BABI NA ARBA'IN DA BIYAR

8.7K 714 216
                                    

Da rashin yadda a fuskar Falmata , ta ɓanɓare jikinta daga na khaalty Rahima , Muryar ta na ɗan ƙyarma tace ,

"wacece ? Rahima kece ?

Zuwa lokacin Murmushi Khaalty Rahima take , murmushin da har ya bayyana haƙoranta , sake riƙe hannun Falmata tayi , da sautin muryar ta mai ɗan ƙarfi tace , "Falmatana ni ce Mamar ku , ni ce , ashe kuna raye Falmata , ina Yakaka ?

Da wani irin yanayi Falmata take sake wara idanunta tana ganin dusu-dusun fuskar matar da take gabanta , tana jin wani irin bugu da zuciyarta ta sauya a take da ziyarta ruɗani a tare da ita tace, "Mama na ? Ke ce Maman mu ?
Sai tayi baya da sauri kamar zata gudu , ta waiga dama da hagunta , da wani sauti tace , "Yakaka ina kike ? Kina ina ? Ki zo ki ganta wai wannan Maman mu ce ? Wai da gaske ita ce ?

Murmushin fuskar Khaalty Rahima bai ɗauke ba lokacin da hawayen fuskarta suke cigaba da sauƙa ta matsa tana sake kusantar ta , sai ta miƙa hannu ta jaa hancin Falmata da bai wani ciƙa tsayi ba , ta zarce da riƙe kumatunta duk biyu da hannuwanta , sannan ta haɗa goshin su guri guda , tana sake cewa ,"Ni ce Mamanku Faɗimah-Zahra ni ce Ina Amina ?

Wani irin yanayi ne na zallar Farin-ciki mai tafe da sanyi mai samar da nutsuwa , taji yana bin duk wata jijiyar jikinta , a sanyaye ta karkata kanta , muryarta da rangwamen sauti tace ," Maman mu ke ce ? Ke ce Mama da gaske ba mafarki ko gizo ba ? Mama daman kina Raye ? Mamana .
Bata jira ta amsa mata ba ta zarce da rungumeta ,tana sakin kuka da ƙaramin sauti , irin kukan da Ɗa yake irin sa a lokacin da ya tsinci kansa a gaban Mahaifiyar sa bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana haɗiyar baƙin-ciki cikin kewar ta .

Khaalty Rahima ta sa hannu biyu ta rumgumeta , tana jin wani irin tarin farin-ciki marar misaltuwa , ashe daman rayuwa zata sake iya yi mata sauyi mai tattare da farin-ciki irin wanda ta fidda rai da samun sa , ashe watarana zata zo da zata sake ganin ƴa'ƴan ta ? Allah abin godiya .

Sauƙowar Amnee daga Sama ita ta jaa hankalinta, da mamaki ta ƙaraso tana kallon su , da har zuwa lokaci , Falmata take kwakume da Mamanta bata bar kuka ba , da alamar tambaya a muryarta tace

"Ukhtee Rahima me ya faru ? wacece wannan ?

, jin sautin muryarta yasa Falmata ɗago kanta , kafin ta bi bayan Khaalty Rahima da take riƙe da hannunta , suka ƙarasa gaban Amnee , da murmushi Khaalty Rahima ta haɗa hannun Falmata da na Amnee , tana cewa

" wannan ita ce 'Ya ta Falmata da na baku labarin su ina zaton sun mutu ita da yayar ta mai sunanki Amina da ake mata laƙabi da Yakaka , ikon Allah da girma sai ga shi ya kawo min ita har gabana .
Sai ta waiga ga Falmata , tare da cigaba da cewa , "Fatima ya akayi kika san ina nan ?

Da bayyanuwar murna Amnee ta zarce da rungume Falmata , kafin ta ɗora da cewa , Alhamdulillah , Alhamdulillah , ashe ba haka nan ba na so yaran nan tun a rana ta farko da na fara ganin su , ace 'ya'ya nane , jini na , 'ya'yan 'yar'uwa ta , Ukhtee Rahima ai nasan Fatima da Yakaka tun shekarun baya suke rayuwa tare da 'yan uwansu a gidan nan ba tare da sun san dangantakar su da juna ba , kai Alhamdulillah .

Saman kujerun wajen suka zauna ,suna sanya Falmata a tsakiyar su , khaalty Rahima ta ce ,

"Ikon Allah Ukhtee ashe ma kun san su ? Ashe suna hannun ku ?

" ƙwarai na san su , ai yayan Zainab ( Doctor Hamza ) shine ya kawo su gidan nan a matsayin ƴan gudun Hijira , a gidan nan suke tsawon shekaru kusan biyar zuwa shidda , ikon Allah kenan ai kuwa ko zuwan Yakaka na kwanan nan taje har wajena ta gaishe ni , ai itace wacce kika ji na tambayi Rahima shekaranjiya kan ina take ta shaida min ta tafi Niger wajen Ƙanwar ta da 'yar ta , Allah ya saɓa haɗuwar ku ai da gidan nan zaki tarar da ita .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now