NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *7* 🌱
Ba'a ce ta shigo ba amma tayo gaba abunta kamar gidansu, saida tad'an shigo cikin gidan sannan ta juyo ta kalli Mariya tace "yadai? Naga kamar bakiso zuwana ba?"
"Laaa kai haba yazaki ce banso zuwanki ba, mu shiga ciki mamanmu ma tana nan" Mariya ta k'arasa maganar tana d'an guntun murmushin dole.
Takai ta har inda mamansu take suka gaisa da Maijiddah.
"Mama sunanta Maijiddah sabuwar mai aikin gidan Alhaji Abdullahi ce kuma babbar d'iyar baba yawale, tanada hankali"
Wani irin kallon gefe Maman tayima Mariya irin na gulma d'innan, batasan dama ta riga ta zare bunun ba (ta fad'a mata ba).
Sai tace "Allah sarki sannu, kice kakata ce ma (Hauwa'u), to Allah ya taimaka"
Suka amsa da "Amin"
Suka tashi Mariya taja Maijiddah d'akinta, sai kame-kame take hardai ta gaji da kwana-kwanar tace "Maijiddah kiyi hak'uri wancan karon kin tafi kin barni da tinani sai wani iri nake ji, wallahi bansan cewa Baba Yawale mahaifinki bane"
Maijiddah tayi sauri ta amshe "da baki fad'aman ba ko? To ai gara da akai haka kinga yanzu naji inda tattalin arzik'in mu ke tafiya, kinga niba wannan ta kawoni ba don ta riga ta wuce, kud'in uba na nedai baku k'ara ci, wanda kukaci a baya ma zan fanshe"
Zaro ido Mariya tayi don bata fahimci yaren nan na zata fanshe ba,
Maijiddah ta karanta fuskarta sai tayi y'ar dariya tace "ke wasa nake miki ta ina zan fanshe ai kunci bulis kawai hajiyata, maganin maza irinsu kenan"
Ta k'ara da cewa "Nasan kinyi karatun boko ko Mariya?"
Mariya da sauri tace "eh nayi wani abu?"
"Turanci nakeso ki fara koyamin" Maijiddah ta amsa.
"Tofa, haba Maijiddah ai yanzu kin wuce koyon turanci saidai wasu abubuwan, kinga na iya d'inki kuma girke-girke na karanta a makaranta meze hana idan kinaso na koya miki su?"
Maijiddah tace "ahab ashe dai da gaske zan fanshe d'in? To inaso ki rik'a koyamin dika idan ba damuwa, sannan ya zakice nayi girma da koyon turanci kufa ke cewa ba'a girma da koyon ilimi, nifa basai na k'ware ba don ance tun ran gini tun ran zane, amma tunda yanzu na tsinci dami a kala kawai inaso na koyi koda irin na yau da kullun ne"
Mariya tace "ai sa kai ne har k'warewar ma kina iya yi don naga kamar kinada k'wazo"
Murmushi Maijiddah tayi sannan tace "Bakiyi k'arya ba kaina yana ja, idan kinaso kema ina iya koya miki na addini daidai iyawata"
"Ke nafa yi sauka, ni yanzu yaushe rabona ma da islamiyya ai tunda mukayi sauka" inji Mariya.
"Kin sauka a mashin ko a mota? Don bakiyi kama da saukakka ba, ai matsalarku kenan wai don kunyi sauka shikenan kun gama karatu, shifa ilimin addini kogi ne ba'a tab'a gama shi, ba kamar na boko bane da idan kunkai wani mataki sai ace kun k'are ba, nikam nan har so nake na gano wata islamiyyah nan kusa insamu inshiga kota Asabar da lahadi ce kad'ai"
Mariya tace "tabd'i sannu da k'ok'ari aini gaskiya na tsinci na tsinta, tunda dai zan iya cika sallata ai shikenan, nan gaba idan na samu dama na koma amma badai yanzu ba"
"Kanki kika yiwa ba Maijiddah ba wallahi, nidai yanzu samo man takarda mu fara koda kalmomi biyar ne kafin na siyo littafina"
Mariya tayi murmushi ta mik'e domin nemo littafi da biro.
Bayan ta d'auko biron ta zauna sai tace "to yanzu kamar su me da su me kikeso ki fara koyo?"
"Kinga ina dai irin na yau da kullun d'innan, kamar su Zo, tafi, to, eh, a'a, abinci, ruwa, zauna, ci, dadai sauransu kafin muzo kan su zagi kuma" cewar Maijiddah.
Mariya tayi dariya.
"To kinga dai a turance idan akace 'come' ana nufin zo, 'go' na nufin tafi, 'okay' kuma to, 'yes' eh, 'no' a'a, 'food' abinci, 'water' ruwa, 'sit' zauna sai kuma 'eat' yana nufin ci"Tabi ta rurrubuta mata su a tsaye yadda zata gane.
Maijiddah tayita maimaitawa Mariya na gyara mata, sai mariya tace "to wai Maijiddah keda ya kamata ki fara da koyon hausa saiki koyi turanci kuma?"
"Ke waya ce miki ban iya hausa ba, nad'an iyata a rubuce sama-sama, saboda islamiyar mu wurin koyon haruffan larabci da sunayen larabci akan yi mana fassara a rubuce da hausa, bandai k'ware ba amma na iya"
Ta lumfasa sannan ta k'ara da cewa "bari na tashi da wannan tun kafin a aiko kirana koda yake ba'asan inda nayi ba, yanzu dai sai yaushe zamu fara koyon sauran? Kokuma dai bari zan dawo sai mu tattauna dakyau"
Mariya tace "to ba damuwa sai kin dawo d'in".
Ta fito har gaban gate rakiya, bayan sunyi sallama har ta juya sai kuma ta juyo tace da Mariya "Nafa gode d'iyar Babanmu"
Mariya tace "godema Allah, aidai gashi zamu fanshe"
Kowa ya tafi yana dariya.
**********************
Ba sauran zama wai an d'aurama karya aure, Maijiddah jinta take wata hamshak'iyar baturiya, ko aiki take ita kad'ai zaka ga tana mui-mui da baki.
Yau bayan ta gama girki tana nan kitchen bata kaiga juyewa ba saiga Khalil yazo d'ibar ruwa a fridge, aiko sai Maijiddah ta wani gyara tsayuwa aka wani d'aure fuska ita a dole yau zata nuna masa taji turanci, kamar daga sama sai ji yayi tace "Khalil Come"
Haushi ya kamasa bayan daya gama zuba mata ido sannan yace "is dat a command? U re nt serious"
A yadda tayi maganar kamar wata uwarsa.
Ya yamutse fuska yana ganin rainin wayo
Ta k'ara cewa "Khalil come eat poot (food)"
Ai sai wata iriyar dariya mai shegen k'arfi ta kufce masa, sosai ta bashi dariya don haka dariyar yake da gaske hada k'walla, Maijiddah ta rik'a mamakin to me yakema dariya kodai ba daidai ta karanta ba koko Mariya shirme ta koya mata, kallonsa ta rik'ayi da yana dariya don bata tab'a ganin dariyarsa ba tunda tazo gidan ashe haka yake idan yana dariya 👌.
Ta juya da sauri ta nufi d'akinta, ta d'auko takardar nan taga fa yadda dai aka rubuta mata haka ta fad'a, aiko tace "zanko je na sami Mariya don inaga itace y'ar iskar data koya min wannan haukar"
Ai bata jira washe gari ba, a ranar da yamma taje gidan su Mariya, ta kwashe duk yadda akai ta fad'ama Mariya, itama Mariya tayi dariya mai isarta sannan tace,
"To ai kema laifinki ne Maijiddah shi turanci ba haka yake ba, niban koya miki magana ba, sunayen abubuwa na koya miki, sannan kema kinji fa a yadda kikace kinyi masa maganar, a hausance fa haka kika ce masa 'zo ci abinci' kuma ma fuska d'aure kamar dole"
Ta cigaba da cewa "cewa zakiyi 'come and eat food' ma'ana 'zo kaci abinci' kuma ba 'poot' ake cewa ba 'food' zaki ce.
Nandai tad'an k'ara nunnuna mata wasu abubuwan kafin daga bisani ta wuce gida.
******************
Yau Alhaji Abdullahi ke dawowa gida, Khalil duk shegen yawonsa yau ya natsu be fita ko ina ba, sai zaman parlour daya aure sa.
Maijiddah ta shigo parlour da burner d'inta a hannu tanasa turaren wuta.
Khalil ya kalleta yayi tsaki yace " ke dallah bar wurinnan, kina ganin ina zaune kinzo kinata bad'e mutane da hayaki sai kace wata y'ar bori"
Maijiddah tace "oh sorry fa da Allah, ina mutanen suke? Nidai Khalil kad'ai nagani banga mutun ba, sannan kada kadamu wannan hayak'in bamai yaji bane, baya illa wannan k'amshi gareshi"..........