45-50

2.6K 96 3
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Yayata kuma k'anwar uban y'ay'ana MARYAM AMINU (MRS NOOR)  kinyi mini daidai daidai, ga jinjinar ban girma nan Allah ya raya su Lilmaigold, u no say ur Sisi luv u plenty, i dey do u i swear*

                🌱 *45* 🌱


Kamal fa shima ji yake kamar yayi tsuntsuwa yabi su Maijiddah, saidai daurewa yake amma abun na matuk'ar cinsa a zuciya, bunu-bunu ya lek'a d'akin Maijiddah ya kalli ko ina ya juyo, wani lokacin ma har zama yake kan gadon kokuma ya kwanta abunsa kamar tab'ab'b'e.

****

Kamal da kansa ya fita ya shigo da sabon Maigadin da aka kawo bayan da suka kirasa a waya cewar suna k'ofar gida.

Ya kallesa ya sake kallonsa saidai yace su shigo kawai, amma a zahirin gaskiya beyi masa kama da Maigadi ba, kama ma yayi masa da d'an giya.

Suka shigo ciki yace su zazzauna kana shi kuma ya wuce d'akin Hajiya kiranta.
Tare suka fito, sai shashshan k'amshi take ita da bala'i Hajiya babba, itama zaman tayi bisa kujera daga gefe tana kallonsu d'ai-d'ai.
Suka gaisheta, ta amsa cikin isa da tak'ama sannan kuma tace "waye maigadin a cikinku?"

"Dukkanninmu aikin mu kenan gadi, saidai ni nan mak'otanku nake aiki, wannan shine maigadin dana kawo maku kugani idan yayi" inji Maigadin mak'otansu.

"Mtsww amsa y'ar kad'an wadda befi kace 'gashi nan ba' shine ka wani tsaya dogon labari, gara ma da Allah yasa bakai bane" ta k'arasa maganar tana wani yamutse fuska kamar taga kashi.

Kamal saidai ya kalleta ya girgiza kai, ya maida dubansa kansu yace "Malam mamuda mungode Allah ya saka da alkhairi, shi kuma daka kawo mana Allah yasa ya iya maye gurbin Baba Yawale, Allah yasa ya kasance me amana"

Malam mamuda yace "tabd'i ai Alhaji bazan sage maku guiwa ba, amma samun mutun kamar Yawale a duniyarnan ai sai anyi zufa, saidai kamantawa kam"

"Wai ma meye sunan sabon maigadin? Ko kurma ne? Naga baya magana" Hajiya Uwa ta tambaya.

"Sunansa Rabilu Hajiya, kuma ba kurma bane, kawai dai baya ji ne sosai sai an d'an d'aga murya" cewar mamuda.

Cikin barkwanci Kamal yace "hala d'an zamfara ne? Kasan sune ba'a masu magana kad'an suji sai an d'aga murya"

Mamuda yayi dariya yace "a'a mutunen nan cikin gari ne"

"A'a kace dara taci gida kenan?" Kamal ya fad'i haka yana murmushi, kafin nan ya cigaba da magana,

"Batare da b'ata lokaci ba, Malam Rabilu zaka yi gadi sannan kuma zaka d'an rik'a yin wasu aikace-aikacen na gida wanda basufi k'arfin iyawarka ba, misali shara da gyaran harabar gida da kewaye, bama flowers da shukoki ruwa dai da sauransu, sannan yanzu idan muka fita zan nuna maka d'akinka da wasu abubuwan da duk ya kamata ace kasani"

Rabilu cikin girmamawa yace "to Alhaji insha Allah za'ayi komai yadda ya kamata, nagode sosai"

Suka tashi zasu fita, harsun zagaya zasu fita k'ofa Hajiya tace "da Allah mamuda kake ko wa? idan kanada wata wadda kasani med'an tsafta haka da sanin ciwon kai, wadda tasan girma da darajar mutane ka kawo mana ita ta rik'a yi mana aiki"

Malam Mamuda yace "babu matsala Hajiya insha Allah za'a duba" su ka fita.

Suna fita kira ya shigo wayar Hajiya, tana dubawa taga Yaya ne, tayi sauri ta d'aga, bayan da suka gaisa ya sheda mata cewa tun d'azu fa AIDAN da FU'ADA suka kamo hanya (manyan yaransa, Aidan ne babba me kimanin shekaru 15, sai Fu'ada wadda bazata wuce 12 ba), driver ya taho kawosu, sunce nan wurinku zasuyi sallah, "tun d'azu nake nemanku tak'i shiga, na samu Auta  amma be d'aga ba".

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now