BABI NA BAKWAI

7.5K 532 32
                                    

Juyi ya sake yi a karo na barkatai bisa makeken gadon nasa na alfarma, tare da runtse idanu yana mai sake jin yadda kan sa yayi masa mugun nawi har baya iya buɗe idanun sa sosai , ɗan ƙaramin tsaki ya jaa da yayi sanadin juyowar Tafeedah wanda yake zaune bisa doguwar ƙawatatciyar kujerar da take gaba ƙadan da gadon .

Cikin takaici yake duban biyamuradi yousouf ɗin , kafin ya ɗan yi gyaran murya ! "cikin kowanne daƙiƙa ɗaya da yake wucewa yana sake nisanta ka da lokacin sauke farillah " tafeedan ya furta kalmomin masu nuni da tunasarwa , cikin nuna halin ko in kula ga biyamuradi yousouf , wanda koh kafin tafeedah ya idasa bayanin sa ya buɗe idanun sa tarwai da jijiyoyin cikin suka yi jaa , kammala bayanin nasa ya zo dai-dai da miƙewar sa zumbur daga kan gadon .

Bai yi wani jinkiri ba ya fara taku cikin sassarfa lokaci ɗaya yana sauke idanun sa akan tagar ɗakin sa wanda hasken rana ya riga ya hudo ta tsakanin labulen .

Bayan tsawon mintoci fiye da talatin da biyamuradi youssouf ya ɗauka yana addu'a da neman gafarar mahaliccin sa bayan ya idar da sallah ,

sadda kansa ƙasa yayi yana me jin kunyar ɗago kansa ya dubi aminin nasa wanda ya tabbatar idanun sa a kafe suke a kan sa , yayin da sashi guda na zuciyar sa yana me son tuno da wani abu .

A firgice ya dago kan sa a sakamakon tunowa da yayi dawowar sa daren jiya da faduwar da yayi a harabar lambun sa wanda daga nan bai sake sanin inda yake ba a sakamakon kakkarfan baccin da yayi awon gaba da shi a wurin a yashe , da hakan baya rasa nasaba da sabuwar sumfurin dahuwar burkutun da ya sha a jiyan wanda gaba ɗaya ta hargitsa masa ƙwanya .

Aina ka tarar da ni ?

Shine kawai tambaƴar daya jefawa tafeedah bai koh kula da irin kallon da tafeedan ke jifan sa da shi ba mai cike da tarin ma'anoni .

A jefa a inda kaga yafi dacewa da kai cikin kuma irin yanayin da ka zabarwa kan ka ."amsar da tafeedah ya bashi kenan " yana me miƙewa cikin yanayi na nuna alamun tafiya yake da niyyar yi ,"

Wani boyayyar ajiyar zuciya biyamuradi youssouf ya sauke a sakamakon fahimtar da yayi cewa tafeedah ne ya kawo sa ɗakin nasa ,"

Da misalin karfe nawa ka shigo gidan ? Su wa ka tarar a haraba ta ina nufin ma'aikata na sun yi chanji ?

Mts! Idan kasan kana gudun zubewar mutuncin ka me zai sa ka jefa kan ka cikin rayuwar da kake youssouf ," tafeedah ya furta hakan cikin ƙufula yana me komawa ya zauna a inda ya tashi ,"

Cigaba yayi da cewa karfe uku na asubah na shigo sashin ka bayan tasowata daga wurin taron mu (meeting) ,inda masu tsaron gidan suka tabbatar min kana ciki tun farkon dare ,"

Amma abun mamaki nazo na gama neman ka ƙasa koh sama baka nan har nayi niyyar fita na sanar da masu tsaron ka , sai nayi tunanin zagayawa har cikin lanbu inda na tarar da kai kwance a ƙasa , da farko na tsorata amma daga baya na fahimci abun da ka min alkawarin ka daina sha kayi min rantsuwa da Allah akan baza ka sake sha ba ita ka sha youssof , ƙarin abun takaicin ma a cikin gidan nan , bayan ka san duk cikin ahalin gidan nan babu wanda ya taɓa sanin kana ta'amali da barasa ," kafi kuma kowa sanin masifun da fallasuwar wannan mummunar ɗabi'ar taka zata iya jawowa a garemu baki ɗaya ,"haba youssof , haba youssof , duk cikin tarin ababen zubda mutunci da jawo tozarta ka rasa wanda zaka zaɓa sai BARASA ? Bayan kasan itace shugaba ummul'aba'isi na jaan ɗan adam ga aikata kowanne irin sabon ubangijin mu ,"

tsagaitawa yayi lokacin da yaji muryar sa ta fara karkarwa alamun gaf yake da fara kuka sakamakon ƙona masa zuciya da wannan ɗabi'ar ta abokinsa ,amininsa kuma ɗan uwan sa youssouf da ya jefa kansa a ciki tun yana da ƙarancin shekaru sosai domin shi da kan sa ba zai iya cewa ga lokacin da youssof ɗin ya fara shan barasa ba , kawai dai ya farga ya gane ne shi da kan sa a saboda kusancin da suke da shi da juna ta yadda wasu lokutan dayawa zai taradda da youssouf ɗin cikin maye ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now