29

1.2K 60 2
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Aysha Sada Machika Novels group, ku huta girmanku ne❤*

*Fa'izah Bukar u re special💋*

               🌱 *29* 🌱

Tana fita ga mamakinta sai taga motar Khalil, shima yana ganinta ya fito daga cikin motar.

"Cabd'i lallai ma wannan mutunen, ashe yanada tinani" inji Maijiddah ta fad'a a zuciyarta.

Ta k'arasa jikin motar, yaukam anyi gaisawar mutunci kamar ba'a tab'a fad'a ba.

"Wai kaine kuwa? Me kazo yi nan garin?" Ta tambaya.

"Wannan yarinyar y'ar rainin hankali ce bata gane kome zanyi, danayi abu saita fassara shi ba daidai ba" wannan shine abunda ya fad'a a tasa zuciyar, amma a fili sai yad'an saki murmushi yace "babu komai nazo duba jikin Mamanki ne dakuma ganin ya kike"

Maijiddah ta zaro ido tace "don girman Allah?, lallai anya kuwa, hmm kazo duba ya nake a gidan namu? Kodai kana tashi daga bacci kayo nan?"

"Ban gane me kike nufi ba?" Ya tambayeta gami da yamutse fuska.

"Ina nufin kodai cikin magagin bacci kayo nan ne? Koko nice ke baccin"

Sai Khalil ya had'e fuska, beji dad'i ba, yana k'ok'arin yaga yana faranta mata, ta rik'a jin dad'insa kamar yadda take jin dad'in Kamal amma da yayi abu saita gwasale shi.

Maijiddah data lura beji dad'i ba sai ta k'ak'alo murmushi tace "kaga wasa nake maka, nima naji dad'in zuwanka sosai wallahi, mu shiga ciki to"

Ta shiga gaba yana binta a baya.

Suka k'arasa ciki Maijiddah na cike da mamakin ganinsa, tunda Allah yasa suka taho yake kallon Maijiddah ta baya sai kace *Nameer*🤣.

Gidan yasha shara, an gyarashi tsaf (kusani itafa tsafta bata ga birni bata ga k'auye).

Khalil ya zauna bayan da aka shinfid'a masa tabarma, ya gaishe da Yabi cike da ladabi kamar ba shiba, cikin sakin fuska ta amsa.

"Banfa gane shiba Maijiddah daga ina?" Yabi ta tambaya.

Maijiddah ta gyara zama sannan tace "uhmm Innah Autan Hajiya Uwa ne fa Khalil".

" Auhooo Allah sarki, sannu kaji ya mutanen gidan?"

"Lafiya k'alau" ya amsa atak'aice.

Daganan be sake cewa komai ba saboda be iya ba, saidai ya kifa kai k'asa kamar wani munafiki.

Maijiddah nata kallonsa tana dariyar zuci.

Saima itace ta rik'a tononsa.

"Innah kinga abokin fad'a na ko?"

Yabi dai tayi murmushi.

Ya gaji da sunkuye-sunkuyen ya tashi yace ze tafi.

"Da wuri haka" yabi ta tambaya.

Yayi murmushi kawai yana sosa kai.

Yabi tace "ka gaishe da mutanen gida", tayita sa masa albarka.

A karo na farko da ya tab'a yima wani babban mutun aikin k'warai dahar aka sa masa albarka, sai kuma yaji dad'i sosai marar misaltuwa.

Maijiddah ta fito rakasa mota, da suka iso ya jingina jikin mota ya linke hannuwa yace "yaushe zaki dawo gida?"

Ta sake zaro ido tace "wai dagaske kaine? Nifa mamaki kake bani"

"Yauwa Maijiddah wai meyasa ba zamu zama frnds ba, wannan fad'ace-fad'acen da muke ya kamata mu dena" Khalil ya fad'a a gadarance.

"Sai sanda ka koyi d'aukar kuskurenka ka kuma iya bada hak'uri, sannan ka koyi girmama na gaba dakai, ka koyi daraja mutane, ka canza ka dena duk wasu abubuwa da basu dakyau, sai sanda ka girma ka mallaki hankalin kanka" Maijiddah ta fad'i haka bilhaqqi da gaskiya.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now