42-44

1.7K 66 4
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Ds page is dedicated 2 my 2nd family Ex-bakorians, u belong here❤👈🏻*

               🌱 *42* 🌱


Maijiddah tayi sauri ta datse kiran, aka sake kira sai bata d'aga ba.

Caaan jimawa kad'an Kamal ya shigo bayan ya sallami bak'insa, Maijiddah ta bishi da ido, yace "lafiya?"

"Lafiya lau, ankira ka yafi a k'irga"

Da sauri ya d'auki wayar ya duba, yana ganin wanda ya kira yace da ita "kinyi picking?"

Kafin ma ta amsa masa ya d'auke idanuwansa daga kallonta ya maidasu kan wayar ya hau kiran number, bugu d'aya aka kama, mudai bamuji me wanda aka kira yake cewa ba saida abunda shi wanda yakira d'in.

"Wr is she? Lemmi talk 2her plz" bayan d'an shiru da yayi sai kuma ya cigaba da magana "hi Anna, hw re u? I'm so sorry Daddy was busy wt oda things wen u called, 4gv me sweery" ya sake yin shiru alamun yana sauraron me magana, sai  zuwa can yace "ohh no sweery Daddy is missing u more, i'll be back soon, doing something now we wl talk ltr ok? Tek kia i luv u"

Ya yanke kiran, yayinda ita kuma Maijiddah keta binsa da ido cike da mamaki, ya kalleta yayi murmushi yace "dat was my Angel Annabelle she used 2 call me Dad, d'iyar wata abokiyar kasuwancin mu ce, y'an nan Nigeria ne bt suna china, her name is Grace inyamura ce she is a single Mother, ina nufin bata da aure, to yarinyar bata tab'a had'uwa da Dad d'inta ba saboda muna gida d'aya kuma tanasona yarinyar nima inasonta sai take d'aukana as Dad d'inta"

Wani irin lumfashi da Maijiddah ta aje bayan da yakai Aya, har saida ya sashi zaro ido.

"To ai abun ne da mamaki, mudai munsan baka da aure, ko budurwa ma baka tab'a yi ba bare har a samu y'ar da zata kiraka babanta, kawai dai kace d'iyar shege ce" cewar Maijiddah.

Kamal ya nema wuri ya zauna yana cewa "kice da har hankalinki ya tashi?"

"Ya hankalina baze tashi ba, tab'di ai ba tashi kad'ai hankalina yayi ba hada b'acin rai ma don har na fara tinanin irin hukuncin dazanyi maka, hmm lallai Allah bakaji yadda gabana yace daram da na d'auka naji ance Dad ba"

"Oh kice kinma d'aga kiran kenan?" Ya sake tambaya.

Cikin y'ar harara tace "eh na d'aga mana da suka dameka da kira"

Murmushi kawai Kamal yayi be sake cewa komai ba.

********

Maijiddah na kwance rigingine tana danna wayarta bayan data gama gwada d'inkin lace d'inta da Mariya ta aiko mata ta mota, sai kiran Fahad ya shigo, taja d'an guntun tsaki alamar bataso kiran ba, sai tak'i d'agawa, bayan data tsinke sai ya sake kira, har saida ta kusan tsinkewa a karo na biyu sannan ta d'aga tayi sallama, ya amsa cike dajin dad'i, dayake wayar Maijiddah tasa k'ara sosai idan kana zaune kusa da ita zaka iya jin abunda me maganar ta waya yake fad'a.

"Kiran farko baki d'agaba nasan k'ila baki kusa da wayar"

"Umnnn" ta amsa a tak'aice.

"Yakike ya gida? Naji dad'i da kika d'aga wayar domin sak'one na aiko miki ta mota tun asuba inada tabbacin ko basu iso garinba suna gab da isowa, na bayar da number ki idan sun iso nasan zasu kiraki kije tasha ki karb'a"

"Sak'o kuma wane irin sak'o?" Maijiddah ta tambaya.

"Karki damu idan kinje zasu baki, ban fad'a maki bane saboda nasan kina iya cewa baki so, shiyasa na turo kawai ta yadda koda ba zaki soba nasan bazaki wulak'antasu ba, kiyi hak'uri da abunda zaki gani bansan abunda kikeso bane kuma baki bani lokaci muyi magana"

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now