BABI NA HAMSIN DA ƊAYA.

11.3K 862 216
                                    

Da baya-baya Falmata ta fara taku tana jin wani tsoro-tsoro daga ƙasan ran ta kafin ta juya da hanzarin son gujewa haɗuwar su da ita da mamallakan muryoyin da ta ji suna kitsa sharri da bata kai ga sanin su waye ba .

Sai dai taku biyu kawai tayi ta ji an fisgo rigar ta ta baya da matuƙar ƙarfi da ba domin rigar tana da faɗi ba da babu abunda zai hana ta yagewa bayan ta jefar da ita a ƙasa warwas .

A tsorace ta juyo da taimakon hasken lantarki suka yiwa juna kallon tsakar ido tsakanin ta da Hajiya Mama ,

Ba tare da Hajiya Mama ta saki rigar Falmata ba tana ƙanƙantar da idanun ta da suke cike da tashin hankali tace "wacece ke ? Me kuma kike nema anan ? Wa ya aiko ki ? Sannan me kika ji ana cewa ?

Falmata ta kif-kifta idanun ta da basu cika karfi ba kafin ta fara kici-kicin kwacewa cike da dakiya a muryar ta tace " Ni ce Falmata , matar unh ' Umh Yarima Youssouf Abdoul-aziz , kuma ki sake min riga ta na tafi .

Wani irin zillo Hajiya Mama tayi a take gumi ya karyo mata ta shiga juya kan ta daga ɓangaren hagu zuwa dama baki ɗayan jikin ta tsuma yake .

Idanun ta da suka fir-fito a halin yanzu su ta gwalalo cikin kufcewar nutsuwar ta ta shiga jijjiga Falmata da wata muryar da ta fi kama da raɗa take cewa "Annamimiya ke kuma salon ki kenan ? Da salon da kika zo kenan ?? Lalle kin yi kuskure mafi girma da da ɗai wallahi baki sake maimaita makamancin sa .

Juyawa tayi tana jaan ta ita kuma tana turjewa , cikin ɗakin da suka fito ta koma jaye da ita tana shiga ta ingiza ta ba tare da ta kula da cikin jikin ta ba da sauran ƙiris ta faɗa kan cikin ba dan ta riƙe gadon da ta samu damar ƙarasawa gaban sa ba.

Hafsatouwa da tuntuni bata samu damar cewa kome ba illa fargaba da ita ma ya cika mata ciki maƙil jin wacece Falmata , da matsayin ta a gidan da kuma alaƙa mai girma da take da shi da zancen da suke tsakiyar yin sa ita da uwargijiyar ta da babu shakka Falmata ta ji kome .

Tana shiga ɗakin ta rufe ƙofar ta murza ɗan makulli da hanzari ta juya jin sautin mari da ya karaɗe ɗakin .

Akan Falmata ta sauke ganin ta wacce ta durƙusa akan guiwar ta riƙe da ƙuncin ta da Hajiya Mama ta zage iya ƙarfi ta mare ta .

Sake chakumota tayi ta ɗaga ta tana sake chukui-kuiye ta tace "za ki faɗa min me kika zo yi nan wajen a dai-dai wannan lokacin kuma wa ya turo ki ? me kuma kika ji ina cewa ? ko kuma sai na shaƙe ki kin mutu ?

Falmata da zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska zuciyar ta kuma ta cika da tsoro cikin rawar murya tace "wallahi ban zo yin kome ba kuma ba wanda ya aiko ni nan , mantuwa nayi na kasa gane hanyar komawa sashin da aka sauƙe mu saboda tunda muka zo ban taɓa fita ba kuma kin ga idona , idona wallahi bana gani mai kyau dan Allah kiyi haƙuri ku mayar dani sashin da Hajja take .

"Ƙarya kike yi munafuka , me ya fito da ke a daren nan idan da gaske dindimin kike yi ? Baki bani amsa ba me kika ji muna tattaunawa nace ? Kuma uban waye yace ki min laɓe ?

Mukut ! Falmata ta haɗiyi yawun tsoro cikin rashin sanin takamaimai amsar bayawar tayi shiru .

Cikin rashin sanin ta shirun da tayi shi ya basu tabbacin ta ji kome , abunda suke gudun kuma yana gaf da faruwa watau fallasuwar asirin su .

Falmata bata ankara ba taji sauƙar wani marin kafin tayi wani yunkuri ta ji sauƙar  duka da dundu ta ko'ina kusan gabadaya Hajiya Mama bata hankalin ta dai duka kawai take kai mata .

Ihun da Falmata ta buɗe maƙogoro ta rafsa shi yasa Hajiya Mama dakatawa daga dukan ta , idanun ta jawur ta juya ga Hafsatouwa tace "Hafsatouwa tai ki ɗauko min wuƙa mai kaifi ki kawo min .

Da gudu Hafsatouwa ta miƙe daga durƙuson da tayi ta fita .

Cak Kukan Falmata ya tsaya ta shiga wara idanun ta da ganin su ya sake yin ƙasa saboda kukan da take yi , ta fara taku tana laluben hanya so take tayi wani yunkurin tseratar da kan ta .

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now