NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *11* 🌱
Ushe tace "wannan shine abun tambaya, wallahi Yabi duniyar nan tsoro take bani wanda bakayi tinani ba ma sai kaga ya aikata wani mummunan abun"
Yabi ta mik'e tace "kedai Allah yasa mu dace"
Ta shiga d'ayan d'akin ta d'auko ma Maijiddah faten tsaki yasha zogale da wake ta kawo mata sannan ta d'ebo mata ruwa a mod'a (cup) ta aje mata a gabanta.
Maijiddah taji dad'in ganin faten nan domin tayi kewar irin wannan abincin nasu na k'auye sosai, bama kamar su ganyayyaki da suke k'wad'awa da k'uli, garin gero kokuma daddawa, (Veggies) irin su zogale, yad'iya, alehu, tafasa, rama, yakuwa, dinkim, k'awuri dadai sauransu.
Taci faten nan sosai hada tand'e baki saidai bata iya cinyesa dika ba saboda d'an zuwanta birni cikinta yad'an fara ragewa, irin mugun cin da take da yanzu ta rage.***********
Da yammar ranar, Ushe ta fita zuwa gidan k'awarta barka.
Yabi ta fiddo tsarabar da Maijiddah tayi tanata faman kasa wa za'a kaima mak'ota, y'an uwa da abokan arziki, sai Maijiddah taje ta d'auko sak'on da Yawale ya bata da kuma kud'in da Alhaji Abdullahi ya bata.
Ta zauna kusa da ita ta mik'a mata tace "Inna kinga wannan Baba yace a kawo maki kiyi cefanen gida, wannan kuma Alhaji Abdullahi ya bani su, dubu Hamsin ne ya bani na cire dubu biyu nayi kud'in mota dakuma tsaraba, yanzu ga arba'in da takwas nan, saiki had'a ki juya wurin kasuwancin ki"
Habaaa ai sai Yabi ta tsaya cak da abunda take, hawayen dad'i ya fara zubo mata ta karb'i kud'in a hannunta ta jujjuya tace "yanzu wannan uban kud'in duk daga babanku? to shidai ya rik'e wasu ko?"
Tausayin Yabi ya kama Maijiddah, a cikin ranta tace "wayyo ita tama fi damuwa dashi, shiko da yana can yana bada su inda be dace ba"
A fili tace "karki damu Inna ai daga yanzu zaki rik'a samun sak'on Baba akai-akai kuma zaku rik'a ganinsa sosai domin yana samu yanzu ba laifi"
"To Alhamdulillahi ubangiji Allah ya k'ara bud'i yakuma k'ara rufa asiri, shima wannan mutune Alhaji Abdullahi Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yayi masa abunda yake mana, Allah ya biya masa buk'atunsa na alkhairi duniya da lahira" ta k'arasa maganar tana mai goge hawaye da hab'ar zaninta hada fyace y'ar majina"
Maijiddah ta amsa da "Amin, wai ina yaran gidannan najisu shiru haryanzu basu dawo ba?"
"Aiko suna gidan Iyatu k'ila daga can sun wuce hayi"
Maijiddah tad'an jinjina tace "hayi kuma Innah me zasu je yi hayi?"
"Islamiya mana ai yanzu babu me zuwa islamiyar bakin layi saboda abunda Shehu ladan yayi, kinsan abunki da karkara Masallacin nan ma ba kowa ne ke zuwa ba yanzu" Yabi ta amsa.
"Waini Inna ki bani labari wai garin yaya haka ta faru? Kodai k'azafi aka yima Malam shehu ne? Saboda ni har yanzu zuciyata ta kasa yadda cewa ze iya aikata hakan"
Yabi ta gyara zama tace "aiko zuciyarki ta yadda domin abun ba'a kama yake ba, ai idan baki manta ba ansha yin jita-jita kan cewar yana b'ata yara amma ba'a yadda ba kowa da abunda yake cewa, kinsan idan Allah ya tashi tona maka asiri ranar nan bayan an idar da sallar isha'i kowa ya watse sai kai Ubale mijin Haire da kaje da d'anka masallaci sai ya baro takalmansa can, bayan sun koma gida yaro ya addabesu ya damesu da kuka shifa sai an nemo masa takalmansa, Ubale yace bari ya koma masallaci tunda yanzu duk an watse ya duba ya gani ko za'a ganshi, to wurin dubawar ne ya rik'a zagaye masallacin har yazo ta bayan masallaci ga duhu wurin, sai ya rik'a jin nishi sama sama, aiko ya fiddo cocilarsa daga aljuhu mai shegen haske ya haskasu, meze gani sai yaga Shehu Ladan a kwale yanata amfani da wannan yaro, yaron can na sak'o dan gidan wannan natar uhmm bani sunanta, kai haba kinji sunan nan ya shige man, to shidai, aiko sukayi tsuru-tsuru, Shehu ya fara rok'on Ubale don girman Allah ya rufa masa asiri, aiko Ubale yaje ya rik'esu gam ya rik'a ihu yana kiran jama'a, nandanan aka taru ga Shehu wando sauke shima yaron haka, suka rik'a bugunsa, aka tambayi yaron yace ai sun dad'e yana masa haka, bama shi kad'ai bane hada yaron wane da wane duk ya lissafa, yace idan ya gama amfani dasu sai ya basu goma ko ashirin suje su sayi wani abu, aiko yaci bugu da jifa dak'yar yasha, cikin darennan aka koresa garinnan, yana raye baya raye yanzu Allah shine masani amma fa anyi masa jina-jina"