BABI NA SHA BIYAR

5.7K 750 52
                                    

Dafe da kirjin ta da yake cigaba da bugu ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakunan kwanan mazan sansanin su , domin haka kawai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da rashin ganin ɓullowar falmata har yanzu dan haka ta tafi domin ta taro ta su dawo tare,'

Sai dai har ta cimma ɗakunan bata ga falmatan ba , sai tsirarun mutane da suke giftawa ta cikin duhuwar ," turus ta jaa ta tsaya saƙe-saƙe ta fara yi a zuci ,"
Toh ina falmata tayi ?
Koh dai ta koma ɗakin su ne wurin ajus ?

Ganin bata ga koh alamar ta ba kuma ga shi babu wadatar kafafun mutane a wurin bare ta cigita , ga kuma duhun dare da take tsorace da shi , sai ta juyo gami da kamo hanyar komawa da nufin zuwa ta duba ɗakin su falmata ,

A sanyaye take taku saboda har yanzu zuciyar ta bata bar tsinkewa ba sai ma ƙara dukan uku uku da take yi ,"

Bata yi nisa ba ta tsinkayo wani rishi da alamun fitowar kukan da aka ƙi bada dama ya fito ,' kiƙam ta jaa ta tsaya tare da sake kasa kunne lokacin da ta sake jin irin rishin ," a firgice ta juya laɓɓan bakin ta suna furta sunan ,"Falmata"

Tayi diri-diri cikin rarraba idanun ta a kewayen wurin ,tana neman inda zata gan ta domin tabbas kunnuwan ta muryar falmata suka jiye mata ,"

Cikin rashin sanin gaba zata yi ko baya ta taka da gudu tare da hawa kan barandar wasu tsoffin ajizuwan da suke gefe da ita waɗanda kou rufi babu a kan su ta wasu wuraren ma sun fara zaftarewa da alamun sun zama kango ,"

Da gudu take shiga cikin ajizuwan tare da kwala kiran sunan falmata , sai dai bata tarar da kome cikin ajizuwan sai tarin bola tare da yanar gizo-gizo da tayi dafifi a ciki , cikin tashin hankali ta jaa ta tsaya daga karshen barandar da take daf da katangar makarantar , daddagewa tayi ta sake ƙwala kiran sunan falmatan , sai dai bata kai ga rufe bakin ta ba taji an ɗauke ta da wani kakkarfan mari , kafin ta farga taji an shatile kafufuwan ta , ta tafi ta baya ta faɗi ƙasa tare da bige ƙeyar ta da katangar makaranta ,

zuruf ta miƙe bata koh ji alamun zafi ba lokacin da tashi sautin muryar falmata ya fito tar cikin wani irin kukan wahala tana ambaton sunan ta a kurkusa da ita ,"

Taku biyu ta ƙara ta ci karo da ita a kwance cikin tarin busassun ganyayyakin da ake sharewa a tara a wurin ya zamto tamkar bolar zuba ganye ,"

Ɗago ta tayi ta tarairayo ta tare da rungumo ta zuwa cikin jikin ta tana yi tana waige-waigen jin ta inda waɗan da suka bige ta zasu bullo wanda take da tabbacin sune suke shirin cutar mata da falmata cikin ran ta tana jin karfin yin ɗauki ba daɗi da ko su waye domin ta tseratar da falmata ,"

Tunanin ta ya tsaya chak ! Lokacin da ta ji gaba ɗaya kukan da falmatan take yi ya gauraye da wani irin numfashi tamkar na me shiɗewa , jijjigata ta fara yi tare da kokarin tayar da ita tsaye ,tana cewa
"sannu falmata me suka yi miki ? Duka ? Kin ji ciwo ne falmata tashi muje ki shaa ruwa ,"

Rinjayar ta falmatan tayi a domin ta gaza tsayuwa sakamakon numfashin ta da yake sarƙewa , su duka biyu suka zube ragwaf a ƙasa kafin falmata tayi baya lau ta tafi zata kwanta cikin sauri yakaka ta riƙo ta kwakwalwar ta na son fahimtar me ke shirin faruwa da ƙanwar ta ?

Jijjigata ta fara yi cikin zubar hawayen da suka balle sakamakon tashin hankalin ganin falmatan a kwance bata motsi sai wani irin shiƙar numfashi take ,"

Cicciɓar falmatan take son yi amma ta kasa saboda tayi mata girma da nawi baza ta iya ba , kwantar da ita tayi ta taka da nufin zuwa ta kira mutane su taimaka mata , har ta yi taku biyu a gigice ta sake juyowa , zuciyar ta na bijiro mata da hoton gawar mahaifinta da ta bari a wuri makamancin wannan cikin "gona babu kowa ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now