NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
*Ina mik'a sak'on gaisuwa ta ga writers d'ina y'an K'ungiyar 🌈kainuwa, idan kun manta dani toni ban manta daku ba kuna raina, musamman masu zumunci dani haryanzu irin su;*
*Aysha AR Machika, Ummy Ontop, Maimounath (dotana), Aunty Batul, Sa'adatu Alkali da Jiddah Wali, nagode sosai Allah yabar zumunci*🌱 *9* 🌱
Itadai Mariya sam tak'i sakin jikinta, a d'ar-d'ar take har Allah yasa suka gama abunda suke suka fito.
Mariya sai da taga sun fito daga gidan sannan ta samu bakin magana.
"Maijiddah lallai a gaishe ki kinga mamakin da kika bani koko nace kike bani haryanzu kuwa? Hmmm lallai ke ta dabance ni tsoro ma kika bani yasin" ta k'arasa maganar tana mai rik'e baki.
Maijiddah tayi murmushi tace "ai Mariya bakiga komai ba, nifa rashin mutunci na, rashin jina da rashin kunyata suna zowa tare da dalili ne, idan ko baka shiga harkata ba to bazaka tab'a sanin wani mugun hali nawa ba, kibar ganina y'ar k'auye wallahi zuciyata ta y'an birni ce, bazan lamunci raini da wulak'anci ba fa"
"Tofa kidai yi a hankali kinsan ance mai abu sarki" inji Mariya.
Maijiddah tayi wata y'ar iskar dariya tace "to ai nice sarkin kuma ki tsaya zakiga ikon Allah, kinga nidai da Allah abar wannan zance mu koma zancen mu na koyon d'inki, yanzu dai ki bari zan rok'i maigidan ya barni naje Rimi naga Inna idan na dawo kome kenan sai mu d'ora daga inda muka tsaya don nayi kewarta Allah"
Mariya tace "to ai ba damuwa, koyon d'inki ga creative mutane irinku beda wuya, nandanan zaki cafke, kafin ki tafi dai kin fad'a mana"
"Meye kuma 'kiretib' (creative)?" Maijiddah ta tambaya
"Tofa! Toni yama zance miki 'kamar k'irk'ira dai zance, mai fasahar k'irk'irar wani abu' kuma ba kiretib ake cewa ba 'creative zaki ce, saikin rik'a k'ok'arin banbance V da B dakuma P da F, shi turanci yadda kika ga larabci haka yake, da zarar kin canza sunan abu wurin fad'a (pronunciation) to yana iya canza ma'ana don baza'a rasa wata kalma mai irin hakan ba"
Maijiddah ta zaro ido sannan tace "tirk'ashi Allah ya bani ikon kiyayewa, yauwa Mariya don Allah meye ma'anar 'bilej gyal'?"
"Ba bilej gyal ake cewa ba 'Village Girl' zaki ce, suna ne da yake nufin y'ar k'auye ko yarinyar k'auye, kina iya fad'a ma wani hakan a matsayin zagi, wasa kokuma wurin k'ok'arin suffanta inda yarinyar ta fito, yadai danganta da yanayin da kikayi ko aka yi miki maganar"
Maijiddah tace azuciyarta "ooooo wato wannan hayak'in sigarin daman abunda yake nufi kenan duk sanda yace dani haka? To Mariya shi kuma d'an k'auye namiji fa ya za'a kirasa? Sannan ki koyamin wani zagi ko guda biyu ne mai d'an sauk'i"
"Shi kuma kina iya kiransa 'Village boy ko kuma Village man' zagi keko me zakiyi da zagi? amma dai bari na koya miki d'an kad'an, kina iya cewa 'stupid ko idiot' kuma ki kiyaye saboda yawancin hausawan mu bama keba da kike koyo yanzu hatta wanda suka dad'e da wuce nan zakiji basu iya banbance T da D a turanci, zakiji sunce 'Stupit' mai makon 'Stupid'"
Maijiddah tace "woooo malamata yasin ina yinki, aradu akwai bura uba, mu k'arasa kinji"
Suka kwashe da dariya sannan suka cigaba da tafiyarsu suna y'ar firarsu.
******************
Alhaji Abubakar sauk'in kansa yana masifar burge Maijiddah, tun bayan dawowarsa kullun da yamma zakuga yana gaban gate tare da Yawale suna fira kamar yaya da k'ani, gwanin ban sha'awa, kuji makirci irin na mutun indai Alhaji na gida kwanon abincinsa na dabanne ake zuba masa mai shegen kyau, wani lokacin ma suci tare, aiko tunda Hajiya Uwa ta nuna ma Maijiddah wannan had'ad'd'en kwano taci alwashin ko Alhaji nanan ko baya nan aciki zata rik'a zubama ubanta abinci saidai duk tsiyar da za'ayi ayi.