20

1.2K 68 1
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                🌱 *20* 🌱

Ya gama tsayuwarsa yabar wurin.

Wata iriyar yunwa ta taso masa, yana rawar jiki ya shiga kitchen, saiga malam Khalil d'inku da cin wainar masara da k'ulin da akayi tun rana hada tand'e baki.

*********

Washe gari.

Kamar kullun tunda safe Maijiddah ta hau aikace-aikacen ta ganin tad'an samu sauk'i, sam bata da son jiki akwaita akwai himma, lokaci guda ta turare gidan da k'amshi, bayan ta gama gyaran gidan ta fad'a kitchen, ta d'iba wake ta sassafa ta wanke sannan tasa a blender ta markad'a, k'osai da kunun gyad'a ta kud'iri niyyar yi masu, ruwan bunu ko shi daman wannan k'aida ne akwaishi safe, rana, dare, kullun baka rasa shi cikin tea flask.

Haka ta tak'ark'ara ta kammala komai, sannan ta fita ta gaida Yawale tare da kai masa abincinsa, yayi mata ya jiki, ta amsa "da sauk'i" yace "to Allah ya k'ara afuwa, Allah yayi albarka".

Ta koma cikin gida ta shiga d'akinta ta kwanta tana huta gajiya.

*****

Hajiya Uwa ita ta fara fitowa, taga an gyara gida tsaf ga k'amshin girki na tashi, bata zame ko ina ba sai d'akin Maijiddah, tana tura k'ofar taji a rufe, sai ranta ya bata cewa k'ila bacci ta koma.

Murmushi Hajiya Uwa tayi mai kamar dariya domin ko firar da take a zuci ce ta kusa fitowa fili, cewa tayi "hmm ashe akwai abunda kesa yarinyar nan natsuwa, badon-badon ba dasai nayita addu'a kar taji sauk'i don gidan yafi dad'i a haka".

********

Khalil ma yana tashi d'akin Maijiddah ya nufa, har lokacin d'akin a rufe yake, hada k'arfin halin k'wank'wasawa, amma shiru ba'a bud'e ba, hakanan ya koma d'akin da bak'insa suke.

Bayan sun gaisa da juna, Fahad yace "wai ya jikin Jiddah kuwa ka dubo ta?"

"Mtsw bansani ba gaskiya, nadai je dubata d'akin a rufe, duk ta k'are bacci take" Khalil ya amsa cikin sigar kulawa..

Fahad yace "aiko dole ta bud'e k'ofar nan saboda allurar da za'ayi mata"

Wuri Khalil ya nema ya zauna sannan yace "wai ita allurar nan har nawa ce ne eh?"

Gabaki d'ayansu suka kwashe da dariya, cikin sauran biyun wani yace "ji yadda kayi maganar hada b'ata fuska kamar ance kai za'a yima allurar"

Fahad yace "oowoo kuma dai fad'a"

Firarsu suka cigaba dayi kafin daga bisani Khalil ya fita domin yima Hajiya maganar yadda za'ayi da kayan breakfast d'insu tunda Maijiddah bata lafiya, ga mamakinsa sai yaga gidan tsaf-tsaf an gyara shi, ga kuma alamu da suka nuna cewar har breakfast an gama, saidai dukda ganin hakan bai hanasa k'arasawa wurin Hajiya ba.

D'akin a bud'e ya iskeshi don haka besha wuyar k'wank'wasawa ba, bayan ya gaisheta yad'an zauna gefen gadon ta irin zaman nan mai kamar tsugunni yace "Uwa da na fito nayi miki maganar breakfast sai naga kamar ma kun kammala komai"

"Ta kammala dai" ta fad'i hakan atak'aice.

Yace "Wa? Wai Jiddah?"

Hajiya Uwa ta d'auko wayarta tana dannawa batare data kallesa ba tace "eh ita mana, don nima lokacin dana tashi na tarar ta gama komai"

"Wow ds gal is rly something, dukda bata lafiyan Allah sarki, wallahi Uwa bakiji jikinta ba jiya d'innan" inji Khalil.

Hajiya Uwa tabar kallon waya ta maida kallonta kansa tace "ta ina kaji jikin nata?"

"Ta ina kuma, kamarya? Ina nufin jiya taji jiki gaskiya ga aiki data sha, ta bani tausai sosai Allah" ya amsa.

Ta tab'e baki gami da cewa "yau kuma?"

Bece da ita komai ba.

Suna nan zaune Kamal ya kira Hajiya suka gaisa, ya sheda mata yana nan dawowa gida kwanan nan insha Allah, taji dad'i sosai Khalil ma haka, dukda cewa basu wani jituwa don halayyarsu gaba d'ayanta sab'anin ta junansu ne.

********

Bayan sun kammala breakfast d'insu Khalil ya k'ara komawa d'akin Maijiddah amma har lokacin bata bud'e ba, babu dalili sai tsintar kansa kawai yayi cikin damuwa, wani sashe acikin ransa ya rika rad'a masa cewa kodai akwai matsala shirun nan ne? Kodai jikin ne? Kodai ta mutu ne?

Haka yarik'a tufka da warwara shi kad'ai.

Su Fahad da suka shirya sai suka fita aikin daya kawosu bayan sun gaisa da Hajiya, tayi masu addua tace adawo lafiya.

Shirun sai yayi ma Khalil yawa, ga ita Hajiya babba tak'i bud'e d'akin ama san ko menene.

Maijiddah ce bata bud'e k'ofa ba sai wurin Azahar, tana fitowa da Khalil ya ganta sai cewa yayi "ke baki mutu ba ashe?" Ya fad'i hakan cike da damuwa.

Maijiddah tayi masa wani almirin kallo tace "Na mutu mana shiyasa ka ganni tsaye anan gabanka, Ooh ashe kai nan duk ka d'auka na mutu wato damuwarka ta k'are saboda tsabar tsana, to ban mutu ba inanan daram insha Allah saima ka rigani mutuwa"

"Ke matsalata dake baki da hankali" inji Khalil.

Maijiddah tace "to ai zama da mad'aukin kanwa shike kawo farin kai, haukata nada sila dakuma dalili, don haka kar wannan ya dameka don gidan mu d'aya"

Khalil yayi tsaki yace "Allah ya kyauta" ya wuce ya bata wuri

Shikam be tab'a ganin mutun irin Maijiddah ba.

***********

K'arfin hali irin na Maijiddah saboda batason kwanta ma ciwo yau har gidan su Mariya ta shiga, Maman su Mariya nanan, ta gaisheta sannan suka wuce d'akin su Mariya kamar yadda suka saba, ke Maijiddah da baki gani ki kyale sai cewa kikai "Wai yau wace rana na tarar da mamanku gida? Hala aikatau take irin nawa kokuma gadi irin na saurayinta? Don na lura bata zama"

Mariya ta b'ata rai, amma ita kam Maijiddah a banza ta d'auki wannan b'acin ran don iya gaskiyarta ta fad'a.

Mariya tace "to koma dai me take babu ruwanki tunda tabar karb'arma babanki kud'i kinzo kin raba" sai kuma suka maida abun wasa.

Suna nan zaune sunata fira, sai ga wata kyakkyawar budurwa ta kawo markad'e, Mariya ta karb'a tayi mata, data tafi sai Mariya tace ma Maijiddah "kinga wannan yarinyar da tazo nan?"

Maijiddah tace "gani sosai ma, y'ar kyakkyawa da ita meya sameta?"

Mariya ta tank'washe k'afa tace bari na baki labarin su, "gidan Yayarta yana nan bayan mu, mijin yayarta ke nemanta"

Maijiddah tace "ban fahimceki ba"

"To bari nayi miki dalla-dalla yadda zaki fahimta, ita wannan wadda ta kawo markad'e ita da yayarta y'an Kaduna ne, mijin yayar tata ne d'an nan kano, to k'anwar tana karatu nan cikin gari ne BUK, a hostel take zaune amma takan d'an zo masu ziyara, maganar da nake miki yanzu, Mijin yayar ke neman k'anwar, baiwar Allah yayar bata sani ba, kina ganinta haka kamar ta k'warai shad'aniya ce, to yanzu haka ma da kika ga ta kawo markad'e daga gani yayarta tayi tafiya, idan yayarta ta tafi anguwa sai yaje ya d'auko k'anwar daga makaranta ta maye gurbin matar suyita holewarsu".............

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now