BABI NA HAMSIN

13.2K 1K 507
                                    

.Lokacin da Doctor Hamza ya isa unguwar su Malama Maryam dai-dai layi da gidan da Doctor Suleiman ya kwatanta masa sai ya ga ashe ma ya taɓa sanin gidan duk kuwa da cewa da dare ya taɓa zuwa amma bai manta da yarinyar da ya taɓa taimakawa ba a wani dare ana ruwan sama babu shakka a ƙofar wannan gidan ya sauƙe ta .

Kasancewar ana haramar sallar Azahar a lokacin dan haka a masallacin da yake kusa da gidan nan yayi Sallah .

Bayan ya idar sai ya matsa ya miƙawa Liman hannu suka yi musabaha , nuni ya yi masa kafin ya ɗora masa bayanin gidan da ya zo , to amma kasancewar an sanar da shi matar tana da aure ya zama dole sai da iznin Mijinta zai gana da ita , tunda ba sanin juna suka taɓa yi ba dan haka yake son sanin Mijin ta da farko , a zahiri wata buƙata ce ta son samun wasu bayanai daga bakin Matar da ake ƙira Malama Maryam yasa shi tasowa musamman domin ganawa da ita .

Dan jim liman yayi yana sake nazarin Doctor Hamza , kafin yace " bawan Allah lafiya dai ko ? Ba dai wani al'amari bane marar daɗi ya auku da har yasa kake neman Malama Maryam ?

Da sauri Doctor Hamza ya girgiza kai kafin yace ' ah ah ba wani abu bane marar kyau , kawai tambayoyi nake so nayi mata akan wata ɗalibar ta da ta koyar wacce aka ce daga baya ta zama kamar 'yar ta saboda kusanci da ta samu da ita , sunan yarinyar Amina .

Shiru Liman ya sake yi kafin yace 'Kana nufin Amina Mustapha Dilmari yarinya 'yar Maiduguri ?

" ita fa Malam .

"Allah sarki yarinyar kirki ce ai Amina , ta koma can garin su a halin yanzu har an aurar da ita sati biyu da suka wuce , Malama Maryam da kake nema ai Mata ta ce , kuma ita ce Malamar Amina tsawon shekaru Shida da suka yi tare , bari na shiga gida sai nayi mata bayani na haɗa ku , amma kafin nan zan so jin ko kai wane ne ? Kuma daga ina kake ?

Cike da jin daɗin ganin sauƙaƙuwar lamura Doctor Hamza yace " Malam ai ni ne Mijin Amina bayan haka kuma ni wan ta ne da muke 'ya'yan mata biyu .

" Masha Allah ka ce babban baƙo ne da mu , to Bismillah mana mu shiga daga cikin Falona kafin na yi mata magana .

Ganawar Doctor Hamza tare da Malama Maryam ya zo masa da wani irin sauyi mai girma da yake sauraren bayanan da take yi masa game da baki ɗayan rayuwar da Yakaka tayi tare da ita har ma da wanda tayi gidan uwarɗakin ta samy baby da a farko su kayi zaton yayar ta ce , kafin daga baya lokacin da ta faɗa musu haƙiƙanin gaskiyar kome game da ita ,su gane cewa basu da wata alaƙa ta 'yan uwantaka .

" alaƙar ta da Samy Baby da duk irin Yaudarar da tayi mata . har yadda daga baya Samy baby take son tilasta ta shiga harkar banza amma ta ƙi yarda da hakan shine ya kawo sanadin komawar ta Maiduguri .

Nisawa Malama Maryam tayi tana murmushi ta cigaba da cewa " Abu mafi daɗi da yasa nake yin Alfahari da Amina shine jajircewar ta wajen neman ilmin addini fiye da na boko , Amina ta fara karatun addini bata kai ga sanin ayoyi bakwai na Suratul-Fatiha ba amma sai ga shi cikin shekaru shidda da Yarjewar Allah ta samu cikakkiyar kyakkyawar Haddar izif talatin .

" bata san yadda ake yin cikakkiyar Alwala ba a shekaru shidda baya a yanzu Amina daga kan farillai , sunnoni da mustahabbai har makruhi na alwala ta sani , haka kuma sharuɗɗan Sallar ta sun inganta ta kuma san yadda zata yi gyara ga Sallar ta idan ta ɓaci.

" Amina ta san baƙi , ta iya karatu da rubutun Arabic ta kuma samu tarin ilmi daga littatafan addini da hadisai masu inganci dan haka ta san dukkanin haƙoƙin Ubangiji dake kan ta .

" Alhamdulillah shine kawai abunda zance da Allah ya rataya min nawin tallafa mata ta hanyar samu ilmin addini , ya kuma bani ikon koyarda ita tare da ni da sauran Malaman da ta ɗau ilmi a wajen su , nagodewa Allah da kafin barin ta wajena ta fita daga duhun jahilci .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now