

Hannunsa na rawa ya ɗaga ƙiran wayar da ya zarce da sanya ta a hands-free batare da ya ankara ba ,

Muryar Hajja ciki kuka ta karaɗe falon , da take cewa

"Babban soja , ku zo Dan Allah, ku zo wajen Mama ku ga jikin nata , jikin Mama babu daɗi...

Rige-rigen ficewa daga falon aka yi tsakanin Youssouf ,Yakaka da Falmata  da babu wanda ya saurari kansa bare waninsa burin su kawai su isa wajenta ,

Kuma a tsakanin Falmata da Yakaka babu wacce ta nufi motar Youssouf da ya shiga ya tayar dukkanin su biyu kai tsaye mafitar gidan suka nufa ,

Suna fita ya sha gabansu da Motar ,"ku shigo ,
  Yace da wata irin murya

Dukkanin su a lokacin ganin Mama shine burin su , dan haka suka shiga motar ya jaa da gudun gaske ,

A lokacin hawayen fuskar Yakaka da Falmata sun ƙafe kamar yadda yawun bakin su ya ƙafe ya daƙile fitowar wata kalma daga gare su , bayan addu'o'i babu abunda kowannen su yake yi a zuciya

Suna ficewa daga layin gidan motocin da suka yi jerin gwano su kimanin guda biyar suka shiga layin .

Gudun da yake yi ya wuce ka'idar tuki , kiyayewar Allah kaɗai ta kai su asibitin , ba inda ya kamata ya ajiye motar ya ajiye ba , bai ko lura da securities da suke masa magana ba , ya fito daga motar sauƙar ƙarfar sa akan titin da ya ɗau zafin rana shi ya ankarar da shi cewa fa ko takalma babu a ƙafafunsa ,

da gudu-gudu suka nufi ɗakin da suka san Mama tana ciki suna rige-rigen kutsa kansu ,

Turus suka yi ganin babu kowa akan gadon nata , da sauri ya fita suka bi bayansa , ma'aikaciyar jinyar da ya fara cin karo da ita zata wuce ya tambayeta ,"ina ɗiya ta ?

Ta san shi sosai a saboda yadda suke yawan zaman asibitin da kuma kasancewar sa babban Mutum , sai ta nuna musu ɗakin da aka mayar da Mama wanda yake daga ciki sosai ,

Bai saurari me zata sake faɗi ba ya nufi inda ta kwatanta masa da sassarfa ,

Bankaɗa ƙofar ɗakin yayi ya danna kai su Yakaka suna bin sa ba tare da sun bi ta kan Hajja wacce take tsaye daga bakin ƙofar tana sharar hawaye da gefen mayafin ta ba ,

Shigar su ya zo dai-dai da lokacin da likitan yake zare trach tube ɗin da yake fuskar Mama ,

Da gudu Youssouf ya ƙarasa ya ratsa ta tsakankanin Likitocin da suke zagaye da ita , fuskokin su cike da Alhini ,

Ya tarairayo ta bayan ya zauna a bakin gadon ya ɗagota lokacin da take jaan wani irin numfashi mai tafe da gurnani ciki-ciki , idanunta a buɗe akan fuskar sa  ,

Hannun sa ya kai yana goge mata tsinkakken yawun da yake zuba a bakin ta , muryar sa tana karkarwa yake kallon likitocin yana cewa,

" Doctora yaya hakka ? Kuyi wani abu mana , Mama tana hakka alhalin  kuna tsaye ?

"Mama, kar ki barni ki dubeni Mama ,

ya ƙira ta da wata irin muryar yana jijjigata a jikinsa ganin yadda idanunta suka yi sama , numfashin da take kokawar riƙewa kuma ya ƙarasa barin jikinta , dukkanin wasu jijiyoyin jikinta suka tsayawa aiki , kamar yadda zuciyarta ta tsaya chak daga barin bugawa na har abada .

Da gudu Yakaka ta ratsa tsakanin su ta kai hannu tana riƙo hannun Mama da yayi wani irin sanyi ƙalau ya sake ,

"Mama tashi mana , me ya same ki haka ? Innalillahi wa inna ilaihi raji'oon .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now