BABI NA TARA

5.8K 526 49
                                    

Misalin karfe biyu na rana ya kammala da kome da ya shafi sabon wurin da zai fara aiki inda aka tura su shi da sojojin dake ƙarƙashin sa chan tsakanin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno ,"

Karfe huɗu jirgin su na sojoji ya ajiye su a cikin garin maiduguri inda zasu kwana zuwa washegari su wuce inda suka nufa ,"

Tun isar sa babbar hedkwatar soji na birnin na maiduguri , hankalin sa ya tashi da ganin irin taron mutane maza da aka gaggarƙame cikin ɗakunan horo , a galabaice matuka , cikin azabobi da horo mai tsanani wanda a gaban idanun sa ma yaga an fidda gawarwakin jama'a daga cikin ɗakin horon da azaba ta kashe su ,"

Duk da cewa a matsayin sa na babban soja hakan ba bakon abu bane ,toh amma zuciyar sa ta taɓu da yaji daga bakin wani sojan nigeria cewa waɗannan mutanen , mutane ne waɗanda aka kama akan zargin suna da hannu wurin tada tarzomar boko haram da ba'a kai ga tabbatar da laifukan nasu ba ,sune a jibge a garƙame cikin horarwa da azabtarwa , yunwa da ƙishirwa ,rashin isashen muhalli ta yadda wasu a tsaye suke wuni , wasu a tsugunne ,wasu a tanƙware , wanda yawan su ya tasamma dubunnai ,"

Gagara samun nutsuwar zuciya yayi bayan ya koma masaukin sa ,zuciyar sa sai kai kawo take da tunanin san samar da mafita ga waɗannan bayin Allah waɗanda a zahiri akwai zalinci cikin irin wannan ajiyar da ake musu ,kamata yayi a miƙa su ga kotun ƙasa ta yankewa kowa hukuncin sa dai-dai da shi waɗanda basu da laifi a sake su , wannan hukuncin ajiye su ana gana musu azobobin da suke kai su ga rasa rayukan su yayi tsanani da rashin dacewa ,"

Har gari ya waye bai sake marmarin fita ba sai da suka tashi barin ainahin cikin garin maidugurin zuwa bakin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno , a tare da shi da tawagar sojojin su na niger da kuma ƙarin wasu sojojin nigeria , zuciyar sa cike da tausayin al'ummar da sanadin boko haram ta ɗaiɗaice suka bar ainahin cikin garin na maiduguri .

*******

Cikin kwanaki biyar ɗin da su yakaka da falmata suka ƙara cikin sansanin su basu tsinci kome ba sai tarin wahalwalun da suka sake jikkata gangar jiki da ruhin su ,"

Domin zuwa yanzu karfi da yaji su yakaka sun zama ƴan aikin matayen nan da aka haɗa su rayuwa a ɗakuna ɗaya da su,"

Ta bangaren yakaka matar da suke kwana tare wacce ake kira "fanne" ta maida ta baiwar ta wacce take yi mata bauta nata da na ƴaƴan ta , tun daga kan wankan yaran biyu har zuwa wankin bargunan su da kullum ta Allah sai yaran sun zabga fitsari , wankin ƴan tsirarun kayan yaran da koyaushe ba'a rasa shi da guntun kashi da fitsari wanda yakakan take shan wahala wurin wankin saboda rashin isashen ruwa da sabulun wankin ,uwa uba rainon yaran da suke kusan yini goye bisa bayan ta duk wata jigila da su take yi suna ɗane a baya , ta sauke wannan ta goye wancen ,uwar su kuwa tana chan cikin yaran mata tana zuba hira da ɗinkin hular ta ,"bata chas bata ass ,

Ga falmata kuwa duk da kasancewar ta miskiniya amma hakan bai sa ajus ta ɗaga mata kafa daga sanyata ayyuka ba ," tun farar safiya idan ta tashi daga kan shimfiɗar da a yanzu ita kaɗai ke kwana a cikin gidan sauron sakamakon irin azabar da take ganawa falmatan cikin dare ya sa ta hakure ta samawa kan ta salama daga ,zagi hantara ,hauri , mangari da mintsinin da ajus take buwayar ta da su cikin dare , ta bar kwana a gidan sauron ta komo bakin kofa tana shimfiɗa zanen ta tana kwanciya bisa ,"

amma duk da hakan ita ke lalubawa ta naɗe gidan sauron ta kuma ninke kayan shimfiɗun da ajus ɗin ta kwana a kai , bata bar ta haka ba kullum ita take ɗebo mata ruwan wanka a bokiti da na tsarki a buta , daga bakin famfo inda anan suke samun damar haɗuwa ita da yakaka wacce ita ma take zuwa ɗibo ruwan hidimar fanne da ƴaƴan ta , famfon baki uku ne rak da shi kuma idan aka tayar da injin bada ruwan karfe biyar na asubah zuwa karfe bakwai na safe ake rufewa sai kuma lokutan sallah da shi ma na ɗan kalilan ɗin lokaci ne sakamakon rashin man tada injin tare da rashin wutar lantarki ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now