BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI ,( WASA FARIN GIRKI )

8.7K 637 145
                                    

Da sauri Doctor Hamza yake tafiya ," Amne na bin bayan sa , lokacin da suke kutsawa cikin asibitin , bayan sha da kyar da suka yi a cikin cinkoson ababen hawa da ya fara haɗuwa akan titi sakamakon kusantowar lokacin sallar juma'a ,"

Sai dai tun da ya dosa bakin ɗakin haihuwar taron mutanen da ya gani kama daga likitocin asibitin zuwa kan nurses da securities ya sa shi rage takun sa ,"

Maganganun da ya ji suna faɗa cikin harshen turanci tare da kama sunan AMINA DILMARI shi yasa shi zabura ya kutsa tsakanin su ,
What's happening/ Me yake faruwa ?
yace da su cikin wata irin muryar ,

Calm down sir , Babban likitan da asibitin yake mallakin sa yace yana kamo kafaɗun doctor Hamza ,
Muje office muyi magana ," zame kafaɗun sa doctor Hamza yayi lokacin da yake fuskantar likitan ,
Ina patient ɗina ? Yace da buɗaɗɗiyar murya , "
Shiru likitan yayi ,"
Wani irin bugu zuciyar Hamza take kamar zata fito waje ," kasancewar sa cikakken likita yasan yanayin da suke yi a duk lokacin da suke son sanar da mutanen marar lafiya wani mummunan labari game da marar lafiyan su,!

Ta mutu ?

Ya tambaya yana jin yadda zuciyar sa ke matsewa da tasowar ɗacin kalmar har akan harshen sa ,"

Da sauri likitan yace
Bata mutu ba amma zai fi kyau idan muka je nayi maka bayani a nutse.

A sanyaye Doctor Hamza ya bi bayan likitan bayan ya nunawa Amne wurin zama a gefen Falmata wacce tayi zugui idanun ta sun yi jaa sakamakon hawayen da take ta gogewa kan rashin sani halin da ƴar uwar ta ke ciki har kawo wannan lokacin ,

Mun rasa gane yadda akayi ko dalilin da yasa matar ka tare da ƴar uwar ta suka bar asibiti kuma suka bar ƴar jaririyar ta ba tare da mun sallame ta ba , sannan Alamu suna nuna kai ma baka san sun tafi ba ,"

Ɗan tsayirtawa likitan yayi yana nazarin fuskar doctor hamza wanda yayi saƙare yana kallon sa , kamar dai bai kai ga fahimtar bayanin da yake masa ba ," ɗan ƙwanƙwasa bakin biron hannun sa yayi akan ƴar takaddar gaban sa,"
Idan har an tabbatar tana gidan zamu iya sallamar ku tare da jaririyar domin ayi gaggawar sadata da mahaifiyar ta domin ta shayar da ita nonon farko ,"

Cikin jirkitattacen kallo Doctor hamza yace wacece ta gudu tare da ƴar uwar ta suka bar jaririyar ?

Tamkar dai sam bai ma fahimci bayanin da duk likitan nan ya masa ba ,"
Ba kai ne mijin AMINA HAMZA DILMARI BA ?
Maimakon ya amsa sai ya miƙe tsaye ,
Kana nufin ita ce suka gudu tare da ƴar uwar ta ?
A taƙaice likitan yace
Haka muke zato domin an duba duk inda yakamata cikin asibitin nan ba'a gan su ba , sannan masu tsaro/securities sun tabbatar mana da sun ga fitar mata biyu farare sanye da hijabai sun hau.....
Ankarar da yayi doctor hamza ya juya daga ofishin ya sanya shi miƙewa ya biyo shi ,
Wurin da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo ,"
Fatimah , kun haɗu ke da yayar ki ?
Da sauri ta ɗago kan ta !
Bamu haɗu ba Yaya dakta har yanzu ba'a kai ni inda suke ba ita da baby , ko basu da Lafiya ne ? Dan Allah ka kai ni wajen su ,'!
Wani gumi yaji yana tsatsafo masa daga illahirin ƙofofin gashin jikin sa ,"
Amne ta taso ta matso kusa da shi ,"
Ina mai jegon ne ?
wai ba'a gan ta ba yace da wata irin murya chan ƙasa , Amne dake kusa da shi kaɗai ta iya jin mai yace
Wanne irin ba'a gan ta ba inji amne ,'
Lokacin da likitan ke sake ƙarasowa tare da wasu nurses da wasu securites ,
Kuyi haƙuri sir , a fara duba gida ko suna chan , domin tare da ƴar uwar ta suka fita ,"
Wata kakkarfar tsawa doctor hamza ya yiwa likitan ,
Ka daina cewa tare da ƴar uwar ta suka fita , "
Ga ƴar uwar ta nan , ya juya yana nuno musu Falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye tana rarraba ƙwayar idanun ta da son sanin meke faruwa?
Ita kaɗai ce ƴar uwar ta , ya zama dole ku nemo ta , ba gudu tayi ba sace ta aka yi , Yakaka baza ta gudu ta bar Fatimah ƙanwar ta ba baza ta gudu ta bar baby mama ba , noorie baza ta min haka ba , ya ƙarashe da rawar murya yana jin yadda zuciyar sa ke cika da tsoron tabbatuwar hasashen mutanen asibitin ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now