BABI NA ASHIRIN DA BIYU

6.5K 822 254
                                    

Da gudu ta tako ta fito daga ƴar rumfar , yanayin da ta ga falmata a ciki ya mantar da ita duk wani halin fargaba da tsoron soji da suke ciki ,

Tana kuka ta nufi bakin titin inda ta hango gungun soji da wasu mutane farar hula suna tsaye , tun kafin ta karaso gudun da ta taho da shi ya ɗau hankalin su ,tare da ihun da take faman yi

Tana ƙarasowa ta zube a gaban su ba tare da ta ji tsoron bakin bindigar da ta ga sojojin suna gyarawa ba tare da saita ta da ita ,"

    Da rishin kuka take cewa kun harbi ƙanwa ta , zata mutu , kun kashe min ƙanwa ta me tayi muku ? Mu ba boko haram bane , meyasa zaku harbe ta wayyo Allah ƙanwa ta ,"

Wasu daga cikin su sun fahimci abun da tace dan haka wani daga cikin su fararen hula ya ɗan matso kusa da ita ,
    Ina ƙanwar taki take ?

Waiwayawa tayi tana nuno masa ƴar rumfar da suke ciki , tsabar kuka da ruɗanin da take ciki har numfashin ta sarƙewa yake yi ,

Su biyu suka nufi rumfar
   Yakaka ta take musu baya

Nan take suka fahimci bullet ne ya samu falmata a kafaɗa cikin rashin sani ,"

Da gudu gudu suka koma wajen sojojin tare da neman taimakon su akan a kai yarinyar asibitin kurkusa , ba tare da gaddama ba soja ɗaya ya amince zai jaa su a motar su ta soji .

Dan haka suka ciccibo falmata wacce ta riga ta suma suka ɗora ta bayan hilux ɗin sojin tare da yakaka wacce idan banda sambatun kiran sunan falmata babu abun da take gaba ɗaƴa ta ƙanƙame falmatan a jikin ta .

Da isar su babban asibitin gwamnatin jaha ( general hospital ) wanda bashi da wani tazara mai yawa da bakin kasuwar , aka shige da falmata bangaren bada taimakon gaggawa ( Accident and emergency)  nan suka tarar da mutane dayawa da suke cikin hali makamancin na falmatan wanda tarzomar jiya ta ritsa da su birjik , wasu sun ji munanan raunika , wasu babu hannu , wasu ba ƙafa , likitocin da suke kan aiki sai kai kawo suke , da alama sun gaji likis ga har zuwa yanzu akwai waɗanda ko kai ga fara basu taimako ba'a yi ba ,

Nan suka ajiye falmata akan dandaryar siminti bakin kofar domin duk gadajen da suke cikin ɗakin a cike suke ,

Bayan sojan ya shiga ciki yayi musu bayani , likitocin suka ce a ajiye ta kawai zasu zo kan ta domin aiki ya musu yawa , ko kuma idan likitocin safe sun zo su duba su tun da sun ce harsashin a kafaɗa ya same ta da sauki akan waɗanda bam ya tashi da su ,

Tsayuwar da bata fi ta rabin awa ba mutanen da suka kawo su suka yi , suka matso kusa da yakaka wacce har zuwa lokacin idanun ta zubar hawaye suke har sun kumbura ,
     Yarinya mu zamu tafi , domin muna da aiyuka a gaban mu , su kuma likitocin nan ƴan walakanci ne basu da niyyar zuwa su duba ta , ki cigaba da jiran su , sannan ki dunga leƙawa kina damun su akan su zo su duba ta , idan kuwa ba haka ba har jinin jikin ta sai ya ƙare ta mutu anan indai likitocin nan ne babu abun da ya dame su , mu mun tafi ,

ga wannan ki rike a hannun ki ko zasu ce ki sayo wani magani ,suka miƙa mata dubu ɗaya suka kaɗa kan su suka yi ficewar su ba tare da sun sake kallon inda falmata take yashe a ƙasa ba ,"

Wani sabon kuka ta sake fashewa da shi tana tattaɓa fuskar falmata wacce tayi sanyi ƙalau ,"
    Falmata na dan Allah kar ki bar ni , Falmata dan Allah ki tashi ,'
  Kamar mahaukaciya ta yunƙura ta tashi ta bazama ta faɗa cikin ɗakin da ake duba marasa lafiyan ,"
   Tana shiga nurses ɗin da suke taya likitocin aiki suka yi mata chaa ,"
   Mata meye hakan ? Baki ga aiki muke ba zaki zo kan mu da ihu ? Ki koma daga waje ki jira a fito da marar lafiyan ku , ba'a shigowa nan idan ba mu muka kira mutum ba fita-fita dallah ,"

  Kuka ta fashe da shi
   falmata na zata mutu dan Allah likita ki zo muje ki duba ta jini sai zuba yake daga jikin ta jinin ta zai ƙare ta mutu idan ta mutu bani da kowa ,"

MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA)Where stories live. Discover now