19

1.3K 71 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                 🌱 *19* 🌱

Suna nan sunyi zugum a d'aki sai kallonta suke babu wanda ya sake cewa komai, Khalil a wani sashe na jikinsa sai ji yake kamar yaje yasa ta jikinsa don yanayin dayaga tana ciki, shikam sam ya kasa gane wannan canji da yake ji atare dashi, "wai meke shirin faruwa ne?" Tambaya ce da yayi ma kansa, nima nayi, masu karatu ko nasan har kun fidda amsar, to mudai bisu muji yadda zata kaya.

Lokacin da Yawale ya dawo daga siyo allurar hatta sauran frnds d'in suma sun bisu cikin d'akin don ganin jikin Maijiddah saboda sunji shiru.

Yawale fa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dukda ya ganema idonsa abunda ke faruwa amma shidai ya tsorata da lamarin.

Sanda Fahad ya fasa allurar, sai sauran abokan nasu suka fita, Yawale yayi tsaye yak'i tafiya Khalil ma haka, shikam Fahad bece dasu komai ba, saidai Maijiddah da yayi ma magana yace to ta gyara za'ayi allura, babu shakka ba tsoro ta gyara, ji take jiri na d'ibarta, ganin da sukayi kamar bata iya tsayuwa yasa Khalil da Yawale rige-rigen tareta, amma sai Khalil yaci nasara kasancewar shine mafi kusa da inda ta tsaya, sam bata sa hannuwa ta rik'esa ba, kanta kawai ta aje a kafad'arsa tana fidda lumfashi mai zafin gaske, Khalil har cikin zuciyarsa yake jin fitar lumfashin nan, Fahad beda zafin hannu don har ya gama allurorin bata ma sani ba saida yace ya gama sannan Khalil ya taimaka mata ta kwanta ya lullub'eta, sai suka yo waje gaba d'ayansu.

Yawale ya koma gaban gate su kuma suka koma inda suke zaune parlour.

Rashin walwalar data bayyana b'aro-b'aro a atare da Khalil ne yasa abokansu suka fara tonon sa suna fad'in "Khalil bamu fa gane ba kodai daman kaine mijin da akayi mata tun tana ciki ne? Coz wannan kulawar tayi yawa"

Fahad ya k'ara da cewa "guys ni wallahi banma tab'a sanin Khalil nada kulawa haka ba, wallahi da na zata Khalil Gay ne coz ba ruwansa da mata ko irin kulawar nan da damuwa da mace ba ruwansa, tsakaninsa da mace saidai hawa da sauka, ya kammala yabarta nan ya mik'e (matashin d'an akuya kenan mai tak'ama da fitsara), amma shine yau tabbbb, kunga yadda yake kamar ze cinye yarinyar nan? Anya Khalil kodai Allah yayi maka kamu ne saboda naga canji da yawa atare dakai, koda yake ma ai haka akeso"

Khalil yace "Mtsww Allah ya kyau, wallahi baku fahimtar komai, wai so, aini zuciyata ba sakarya bace da zata kamu dason waccan y'ar k'auyen, yarinyar da idan ka sake kace mata tnQ to wallahi ka bani ka shiga uku da bala'i don zatayi tinanin zaginta kayi, d'if ce yasin ina fad'a maku batasan komai ba sai rashin kunya da raini"

Fahad yace "nidai na gani inaso, idan ma dagaske kake bata iya ba na koya mata, rashin kunya kuma ai ance ko kare baya haushi banza saida dalili, ba wasa nake maka ba Khalil, atattare da yarinyar nan naga matar aurena, ka shige man gaba mana"

"Hmmm" abunda Khalil kawai yace masa kenan.

Sannan ya cigaba da cewa "su Zaks, Sharlo, Bobo da sauransu duk basu san kun shigo gari ba, zan kirasu anjima na fad'a masu muna nan fasowa sai su aje mana kayan aiki"

Sukace "eh wallahi kirasu"

Fahad yace "to nidai kunsan dama ba ruwana da wannan kayan aikin naku don haka k'ilama bazan biku ba zan zauna gida"

Wani irin kallo Khalil ya masa sannan yace "yasin sai kaje, c ds man"

"Wai Bobo shima nan garin yake ashe? Wallahi na zata d'an Katsina ne" wani ya tambaya acikinsu.

Khalil ya amsa da "aiko d'an kano ne mamansa ce y'ar Katsina shiyasa zaku ji yana yawan zuwa, kuma ma sunada gida can"

Bayan wasu y'an sa'anni Khalil ya tashi ya koma duba jikin Maijiddah.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now