NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *18* 🌱
Khalil ya saki hannuwansa ya tab'e baki gami da d'aga kafad'a, ma'ana "ke kika sani" sannan ya shige ciki, itama Maijiddan binsa tayi a baya don dama tanada niyar shiga cikin shine dai be fuskanci hakan ba, yayi saurin yi mata katsalandan.
****************
Gidan yayi babu dad'i, sai yayi shiru kamar ba kowa, kowa acikinsu yayi kewar yaran nan amma ba kamar Maijiddah, aiko sai ta koma kunna abokiyar firarta wato chinar wayarta mai shegen k'ara, idan bata kunna karatun Qur'ani ba to zata kunna wak'a, gashi kusan b'angare d'aya d'akinta yake dana Khalil, hakan yasa yafi kowa shan wahalar wannan sauti, gashi kullun cikin aiki wayar take safe, rana, dare, sai kace shan paracetamol.
******
Bayan kwanaki kad'an.Wasu Samari su uku daga Minna suka bak'unci gidan nasu yau, daga ganinsu basai an fad'a ba, kasan yan hutu ne, yaran masu hannu da shuni.
Kasancewar ansan da zuwansu yasa aka shirya masu tarba ta musamman, Khalil yace Maijiddah ta dafa ma bak'insa abincin mai dad'i, duk a zatonsa zata girka irinsu, fried rice wt peppered chicken ko kuma coconut rice kodai irin su spags wt veggies dai da sauransu, ashe tana can tayi k'uri tanata girka abincin gargajiya, koma wuya bataji, dambun shinkafa tayi wanda yasha kayan had'i irin na zamani, tayi masa vegetable salad da peppered meat 😋, a gefe guda kuma wainar masara (masa) tayi, ga lafiyayyen dakakken k'ulinta wanda shima yaji had'i, don k'uli, yaji, kayan k'amshi, maggi, gishiri da y'ar albasa tasa ta daka, yad'au k'amshi kamar k'ulin tsiren nama, idan muka dawo b'angaren abunsha kuma, mangoro ne ta b'are bayansa ta yanyanka ta markad'a, shima ta had'a masa kayan da duk lemon mangoro ke buk'ata, mango juice dai zance maku atak'aice, basai naje ga yadda ta had'a komai ba, ga lafiyayyen farfesun kifi datayi (wai harna had'e miyau).
Tun safe ta fara aikin amma bata kammala komai ba sai zuwa wuraren la'asar, kasancewar hannu d'aya ne ita kad'ai keyi, Hajiya Uwa batanan kuma koda tana nan bawai tayata zatayi ba.
Bayan da bak'in Khalil suka huta sukayi Sallah, sai ya fito domin umartar Maijiddah data kawo masu abinci, d'akinta ya sameta tad'an kwanta idanuwanta a rufe tana hutawa domin ta aikatu.
"Zo muje kiba bak'i abinci" inji Khalil.
Ga mamakina sai naga Maijiddah bata tanka ba saidai kawai ta mik'e ta kama hanyar kitchen (yau y'an sauk'in kai ne akan nata inaga, don abun da mamaki),
Shiko yana biye da ita har suka shiga kitchen d'in.K'amshin girke-girken nata ya daki hancinsa, ba shiri ya fara had'iyar miyau sai kace tsohon maye, shima ya tayata d'aukan kayan abincin, taje ta baje masu shi a parlour, ta gaishe su fuskarta babu walwala sannan ta koma d'aki.
Wani acikin abokin nasu mai suna Fahad ya bita da ido, har saida wani ya tab'a shi,
"Kabi ka k'ura ma yarinya ido lafiya?"
Fahad ya juya ya kalli Khalil yace "Man wannan yarinyar fa daga ina kuka samota? don nasan kaine auta a gidannan"
Khalil yayi murmushi sannan yace "kaji d'an iska ina ruwanka da yarinyar mutane, kaidai ci abinci malam"
"Wallahi ba wasa nake ba, kyakkyawar yarinya da ita, Allah kaji na rantse tayimin, ya za'ayi ne don dagaske fa nake?" Fahad ya fad'i haka cikin zumud'i.
Lokaci guda yanayin Khalil ya canza kuma baisan dalili ba, besan lokacin daya ce masa "aiko ina tinanin ta kusa aure ma don kasan yaran k'auye tun suna ciki ake bada su"
Fahad ze k'ara magana Khalil ya dakatar dashi ta hanyar bud'e abincin da suka kawo, sai be sake cewa komai ba ya maida hankalinsa ga abincin.
Warmer Waina ya fara bud'ewa, yana bud'e wata y'ar roba mai marfi sai yaga dakakken k'uli sai kace wanda zasuci rogo, ji yayi zuciyarsa na tafasa, a fusace ya k'wallama Maijiddah kira, kiran da har saida Yawale dake gate yaji.
