24

1.3K 77 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Na sadaukar da wannan shafi ga k'annena ABDULMALIK IBRAHIM KEEGAN da MUHAMMAD (MOMED), Allah ya albarkaci rayuwarku da tamu gabaki d'aya, big sis hrt u irin sosai d'innan.*

             🌱 *24* 🌱

Su Hajiya Uwa nata murna itako Maijiddah saidai ta kallesu ta buntsure baki, a cewarta murnar me zatayi bayan tasan duk zani ce ta tarar da muje, duk halinsu d'aya yaran gidannan, k'ila ma yafi d'an iskan nan Khalil halin banza.

Kamal na shirin zuwa gida gobe shi kuma Alhaji na shirin tafiya paris sati me zuwa, to abunka da masu hannu da shuni mudai saidai muce Alhamdulillah.

******

Maijiddah nata wanke-wanke Hajiya ta shigo kitchen d'in, cikin sakin fuska Maijiddah ta gaishe da Hajiya, itako ta amsa ciki-ciki, itadai gwanata ko a jikinta sai ta cigaba da sabgar gabanki.

"Kinsan meyasa na k'yaleki kike abunda kika gadama kwana biyu? To bawai wani abu bane, ina maki hakane saboda Maigidana amma ni baki tab'a yiman ba, mutun marar kunya irinki beda mazauni a zuciyata" Hajiya ta fad'i haka bayan wani d'an guntun lokaci data d'auka a nan tsaye.

Maijiddah tayi sororo da kwano da soso a hannu tayi murmushi sannan tace "Allah sarki Hajiya wallahi babu komai na fahimci yadda kike ji akaina domin nima hakan take, idan baka da ra'ayin mutun komai zaka iya cewa akansa amma bawai kice marasa kunya basu da mazauni a zuciyarki ba don naga kamar zuciyar taki ma cike take da k'aunar wanda suka haifeni a rashin kunya, ni wallahi hakan ma da kikemin kad'ai ya wadatar dani donni bawai ina neman soyayyarku bane kawai inaso kubarni nayi rawa a gaban hantsi sannan a sakeman marata nayi fitsari, kowa yaje yaja tsawon carbinsa, a k'arshe inaso kiyi hak'uri da abunda na fad'a yanzu don nasan ze b'ata miki rai"

Hajiya Uwa ji tayi kamar tayita dukan y'arbanza amma ba hali, kar ace tayi girman banza karkuma Alhaji yazo ya k'ara goyon bayan Maijiddah menakon ta, saidai tayi tsaki tabar kitchen d'in, Maijiddah ma tsakin tayi gami da murgud'a baki bayan da Hajiya ta fita.

****************

Washe gari.

Da safe da misalin k'arfe goma Mariya ta shigo gidansu Khalil, ta k'ara rashin sa'a Hajiya na kile a parlour, bayan da tayi sallama sai ta gaisheta amma ko kallo bata isheta ba bare ta samu arzik'in amsa, Mariya tayi sororo duk kunya ta kamata, ita bata shiga ciki ba gashi ta kasa juyawa ta fita, sai ga Khalil ya shigo cikin gidan, da alama shima ya fita ne ya dawo, ta gaishesa ya amsa sannan yace "ki shiga ciki Maijiddar nanan ciki"

Ta amsa da "to" cikin hanzari ta wuce, Hajiya ta bishi da ido tana mamakin canji irin wanda take gani kwanan nan a tare da Autanta, shikam be ko kalleta ba ya wuce d'akinsa.

Maijiddah taji an banko d'akinta, tana d'aga kai taga Mariya, sai tayi ajiyar zuciya tace "dallah ni wallahi har kinsa na tsorata ji yadda kika banko d'aki sai raba ido kike kamar kinyi k'arya, hala wani kika tono ya biyoki?"

"Mtsww an fad'a miki ni kece? Ni bana tonon fad'a don bani da k'arfin yinsa wannan saidai ke hajiya Maijiddah" inji Mariya.

Maijiddah tayi y'ar dariya tace "aato ai dole na tambaya saboda naga kin shigo kinata tattaro lumfashi kina watso shi babu shiri"

Mariya ta nema bakin gado ta zauna gami da sake sauke wani lumfashin a karo na babu adadi, sai tace "ba dole ki ganni haka ba, karo da Hajiya nayi a parlour, na gaisheta ko kallo ban isheta ba, nayi k'erere saida Allah ya taimakeni abokin rigimarki yazo yace inshiga kina ciki, nidai wallahi zanzo na dena shigowa gidannan kedai kin rik'a zuwa namu gidan don bana iya jure kad'awar y'an hanji aduk sanda na shigo"

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now