NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *51* 🌱
"Baka da amsa Yaya Kamal adai halin yanzu, nifa kaina ya k'ulle plz yiman da hausa, wai me kake so kace ne?"
"Me nakeso nace koko abunda kikaji na gama cewa? Hausa na miki babu ko sirki acikinta, wannan shine gaskiyar magana" Kamal ya amsa yana mai saka idanuwansa cikin nata.
Wani haushinsa Maijiddah taji wanda ta rasa dalili, "to idan ma dagaske ne abubuwan da ya fad'a ai kenan tsautsayine bayin kansa bane, to amma.... Wannan shine lalube wai akace abu a duhu" a zuciyarta taketa wannan zancen.
Kamal ya tsinke mata tinani yace "Maijiddah ko baki fad'amin ba nasan na sakaki cikin rud'ani da lissafi yanzu haka, shiyasa bazanyi tsammanin samun amsarki a halin yanzu ba dole sai kinyi tinani, amma da zaki kyautaman bayan kinyi tinani zab'inki ya kasance K'anina ne KHALIL bani ba"
Bayan wannan maganar da yayi gabaki dayansu sunyi shiru har na tsawon 20mns batare da sunce ma juna komai ba, kowanensu da kalar tasa bugun zuciyar.
Daga bisani Maijiddah tayi k'ok'arin fara magana kamar haka,
"Yaya Kamal kafin ka wuce inaso na baka shawara dukda dai ni yarinya ce akanka amma ni a ganina hakan shi ya dace da kayi"Kamal ya jinjina kai alamar yana sauraronta.
"Ina ganin lokaci yayi daya kamata ka warware wannan sirrin daka kulle na tsawon shekaru hud'u, rayuwa ake yimawa ka godema Allah daya baka aron rai har ka kawo yanzu, kaje ka tara y'an Uwanka ka fad'a masu komai, kosu So ka kosu k'ika ya rage nasu kaidai ka sauke nauyi, Mahaifiyarka itace abunji dama ya lafiyar giwa.... Hakanan zaka fad'a mata kamar yadda ka fad'aman yanzu domin duk yadda nake sonka bekai yadda take sonka ba, ko bajima ko badad'e zata fahimce ka kuma zata yafe maka"
"Wa, Uwa? Tabd'i Allah yasa ba rabon tsinuwa bane ze kaini ga fad'a mata hakan" ya fad'a idanuwansa waje.
Maganar da suka yita tattaunawa kenan har Allah yayi dawowar Yawale cikin gidan, Maijiddah kam tasha kuka kuma babu yadda za'ai fuskarta ta b'oye hakan, ita babban tashin hankalinta ma shine yadda zata fuskanci mutanen gidan da wannan jajayen idanuwan, lokaci guda dibara ta fad'o wata, bayan jin sallamar Yawale aiko sai Kamal yaga ta tashi da sauri me kamar gudu ta fita dafe da ido, tayi kan Yabi ta fara, "Inna huremin dan Allah tun d'azu nake murza yak'i fita, bansan ko meye ya fad'aman a idon ba, inna don Allah huremin" tana magana tana murza idon.
Itako Yabi duk ta rud'e, ta mik'e ta d'ebo ruwa, Yawale shima yayo kansu yana fad'in "meye ya fad'a a idon?"
"Nima bansani ba Baba" Maijiddah ta amsa.
"To Allah shi kyauta"
Yabi tasa mata ruwa a idon har a k'afa, shiko Yawale fad'i yake bata gishiri ta lasa.
Khalil ya fito shida Aidan suka gaisa da Yawale, haba ai yana ganin fuskar Maijiddah tayi kwab'a-kwab'a yayo kansu da sauri,
"Jiddah meya faru, meya faru da idon?" Khalil ya tambaya.
Yabi tace "kaga wallahi wani abune ya shiga idon, nikam banga komai ba k'ila dai kakkab'i ne ko yaji ne haka dai"
Khalil ya rud'e kamar shine abu ya shigar ma ido, nan shima Kamal ya fito bayan daya gama had'a kansa don bayaso ya fito su gansa a firgice, mamaki ya kamasa dayaga anata k'ok'arin wanke ma Maijiddah kakkab'i a ido bayan shine kakkab'in, koda ya k'araso wurin saidai yace mata sannu don yasan komai, sannan ya maida dubansa ga Yawale.
"A'a ha to kai malam Kamalu shigowar yaushe?" Cikin fara'a Yawale yayi masa tambayar.
"Wallahi tun d'azu, mun sameku lfy? Anyi sallah lafiya?"
