15

1.7K 82 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                🌱 *15* 🌱

Hakanan dai ya daure ya cigaba da wankan, yanayi yana susa, yaji dai abun kaiiii bafa sauk'i ai ba shiri ya fito, ya fara soshe-soshe kamar mahaukaci, shine sosa kai, k'afa, wuya, kai ko ina ma har parlourn oga sosawa yake, ya rasa meke faruwa.

Kirtar jikinsa yake, dirza yake, sai ya koma ya k'ara d'auraye jikin da ruwa a tinaninsa ze dena, habaaa aisai ya k'ara kacamewa, yaga dai kar ya mutu shi kad'ai a d'aki babu wanda ya sani, aifa yasa boxers babu riga yayo waje.

Su Hajiya Uwa ya tarar har lokacin suna nan parlour kan dining, tare Hajiya da Hadiza suka mik'e suna tambayar lafiya, ganin yadda ya shigo a rud'e yanata susar jiki, duk ya rud'e ya firgice kamar zeyi kuka.

Suka matso kusa dashi fad'i yake "sosa min nan, sosa min can, ba can ba nan" suna sosa masa suna kallon juna, Hajiya Uwa ta fashe da kuka tace "kinga irin abunda nake gudu ko Hadiza? Kin gani ko? Wannan shaye-shayen beda wani amfani, innalillahi wa inna ilaihirrajiun me nake gani haka ni jikar Amadu, da haka yaron Hajiya Saude ya fara yanzu gashinan ya zama cikakken mahaukaci, hauka yake tuburan"

Khalil ga k'ai-k'ai ga haushin maganganun Hajiya, ya buga wata Uwar tsawa yace "ni ku sosa man nace haba da Allah kun tsaya sai wani maganar hauka kuke, wayace hauka nake? Ina cikin hankali na, wallahi ruwan gidannan kar kuyi wanka dashi don wani abu ya same shi, sosa min Uwa, don Allah ku sosa min"

Ya koma kamar wani zararre, Hajiya Uwa ta k'ara fashewa da kuka tace "wayyo Allah Hadiza jeki tado man Babanku, muje mukai yaron nan asibiti ya tab'u, ruwan gidan nima ai dashi nayi wanka"

Hadiza ta tafi kiran Alhaji tabar Hajiya nata sosa masa.

Maijiddah ta shigo parlour ta gansu, da sauri tace "Innalillahi Hajiya meya same shi?" Ko kallonta batayi ba, ta matso kusa dasu ta kalli Khalil fuskarsa duk tayi kwab'a-kwab'a tace "Sannu Khalil, meke damunka?"

Da sauri kamar ze taune harshe yace "Yauwa, yauwa, yauwa nagode, sosamin kema Jiddah, don Allah Jiddah ki sosa min"

Dariya ta kusan kufce mata amma ta had'iye tace "sannu ga Hajiya nan tana sosa maka, sannu kaji ko, Allah ya sauk'e"

Alhaji ya fito a rud'e da Jallabiya jikinsa, yaga wannan ikon Allah, yayi d'an guntun tsaki yace "to kallesa don girman Allah, yanzu wa gari ya waya? Kullun maganar dai d'aya ce, fad'an dai d'aya ne, addu'ar ma d'aya ce, ko hakkin yaran mutane ma ai baze barka ba, baka kyauta ma kanka ba Ibrahim, Allah ya shirya"

Hajiya cikin kuka tace "haba Alhaji yanzu duk ba lokacin wannan maganar bane, muje mu kaisa asibiti a duba masa shi" tarik'a kuka sosai.

Shidai Khalil abun sai ya had'e masa goma da ashirin, ga k'ai-k'ai ga zargi da maganganun da suke masa bayan shi yasan beyi komai ba, ransa ya k'ara b'aci sai hawaye.

Alhaji yace a d'auko masa riga, shiko fad'i yake "don Allah ku sosa min karku samin riga", Alhaji yace ma Hadiza " maza ki d'auko masa riga sakaran banza kawai, dan ubanka ba riga zamu kaika asibitin?, ke kuma je ki d'auko mayafinki" Yace da Hajiya.

Ta shiga ta d'ako mayafi, itako Maijiddah fad'i take "sannu Allah ya baka lafiya, Allah yasa kaffara ce"

Hajiya ta kamasa suka fito gaban gate aka sashi mota, saiga Hadiza ta fito da rigar tasa aka sa masa a motar.

Zata bisu Alhaji yace ta zauna tunda abun kamar hauka ne gara su tafi da namiji, sai yace da Yawale ya shiga baya wurin Khalil d'in su tafi asibiti, yawale ya shiga suka wuce.

Maijiddah ta shiga  d'aki ta rik'a tsalle har Safwan ya tashi, ta turasa waje tace ya tafi wurin mamansa, yana fita ta maida k'ofa ta rufe ta cigaba da rawa tana jin dad'i.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now