ARBA'IN DA SHIDDA

9K 809 123
                                    

" Yakaka tana nan zuwa ita ma ,

Ita ce amsar da Falmata ta bawa Maman su , daga nan hira ce ta sarƙe a tsakanin su mai cike da labarin yadda rayuwa ta kasance musu bayan rabuwar su da juna .

****

Tiryan-tiryan Falmata ta basu labarin duk wasu bala'o'in da suka afku ga rayuwar su bata ɓoye kome ba illa mummunar rayuwar da Yakaka tayi da har ta kai ga haihuwar Mama da take jin har abada laɓɓan bakin ta baza su taɓa iya bayyana wannan mummunan labarin ga kowa ba .

Ta cigaba da bata labarin ɓacewar Yakaka bayan haihuwar Mama ba tare da ta faɗi ainahin silar barin su da tayi ba har zuwa kan auren su ita da Youssouf yadda kome ya wakana , da rashin lafiyar Mama har zuwa tafiyar su USA da samuwar lafiyar idanun ta , komawar su Niger da kuma dawowar Yakaka , zuwa kan Mutuwar Mama .

Shiru su duka ukun suka yi bayan gama sauraron ta , zuciyar Khaalty Rahima ta girgiza da jin yadda rayuwa tayi walagigi da 'ya'yan ta mata , tsakanin ƙarya da gaskiya , rayuwar rashin gata ta tsantsar wahala abu ɗaya ne mafi ciwo a gareta yadda duk su biyun suka auri Miji guda a wannan ƙarancin shekarun nasu , lalle wannan ƙaddara ce mai girma .

Babu wanda ya fita sanin halayyar 'ya'yan ta duk kuwa da cewa sun jima da rabuwa daga yin rayuwa guri guda , amma ai ita ta haife su dan haka ta san halin kowaccen su tun kafin su mallaki hankalin da zasu iya boye abu a ran su .

Daga zaman Falmata a gabanta kawo yanzu ta fahimci lalle akwai wata damuwa mai girma da take cinta a rai , wanda farin-cikin haɗuwar su bai sa ta manta da damuwar ta ba , ji tayi hankalin yana neman tashi , tana jin kamar akwai wani abu da Falmata take ɓoye mata da tafi danganta shi da Yakaka , dan haka ta muskuɗa tana kallon fuskar ta cike da nazari tace ,

" Falmata kin samu labarin bayyana ta ne kika zo ? Ko kuma kawai dai kin zo ne ?

Murmushin yaƙe tayi kafin tace
" Maman mu ban san kin zo ba , ban San kina nan ba, ta cigaba da cewa Mama ina Yaana da Bulama suke ? nayi kuka nayi kuka na damu akan sanin ina kike ko kina raye ko kin mutu ? shekaru suka yi ta tafiya ba tare da mun san halin da kike ciki ba , har na fitar da rai da sake haɗuwar mu a duniya , na koma yi miki addu'a iri ɗaya da wacce nake yiwa Baban mu , kan Allah ya jiƙan ku .

Ƙwallar tausayin ta ya taru a idanun Khaalty Rahima , kafin tace
" Yaana ta rasu a kan hanyar mu ta shigowa maiduguri , Bulama kuma yana nan ya girma , anjima kaɗan ma za ki gan shi ya dawo daga islamiya ,
Ta cigaba da cewa ,

" Falmata ni na wanke gawar Mahaifin ku a cikin gonar na binne shi , ban yarda gawar mutumin kirki irin sa ta walaƙanta a hannun dabbobin daji ba , bayan na koma neman ku ban same ku ba , na dawo wajen ƙabarin sa mun rayu kwana biyu ni da Yaana da Bulama ina yi ma sa addu'a , kafin mu bar gurin , Allah sarki Mutumin ƙwarai mai tawali'u Allah ya masa Rahama ,

" Amin Mama Amin ,
Falmata ta amsa tana share hawayen da suke zubo mata ,

Amnee ita ta katse musu hirar ganin duk fiye da rabin ta koke-koke suke yi da jimamin rayuwar su da ta wuce .

" Ukhtee Rahima ku bar koke-koken nan haka , Fatima mu tafi ɗaki kiyi wanka ki shirya kafin a kawo miki abinci , "me zaki ci 'ya ta ?
Ɗan murmushi Falmata tayi "kome ma zan ci , amma da zan samu tuwo miyar kuka da man shanu ,

Dariya Amnee tayi tana kama hannun ta " muje kiyi wanka ki shirya , abinda kike so shi zaki ci .

Bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da zanen da Amne ta zaɓo mata daga cikin kayan Rahima , tsumu tayi zaune a kujerar gaban madubi ,

" wani irin yanayi take ciki marar kan gado , ga dai ta a gida ta dawo kamar yadda ta zaɓarwa kan ta , take kuma ganin hakan shine zai raba ta da ɓacin-ran da take ciki , daɗin-daɗawa ma ta dawo ta tarar da farin-ciki mafi ɗaukakuwa a wajenta watau haɗuwar ta da Mama ,

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now