NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌹 *Ds is 4 u my Adviser AYSHA .B ABDULLAHI, ki huta girmanki ne, y'ar mutan Machika na yinki iya wuya.*
🌱 *28* 🌱
Hankalin Maijiddah yayi mummunan tashi bayan da ushe ta sheda mata Yabi jiki babu dad'i tana kwance, hakan yasa tad'au aniyar tafiya babu shiri, Yawale ma haka domin bega ta zama ba sahiba nacan ana bincikar file d'inta.
Da suka fito domin tafiya Kamal ya biyo bayansu tare da sheda masu shine fa ze kaisu, Yawale yace a'a yabarshi kawai amma sam yak'i yace ba damuwa su shiga mota kawai, Khalil yace shima zeje, amma sai Kamal ya hana domin gudun kar abar gidan babu kowa, dama ga tafiyar tazo masu babu shiri Hajiya ta fita saidai Kamal ya fad'a mata ta waya.
Suka shiga mota suka kama hanyar Rimin gado, Khalil ko aka barshi shi kad'ai a gida kamar maye.
Kad'aici kam yanasa abubuwa da dama, domin zuciya zata samu damar raya maka abubuwa da dama, shirun yayi masa yawa sai yake jin bari kawai ya kira frnds d'insa su Zaks, sharlo da sauransu, haka kuwa yayi, ya kirasu domin su d'ebe masa kewa.
Da suka tashi zuwa basu zoba saida tilin kayan cakewarsu, abunda Khalil ya kwana biyu beyi ba, yau kam gida nasu, ko maigadi babu bare wani d'an cikin gidan, Hajiya Uwa ko ita da dawowa sai yamma lik'is.
******
Tunda suka iso garin rimin gado mutane ke binsu da idanuwa suna kallo kamar sunga watan ramadan, sai kace basu tab'a ganin mota ba, duk inda suka kutsa sai an bisu da ido ana washare baki (Allah sarki mutanen mu, duk inda muke sai mun nuna halinmu, badai komai kowa asalinsa nan).
Motarsu bata tsaya ko ina ba sai k'ofar gidansu Maijiddah, ita ta fara fitowa ta shiga gida da gudu, a zaton ta zata iske Yabi warwashe a k'asa kwance bata iya motsi, sai ta ganta zaune jikin ba laifi da sauk'i, Mamaki ya kama Yabi data ganta tace,
"Aaha Maijiddah saukar yaushe? Lafiya kuwa dai?"
"Yo ku zan tambaya lfy Inna, Ushe tace mana kina nan rai hannun Allah, hankalinmu ya tashi muka garzayo gida" Maijiddah ta amsa.
Yabi ta kalli Ushe dake zaune gefenta tace "kai Ushe wannan wace irin wauta ce? Kinbi kin tashi hankalin bayin Allah hakanan kawai babu dalili, haba ai ba'a haka"
"To ni Yabi yazanyi? Jiya ne dana ga jikinki ya tsananta da daddaren nan kamar bazaki kai ba, shine na yanke shawarar kiransu suzo idan da rabon zaku gana, kinsan halin rayuwa"
Ushe na rufe baki su Yawale da Kamal suka shigo.
Maijiddah ta shinfid'a ma Kamal wata k'aramar tabarma sabuwa gal, yanema wuri ya zauna, ya gaishesu sannan yayi mata ya jiki.
Yawale yace "sannu Yabi, ashe jiki babu dad'i shine kika k'i fad'a mana, sannu kinji"
"Ai naji sauk'i, Ushe ce da shirmenta kawai ta tado ku kuka taho wallahi, amma jiki Alhmdlh kam" cewar Yabi.
Ushe taje k'ofar gida ta samu yaro ta bashi ya karb'o masu ruwa a shago, da gudu yaje ya dawo, ta shiga gidan ta basu ruwan.
"Wannan shine Auta ko shine Aliyu?" Yabi ta tambaya.
Kamal saidai yayi murmushi yayinda Yawale ya fara bata amsa "wannan har kin manta shi? Na wajena ne mutanen china"
"Ohooo Kace Kamal ne, Allah sarki Kamalu ya k'ok'ari? Ya ayyuka?"
Kamal ya amsa da "lafiya lau" fuskarsa cike da fara'a.
Suka cigaba da fira, suna tambayar lafiyan mutanen gida.