NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
*MARYAM GATAWA ga gaisuwata ta musamman gareki keda mutanenki masoya wannan littafi, ki sheda masu nima ina yinsu iya wuya, ana mugun tare 🤝🏼😘*
🌱 *38* 🌱
Maijiddah ta cigaba da cewa,
"Hajiya duk iya tsanarki da abu idan Allah ya riga ya rubuta shi a tsarin rayuwa to sai ya faru, ki d'auka zamana daku k'addara ce wadda baki isa ki canza ba, ina rongwanta miki saboda d'anki Kamal, amma ki sani banasonki kamar yadda bakya sona"
Daidai wurin Kamal ya shigo ya iske Maijiddah takai Ayar maganarta rai b'ace, aiko Hajiya Uwa na ganinsa ta fashe da kuka tana fad'in,
"Yanzu ace kamar ni, kamarni bani da k'ima da daraja a idon wannan fitsararriyar yarinyar, tazo ta tasani sai zagi take, idan na fad'a maku halinta ai baku yadda, yanzu gashi nan ka gani da idonka"
Kamal ya kalli Maijiddah, yaga ranta b'ace kamar zata kai hannu, ta cika tayi faful, sannan ya juya ya kalli Hajiya dake kukan munafurci yace,
"Maijiddah Uwa kamar mahaifiya take a wurinki, yadda zamu girmama ta haka muke tsammani daga gareki kema, kamar yadda iyaye ke hak'uri da y'ay'ansu kuma suke sonsu a duk yadda suke, to suma y'ay'a hakan ya zama dole agaresu"
"Me kake nufi?" Maijiddah ta tambaya gami da kallonsa cikin harara, ranta b'ace.
"Ina nufin baki kyauta ba abunda kikai yanzu, be kuma kamata ba, da Allah ki kiyaye domin banason abunda ze b'atama mahaifiyata rai, bama kamar a wannan lokacin da tayi rashi, rarrashinta ya kamata ayi bawai arik'a b'ata mata rai ba" magana yake amma baya kallon fuskar Maijiddah.
Itako k'ura masa ido tayi tanaso ya d'ago taga idanun me magana, tayi shiru nad'an guntun lokaci sannan tace,
"Ai ba'a shari'a haka, kaji me Hajiya tace ai nima kamata yayi ka saurari abunda ya faru daga b'angare na, nida mahaifina fa ta kira m......."
"Koma meya faru banason ji, Uwa bazatayi miki k'arya ba, don haka a kiyaye don Allah"
Ai sai Maijiddah ta kwashi jiki a fusace ta wuce d'akinta, wani d'aci d'aci taji ranta yana mata, mamaki ta rik'ayi waiko dagaske Kamal ne koko dai ya akai.
Hajiya Uwa kam dad'i fal ranta, hankalin d'anta ya fara dawowa jikinsa, acewarta.
Babu wani aiki a gidan sai zuwa yamma kasancewar azumi ne, hakan yasa Maijiddah bata wani cika fitowa waje ba, da zarar tayi aikinta na safe sai ta koma d'aki, ta hauyin karatun Qur'ani, lazumi saiko bacci, sai idan Asr tayi ta fito ta fara aikin kayan bud'a baki.
*******
Tana kitchen tana aiki ita kad'ai baiwar Allah, ga azumin yau yana garata gashi ranta b'ace yake sakamakon abunda ya faru d'azu tsakaninta da Hajiya Uwa da Kamal.
Girke-girke take kala-kala kunsan mai azumi da zari, sai kawai taji kuka ya taho mata babu dalili, hawaye kawai ke zuba babu duka babu zagi, ji tayi kawai tanason kasancewa da mahaifiyarta, komin dad'in gidan wani babu ya gidanku haka komin dad'in iyayen wani babu ya naka, ta share hawayenta ta cigaba da aiki.
Muryar Kamal ta jiyo daga bayanta yana cewa "mezan tayaki dashi k'anwata?"
Koda ta juyo wani irin mugun kallo ta wurga masa sannan ta juya ta cigaba da aikinta batare data tanka masa ba.
Yayi tsaye k'erere a wurin yana binta da ido, yaje kusa da ita ya rik'e wuk'ar da take yanka yanata kallonta sai ta sakar masa wuk'ar ta kama wani abun, ya k'ara matsawa wurinta yace "Maijiddah kiyiman magana"
