NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *4* 🌱
Nan fa ta warware mata zare da abawa takuma fed'e mata biri har wutsiya game da labarin halin ha ula'in da ma'aikatan da sukayi aiki gidan ke tsintar kansu, sakamakon y'an akuyanci irin na Khalil d'ansu.
Ta k'ara da cewa "kinga wallahi kusan ma'aikata biyu duk k'awayena ne, wata mai suna Dije y'ar Gwarzo bayan daya cuta mata Allah cikin ikonsa bugu d'aya ta kamu, wallahi ina fad'a miki sai zubar da cikinnan akai, nan take zuwa tana kawo ma maman mu kukanta, amma me ai itama kanta maman tamu babu yadda ta iya, don a unguwarnan kinadai gani mu kad'ai ne talakawa cin kashin duniya babu wanda babu gani tun bayan rasuwar mahaifin mu"
Maijiddah tayi sauri ta tsinketa tace "to baku da k'auye ne? Ku koma garinku mana"
"Hmmm Maijiddah kenan, ai abunda ya koro b'era daga rami ya fad'a wuta to ki tabbata yafi wutar zafi ne, ai k'auyenmu abun kar a tona Allah dai ya rufa asiri, babanmu tun yana d'an shekara 12 ya shigo nan birni yana almajiranci, a haka har Allah yasa ya fara aiki nan kusa damu gidan Alhaji Mansur, tunda Allah yasa ya fara aiki be bari ba har sai lokacin da aurensa ya tashi, Alhaji Mansur ya bashi wannan gidan da muke ciki saboda yanason ganinsa kusa dashi don irin amanarsa, ya kuma bashi jari mai tsoka, kinji dalilin zaman mu cikin irin wannan unguwa ta masu fad'a aji"
Maijiddah ta lumfasa tace "tabd'i ashe babanku ya kauce? Allah yajikansa yasa ya huta"
"Bari kiji malama nida kike ganina ba irin sakarkarun ma'aikatan da suka sabayi bane, tsaf zan gyara masa zama ai bana tsoronsu wallahi, abunda na sani shine idan babba beji kunyar hawa jaki ba to jaki ko bazeji kunyar kado da k'aton banza ba, ki zuba ido ki gani zakice na fad'a miki"
Ita dai Mariya ta saurari Maijiddah ne kawai amma gani take babu abunda zata iya, yanzu talaka ai ya zama rak'umi da akala sai yadda akayi dashi"
Maijiddah fa wuri ma ta samu tayi dirshen babu niyyar tafiya gida sunata zuba surutu, zani ta tarar da muje kenan, aiko ba zato sai jin sallama sukayi, Mariya na bud'e gate d'in sai taga Yawale, murmushi tayi sannan tace
"Baba Yawale sannu da k'ok'ari ashe kai ne?"Ya amsa da "eh nine, ya mutanen gidan duk lafiya ko?"
"Lafiya kalau" inji Mariya.
"Da Allah wata yarinya batazo nan gidan kawo markad'e ba?" Ya tambaya.
"Da sauri Mariya tace eh tazo Maijiddah ko? Bari a kirata" bata jira amsar sa ba ta juya domin kiran Maijiddah.
"Maigadin gidan Hajiya Uwa ne yazo nemanki"
Aiko Maijiddah tace "to naji amma daga yau ki gyara bakinki sunansa Yawale ba maigadi ba"
Mariya tad'an harare ta cikin wasa tace dallah dika-dika yaushe kika zo gidan kefa bakisan komai ba yanzu zaki sani, na fiki sanin sunansa Yawale saboda har Mamana ya nema mu muka hana auren, amma mutunen yanada kirki sosai wallahi don shi ya siya mata ma injin markad'en nan, kuma haryanzu yana mana abun arziki, kema na fad'i sunansa ne kawai don ki gane ko waye amma wallahi Baba muke ce masa, kedai kawai kije wani lokacin idan mun had'u zan baki labari"
😒 "Namijin goro kenan, aaa ai dole ku kirashi Baba ai baban ne gaskiya, shi nan inda yake har yasan yayita maku bauta da hidima haka ko beda iyali ne?"
"Yanada su mana, sunacan k'auyensu ai kiga Namiji kawai, abun fa babu babba babu yaro, kedai kawai ki bari idan mun sake had'uwa kisha labari" inji Mariya.
"Zan ko so nasha labarin nan, amma kafin nan inaso kisan irin labarin da zaki bani don ninan da kika ganni y'arsa ce ta fari, nice babbar d'iyarsa ta k'auyennan nasu da kika fad'a" ta k'arasa maganar tana wani murmushin iskanci sannan ta fice.
Mariya ta zaro ido waje 😳 (wato allura ta tono galma kenan, ai ga surutu nan ya miki rana).
Maijiddah na fitowa Yawale yace "haba maijiddah an aikeki kinje kinyi zaune, haka akeyi?"
"Tayi wani murmushi tace "yi hakuri baba wallahi k'arar injin din daka siya ne yamin dad'i kasan mu acan gida Innah da Turmi da dutse take aiki ban saba jin wannan sautin ba, saidai idan munje hayi"
Ai yawale sai ya tsaya cak kamar wanda batir ya k'are mawa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai yake maimaitawa a zuciyarsa, (🤣🤣🤣🤣🤣 ba'a tab'a cewa gaskiyarka ta k'are saidai k'arya).
Itako Maijiddah tayi gaba abunta.
Tana shiga gida ta tarar da Hajiya Uwa ta cika kamar ta fashe tsabar fushi, aiko ta hau zagin Maijiddah kamar zata cinyeta, Maijiddah dai bata ce mata k'ala ba, don wallahi idan har ta bari ta bud'e baki bazata ji dad'in abunda ze fito daga bakinta ba, gashi daman itama ran nata a bace yake.
Saida ta bari ta gama masifarta sannan tace "Hajiya mezanyi yanzu?"
Wani irin kallo na mamaki Hajiya Uwa tayi mata don tayi tsammanin zata ce Hajiya kiyi hakuri ne don Allah (tabbb ashe ma ba Maijiddah bace kenan).
Tayi mata banza ta cigaba da aiki, itadai Maijiddah bata bar kitchen d'inba kuma bata kama aikin komai ba, tana tsaye tana binta da ido, amma kuma zuciyarta bata wurin, tanacan tana mamakin k'arfin hali da rashin sanin ciwon kai irin na wasu mazan, wai ace har Yawale nan inda yake ze iya tinanin k'aro wata mata banda yanayin daya barosu can k'auye, shiyasa arzik'insa basa zuwa ko ina, ace shekara da shekaru yana aiki a birni amma gidansa nacan babu canji, Yabi sai aikin k'arfi take tana faman wahala da rayuwa, gashi Yabi na masifar so da tausayin Yawale, yana nan yana wahalta ma y'ay'an wani nasa kam ko oho sai abunda suka gani kuma a haka idan yakai suyita murna suna sa albarka (Maza mutanen mu, ku keda kan ku keda k'afa).
*******************
Da yamma bayan sallar Magrib, Maijiddah na kunna turaren wuta, dayake irin abun kunna turaren wutannen ne na jonawa (electric burner), kowane lungu da sak'o na gidan akwai socket, haka saida ta gama sama ko ina har d'akinta, tazo wucewa ta wurin d'akin Khalil kenan ta hango d'ankinsa a hangame yayi d'aid'ai bisa gado yanata bancinsa hankali kwance da alama beyi sallah bama, aiko ta aje burner ta ruga kitchen ta d'auko silin barkono guda uku a fili tace "ai dama nace maka zan rama, zakuma ka gani" aiko ta shiga a hankali ta nema socket ta jona, dama windows d'insa duk a rufe suke, tasa barkonon nan acikin wutar sannan ta zare key d'in ta maida k'ofarsa ta rufesa ta gaba tayi gaba abunta tare da key d'in.