*NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Aka ce komai saidai idan ba'a sa masa rana ba, kamar jiya ne nayi likimo har kuna ganin nisan lokacin dana d'auka, to gashi har na dawo, nakuma dawo maku da wani sabon littafin nawa, Allah yasa yabiyaku kamar yadda kuke zato daga gareni, nice dai taku akoda yaushe UMMU ABDALLAH, iya wuya ana mugun tare🤝🏼, ku huta girmanku ne👍🏻.*
🌱 *1* 🌱
Kiran da Yabi tayi mata a karo na biyu yasa Maijiddah fitowa daga d'an akulkin d'akin nasu na k'asa cikin hanzari gami da amsawa cike da ladabi sannan tace "gani Inna, kiyi hakuri kiran farko da kikayiman ban idar da sallah bane saida na idar yanzu nasamu damar amsawa".
Yabi tace "dama ba wani abu bane Babanki ne yayo aike akan cewa lallai duk abunda kike ciki kiyi gaggawar shiryawa zuwa birni akan waccan maganar da mukayi tare kafin ya koma, domin kuwa Hajiya Uwa tana buk'atar yarinya mai jini a jika da zata cigaba da kula mata da girkin gidan tunda waccan mai aikin tayi aure"
Wata iriyar fad'uwar gaba Maijiddah taji, lokaci guda yanayinta ya sauya, kasa yin shiru tayi har saida tace da mahaifiyar tata "Innah ni bawai nak'i ta taku bane, inason zuwa birni amma bawai a matsayin da kukeso naje ba, bance nafi k'arfin aikatau ba amma Innah tayaya za'ai na tafi na barki ke kad'ai sai yara? Aikin zai yi maki yawa, sannan sanin kanki ne ko a karkarar nan kowa yasan halin Hajiya uwa bawani mutunci ta cika ba, kina gani fa ko ganin gida suka zo nan irin wulak'ancin da takema mutane abun babu kyau, hakan yasa ko gaisheta ban tab'a yunk'urin zuwa yi ba idan tazo, tun wani zuwa da mukayi wata rana tare dake da suka zo ban k'ara kwad'ayin zuwa ba, baya ga haka ma nifa bazan iya jure ganin yanayin da babana yake a gidan ba, babana maigadi ni kuma mai aikin gidan, haba Innah kifa duba don Allah".
Haka Yabi tayi ta k'ok'arin rarrashin Maijidda har ta samu ta shawo kanta, Maijidda tadai amince ne kawai amma ba don ranta yaso ba sai don batason tayita ja'inja da mahaifiyar tata.
*********************
Sati na zagayowa Maijidda ta shirya y'an tarkacenta ta hau hanyar birni.
A kwatancen da akayi mata bata b'ata ba, Unguwar ta sauka batare da tasha wuya ba taci sa'ar gane gidan domin sanannen gida ne (Kud'i baki garesu suna magana saidai idan dama babu su).
Gate d'in tayita k'wank'wasa wa, Yawale maigadi wato mahaifinta shine ya bud'e, yana ganinta ya saki wani irin murmushi wanda ke nuni da irin farincikin ganinta da yayi, har k'asa ta zube ta gaishesa, ya amsa cike da jin dad'i, yayita tambayarta lafiyar mutanen gida ita kuma tana basa amsa daidai da yadda ta baro su.
Suka k'arasa cikin gidan tare domin yayi mata iso.
Kalle-kalle Maijidda ta rik'ayi domin ko ganinta kawai take kamar a aljannar duniya, suka rik'a k'walla uwar Sallama babu wanda ya amsa, sai daga bisani Sangamar matarnan mai kama da k'irar samudawa wato Hajiya Uwa ta fito tana wani takun k'asaita
"Wa alaikumussalam" ta amsa cikin isa da gadara, fuskarta babu yabo babu fallasa ta cigaba da cewa "Allah yayi kin iso kenan, ya mutanen k'auyen?"
"Lafiya k'alau na baro su sunata gaishe ku" Maijiddah ta amsa.
Rufe bakinta keda wuya sai jin Sallamar wani matashi tayi, tana d'aga kai sukayi ido hud'u dashi, ba wani bane face *KHALIL* Autan Hajiya Uwa ( Namijin goro mai shegen d'aci, Yaro d'an hajiya kome kayi dadai, matashin d'an akuya mai tak'ama da fitsara) wannan shine kirarin sa.
Tun bayan kallon nan dayayi mata ya kawar da kansa baiko k'ara duban inda take ba, Mahaifiyar tasa ma saidai kawai yace da ita "Sannunku Uwa, mun sameku lafiya?" (Dayake kaf yaranta haka suke kiranta *UWA*), ita kam cikin sakin fuska ta amsa da "lafiya k'alau Auta, andawo kenan?"
Abunka da ba'a saba ba, sai Majiddah ta rik'a kallon abun wani iri, a nata lissafin sai take hangen kalamansa kamar cike suke da tsantsar rashin tarbiya, (tabdijam ai bakiga komai ba tukun, wannan ai aikin hankali yayi).
Kamar saukar aradu sai ji tayi ya daka ma Yawale tsawa, jifarsa ya farayi da lafuzzan sa kakkausa babu girmamawa ko kad'an acikinsu.
"Wannan ai iskanci ne, ace shekara da shekaru kana aiki gidannan amma kullun sai anyi maka gyara kan wani abu, sunanka fa maigadi ba mai aikin cikin gida ba, to yanzu da kabar bakin gate kazo kayi k'erere anan me kake nufi ne eh?" Ya k'arasa maganar yana mai tsaki.
"Kaima dai ka gani" inji Hajiya Uwa.
Cikin hanzari yawale ya juya batare da yace k'ala ba.
Maijiddah ji tayi zuciyarta na tafasa kamar zata k'one, wani irin kallon tsana ta rik'a yima Khalil, ji take kamar ta mik'e tayita kifa ma d'an banza mari, lokaci guda tsanar sa ta mamaye Zuciya, Ruhi da kaf ilahirin wani sak'o da lungu na sassan jikinta, "ta yaya mutane suke bari makantar zuci ta kama su? Baba ai yayi tsara da mahaifinsa inma bai girmesa ba, gaskiya da sake" maganar da Maijiddah ta rik'ayi a zuciyarta kenan.
Shikam gogan nawa ko a jikinsa saima bugama k'afafuwansa iska da yayi ya kama hanyar d'akinsa.
Hajiya Uwa ce ta tsinkema Maijiddah labarin zucin nata tace "Muje na nuna miki masaukin ki, kid'an huta sannan mu shiga kitchen da sauran wurare duk ki gaggani"
Maijiddah dai bata ce mata komai ba, har saida ta sake cewa "ko kurma ce ke ne, bakiji me nace ba?"
"Naji" iya amsar data bata kenan.
Hajiya Uwa takai Maijiddah d'akinta ta juya ta fita, fitarta keda wuya Maijiddah tace "Kan ubancan kai" ta fad'i hakan ne a fili, itafa a zahirin gaskiya bazata d'auki wannan wulak'ancin da k'ask'ancin ba.
********************
Bayan da Hajiya Uwa ta gama nunnuna mata gida, sai Maijiddah batai k'wauron baki ba tace "amma hajiya ni na zata abinci kawai nazo inrik'ayi banda sauran aikace aikace, ga mamakina sai nake ganin kinata lissafamin abubuwa irinsu, aike, share-share, goge-goge, wanke-wanke da sauransu"
"Abinci, Dama kin iya abinci ne? To ai ko zaki fara shigarmin kitchen sai na koyar dake tukunna, au ke yanzu idan nace ki shiga kitchen kiyi abinci sai ki shiga? To ma me zaki dafa me kika iya kunnawa acikin kayan aiki? Shi yawalen bai fad'a miki aikin da kikazo yiba?
Maijiddah ta wani had'e fuska tace " inda ya fad'a ai bazama ki ganni anan ba bare har na tambaya"
Da sauri Hajiya Uwa ta d'ago kai ta yamutse fuska sannan tace "me kika ce?" Domin batayi tsammanin amsar da zata fito bakin Majiddah kenan ba.
Maijiddah tayi shiru bata sake cewa komai ba.
Nandai ta gama nunnuna mata komai dama fita zatayi, taje taja mota tabar gidan.
*************
Parlour Maijiddah tazo tayi zamanta kan kujera ta hakimce tana kallon TV.
Khalil ya fito cikin singlet da boxers da niyyar zama parlour ya kalli k'wallo sai kawai yaci karo da hakima d'iyar sarki Ado bayero (🤣🤣🤣).
Yace "(Wa da fuck.... 4rm wch planet, hu re u?)"
Tabd'iii yo ita inama tasan me yake cewa, kwakwalwar nan dod'e take da miyar kuka, ammafa sai tsantar ilimin Addini (ina yinki Jiddah, ki basu 🔥).
Ko kallo be isheta ba, saima data lura fa da ita yake aiko ta tab'e baki tace "kaji dashi donni bansan me kake cewa ba inzakai hausa kayi hausa mallam"
Khalil ya zaro ido da sauri sannan ya sake cewa "ke y'ar gidan uban waye da zaki zo k'azama dake ki zauna nan ki wani hard'e k'afa?"
Aiko sai Maijiddah ta mik'e ta rik'e k'ugu da hannu d'aya tarik'a kad'a yatsun dayan hannun, dama besan tanada cikinsa ba (tana k'ule dashi), ta nunasa da yatsa tace "karka kuskura kace zaka zagi mahaifana a gabana don sunfi naka, niba d'iyar uban kowa bace face Yawale maigadin gidannan, k'azanta ai kala-kala ce, bama gara tawa ba ina iya wanketa da ruwa ta gushe kaiko taka fa? Don da alama baka da ta ido....................