BABI NA ASHIRIN DA SHIDDA

8.5K 618 309
                                    

Ji tayi an riƙo hannun ta ta baya , tana daf da ƙarasawa sashin doctor hamza , fuskar ta da murmushi ta juyo ga zaton ta rahima ce ,"

    Rahima , Falmata nake son na duba , kin ga dare ya fara yi bana son .....

   Sauran kalmomin ta maƙalewa suka yi a fatar bakin ta lokacin da tayi arba da fuskar samy baby a maimakon rahimar da take zato ,

    An-anty samy  ke ce ??

  Ba tare da samy baby ta saki hannun ta ba ta fara tafiya tana nufar cikin gidan da ita sashin su rahima , ba musu ta bita tana waiwayen hanyar sashin doctor hamza , da fatan ko zata hango falmata , yayin da ran ta yake cike taf da fargaban abun da samy baby zata bijiro mata da shi ,"

Waye ne a anan ?

Falmata ta furta hakan tana mai sake wara ƙwayar idanun ta ,"

Shiru youssouf yayi  tare da kafe ta da ido ,
  Watau dai ita mace kome ƙanƙantar ta mace ce ," ji wannan ƴar yarinyar ma wai dan kawai nayi mata magana shine har zata min gwalangwaso da fi'ili ta nuna ma bata ma ganni ba sam.,"  tsaki ya jaa gami da mayar da hankalin sa kan wayar sa ,

Sarai ta ji tsakin da yayi mata kasantuwar ta mai nisan ji , ko yaya abu yayi motsi tana iya ji tun daga ƙasan ran ta ," jikin ta taji yayi sanyi ," koma waye bai gane bata gani ba , " ba laifin ta bane ,"

Dan haka ta juya a hankali tana laluben jikin bango da nufin komawa ɗakin doctor hamza ,"

Kiran wayar sa da Tafeedah yayi shi ya sanya shi miƙewa bayan ya ɗaga kiran inda yake sanar da shi ya zo su tafi masallaci daga chan kuma su wuce masauƙin su sai kuma gobe su dawo ɗaurin aure !

Da sassarfa ya bar gurin da daman jin sa yake tamkar akan ƙaya !

Tsumu yakaka tayi a gaban samy baby wacce ta tsare ta da tarin tambayoyi wani kan wani ,"

Sake ɗagowa tayi a karo biyu ta dubi samy baby kafin ta muskuta cikin yin ƙasa da murya tace :
   Antƴ samy a gidan nan muke da zama ni da falmata , kuma yaya dakta shi ya kawo mu ,"
   Wanene yaya doctor ? Kina nufin likita yayan su zainab ?
Gyaɗa kai tayi
  Shi ne !
Daman ya san ku ne ? Ko ƴan uwan ku ne ??

  Kawai ya taimake mu ne bamu san shi ba amma tun farkon zuwan mu garin nan tun muna sansanin mu yake taimaka mana !

  Jimm samy baby tayi tana aunawa tare da juya zantukan Yakaka cikin ran ta ,"
   Meye tsakanin ku da shi ? Ya taɓa cewa yana son ki ne ?

Da sauri ta girgiza kan ta
  A ah ni baya so na !

Bai tambaye ki akan cikin jikin ki ba ?  Me kika ce masa game da cikin ?

Cewa yayi waye ya min cikin ? Ni kuma ban faɗa masa ba , tun daga ranar bai sake tambaya ta akan cikin ba , sai ya kawo mu gidan su nan , yace mu zauna , yana kula da mu sosai ni da falmata , har asibiti yake kai ni ayiwa baby photo dan Allah kar ki sa su kore mu anty samy bamu da wani wajen da zamu je a yanzu da ya fi nan ,
   Ta ƙarasa zancen hawayen da take tarawa a ido suna silmiyowa ,"

Guntun murmushi tayi
  Ni bazan sa su kore ku ba yaks , ki daina kuka ,!
     iyeeh watau har hoto aka yiwa baby ? kice dai kin shirya zama uwa sosai yaks
   jaan numfashi tayi kafin ta sake  wurgo mata wata tambayar da ta sa zuciyar yakaka tsalle ,"

   Ya labarin yarima uban cikin jikin ki ko har kin haƙura da neman na shi kin daina son shi saboda kin samu gidan hutu ?

  Ban - ban daina son shi ba anty samy kullum yana raina inason sake ganin sa , ban san yadda zan yi na gan shi ba ne ,! Ko kin samu labarin inda yake ?

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now