page 2

2.4K 123 1
                                    

*NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

               🌱 *2* 🌱

(Kunsan fa akwai irin maganar da za'ayi maka komin zafinta kama rasa abun cewa don tsananin tsabar mamaki).

Khalil shiru yayi yadda kasan wani sakarai, ya kafeta da ido, hajiya Maijiddarku ko ta koma ta k'ara hard'e k'afa kan kujera ta cigaba da bama ido abinci.

(Hhhhhhh)

Khalil ya yamutse fuska gami da kallon sama kad'an alamar ya shiga guntun tinani, zuwa caaan yayi wani irin munafikin murmushi ya fice zuwa harabar gida.

***********

*MAIJIDDAH*

Maijiddah kyakkyawar budurwa ce wadda bazata wuce kimanin shekaru 17-18 ba, tanada matsakaicin tsayi, wankan tarwad'a ce, tanada dogon hanci daidai misali, idanuwanta y'an daidai suba manya ba kuma suba k'anana ba, saidai farare ne tass kamar k'auyensu babu k'ura, tanada gashi sosai domin ko gado tayi mahaifiyarta cikakkiyar bafulatar jihar Gombe ce, mahaifinta ko haifaffen garin Rimin gado ne dake jihar kano.
Tanada jiki, don lallai kam bazamu kirata siririya ba (don tayi biyu na 😜)
Bakinta yanada d'an tsawo kad'an kuma tanada wushirya, hak'oranta ruwan madara, tanada diri daidai nata masha Allah.

Ta kasance y'a ta fari a wurin mahaifanta (Yabi da Yawale), tanada k'anne su hud'u biyu mata biyu maza.

Maijiddah mace ce mai kamar maza, babu irin aikin da batayi acikin gidan nan, Yawale bai yadda da karatun boko ba hakan yasa be kaita makarantar boko ba amma a b'angaren ilimin addini kuwa (hmmm bama niba ko Uwar Audu albarka🤣) ta sauke Qur'ani a haddace, zakuma ta iya rubuce shi tare da sanin littafai manya da k'anana na addini iya gwargwado (toh yanzu zasu fara tinanin ko a bakin ka'aba aka haifeta 😏, baiwa ce kawai daga Allah 😎).

Amma fa a b'angaren boko ko (Good) kace tana iya cewa kace mata gutsun..........

Maijiddah bata d'aukar raini kowa yasan halinta a garinnan, idan ko kanaso ka kirama kanka bala'i to ka kuskure ka zagi Yabi ko Yawale ranar zaka ga k'arshen alewa.

Aikin Mahaifinta GADI, yana gadi ne a gidan wani d'an uwansa na b'angaren uwa dake cikin birnin kano wato *Alhaji Abdullahi* amma dangantakar tasu da dan nisa gaskiya, Alhaji Abdullahi babban D'an kasuwa ne bema cika zama ba saidai yanada kirkin gaske, halascin sa yasa Yawale yake tare dasu haryanzu komin rintsi komin wuya.

Mahaifiyar Maijiddah ko takanyi wankau da surfe, saiko d'an k'ulle- k'ullen kayan miyan da ba'a rasa ba, irinsu kuka, busassar kub'ewa, gishiri, daddawa dadai sauransu.

Maijiddah nasan gayu, boko dakuma birni saidai kashhh babu mafarkinta d'aya da yazo daidai da ra'ayin mahaifan nata, burin mahaifanta shine ta samu miji tayi aurenta anan garinsu Rimin gado kusa dasu, (ta yaya zatayi auren bayan kowa acikin samarin garin tsoron tunkararta yake saboda masifarta da rashin d'aukar raini?).

*KHALIL*

Khalil matashin saurayine wanda baze wuce kimanin shekaru 26-27 ba, Auta ne a wurin Alhaji Abdullahi da Hajiya uwa y'an asalin garin Rimin gado mazauna birnin kano ayanzu haka, yanada tsawo tubarkallah sannan  kyawunsa daidai gwargwado saidai kaf cikin yaran gidan shi kad'ai ne bak'i sauran duk farare ne, bak'in nasa bamai muni ba sannan shi kuma yafisu kyau (dondai kunsan abunka da bak'in mutun ba lallai bane ku yadda yafisu kyau ba), yanada yayye har uku, biyu maza sai d'aya mace, kowannen su ya kama gabansa, babban yayansu da ita macen suna gidajensu na aure, na biyunsu ko baya k'asar yana china domin gudanar da wasu aiyukansu na kasuwanci, Khalil ne  kad'ai ya rage a gabansu, Hajiya Uwa bata had'a kowa da Autan nata ba, sam bataso a tsawatar masa, yayyensa sunyi fad'a har sun gaji.

Ya kammala karatunsa na matakin Degree amma daga nan be sake kwad'ayin cigaba kokuma shiga cikin wata harkar cigaba ba.

Sai tsabar jawo magana iri-iri, shaye-shaye kam babu kama hannun yaro don acikin abokansa shine ma shugaba.

Idan ya rasa kud'in siyo k'waya to lallai ko b'era baze nuna masa sata ba acikin gidannan, tabbas babu wanda ya tab'a kawo k'ararsa daga waje kan cewa ya satar masa kaya amma fa acikin gidansu abun ba'a cewa komai 🤐.

Anyi ma'aikata masu tarin yawa y'an mata acikin gidansu amma tunda ya mallaki hankalin kansa babu wadda ya tab'a bari tabar gidan hankali kwance sai ya mata illa (yaci takensa *D'an akuya*) , ma'ana *Fyad'e (titsiye)*, kuma gashi babu halin su d'aga magana (Allah sarki talaka ko kuma ince rashin sanin y'ancin kai).
Haka zasu rufe magana suce sharri ne akayima d'ansu, wasu kuma su amince amma su rufe masu baki da masu gida rana (kud'i).

Khalil bashi da kunya ko kad'an gashi baya daraja mutane komin girmansu, ba kamar talaka yanada k'yamar talaka (Dan iskan sai kace da rigar kud'i aka haife shi).

***************

Washe gari.
Bayan Maijiddah ta idar da sallar asuba, ta zauna ta cigaba da lazumi da adduo'i har gari yayi haske sannan ta fita domin gaishe da mahaifinta.

Tana zuwa ta iskesa yana waya hak'ora bud'e kamar gonar auduga, yana ganinta yace yauwa gata ma ku gaisa, ya mik'a mata, murya k'asa-k'asa tace "Baba waye?" Ya amsa mata da "Innar ki ce".

Haba aiko nan fa manya suka hau waya, murya sama sai kace tanayi da mutanen dake can bakin titi.

"Na'am Innah ya kuke? Yasu Garba? Wlh inata kewarku, aiko na iso lafiya"

Irin maganganun da suka rik'ayi kenan.

Khalil ya gaji dajin hayaniya don wurin yana saitin window din d'akinsa ne, aiko ya fito a sukwane, yana zuwa yaga ashe hajiya babba ce ke waya.

Yace "ke dallah rufema mutane baki duk kin cika mana unguwa da tsinanniyar muryarki, yanzu kinji mak'ota sun shigo da makamai su d'auka ko ba lafiya, ance miki nan k'auye ne? Kowa nacan kwance kina nan kina ihu, mu nan wuraren ko maza basu irin wayar da kike bare ke, nanfa sai ki kira kanki mace ko? Kalleki da Allah".

Kafin ya rufe baki ta saki wayar tace a'a namiji ce, kai makaho ne baka gani, kai zance ma jibakka don inaga da wuya idan ma kayi sallar asuba, sannan ina ruwanka da muryata a'a ba mak'ota ba Allah yasa dala da goron dutse ne zasu had'unan da makamai ni ina ruwana, malam niba malalaciya bace bana baccin safe kudai da Allah ya d'ora mawa sai ka koma kayita yi amma fa idan zaka iya, magana dai ce wallahi da bakina babu wanda ya isa ya hanani yinta aiba gidan yari aka kawo ni ba ko? Nifa kaga da zaka taimaki kanka daka dena shiga harkata don wallahi ni duk wanda yace ze shiga harkata baze kwashi komai ba sai wahala". Yawale na hanata amma saida takai aya.

Tana kaiwa bata jira taji me ze ceba aiko ta juya gefen Yawale ta zube har k'asa tace "Na manta bamu gaisa ba baba, ina kwana?" Ya amsa da lafiya lau, ta mik'e tsaye ta cigaba da cewa "wai baba da wayar waye mukayi waya dasu Innah?"

"Aiko lawwali ne na kira jiya nace idan ze fita gona yau ya biya nan gida ya basu wayar" inji Yawale.

Maijiddah tace "Allah sarki ai lawwali badai kirki ba"

Sai ji tayi an juyo da ita an sharara mata mari, ashe duk wannan abun yana nan tsaye yanata huci.

Maijiddah tayi mishi-mishi da idanu sannan ta waresu tana k'are ma wanda ya mareta kallo...........

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now