*NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *26* 🌱
Ya gama kallonta sannan ya wuce, har ze shiga mota ta lek'o tace "Kayi kyau amma ka cire hular batayi maka kyau ba"
Yayi kamar be jita ba ya shige mota suka wuce, amma kuma bayan sun d'au hanya sai ya cire hular ya ajiye gefe guda gami da yin murmushi.
Da zasu dawo daga masallaci Kamal ya tsaya ya siyo masu ice cream da Burger, yaba Khalil nasa, tun a mota ya fara ci.
Lokacin da suka iso gida Maijiddah ta gama aikinta ita ma tayi wanka tayi kwalliya da kayanta wanda Hadiza ta bata, doguwar rigar atamfa ce wadda ake kira da A shape Gown, atamfar mai kalar ja da ruwan toka, tayi mata kyau sosai.
Su Khalil na shigowa suka isketa parlour, da farko basu ganeta ba ma har saida suka shigo tsakiyar parlourn, Kamal yace "Wooooow K'anwata kinyi kyau sosai, zo inyi mana hoto"
Da farko dai tana ta d'an nonnok'ewa sai taga shi sam babu abunda ya dame shi, hakan yasa ta saki jiki, yayi masu d'aukar hotunan nan da ake cema selfie masu yawa, hada dafa kafad'arta suna dariya, Khalil na tsaye daga gefe guda kamar ya mutu don takaici, Kamal ya bashi wayar yace ya d'aukesu, babu halin yace a'a, hakanan ya amshi wayar ya cigaba da d'aukarsu, bayan daya gama d'aukarsu Kamal yace yazo suyi tare, amma sam Khalil yace a'a be shirya ba, yana bashi wannan amsar ya wuce d'aki.
Kamal be kawo komai aransa ba saima mik'ama Maijiddah ledar Ice cream da Burger d'in daya siyo mata yayi, ta karb'a badon tasan ko meye ba kuma bata taba gani ba bata tab'a ci ba, kunsan bata shiru.
Tace "meye wannan d'in?"
"Wannan ice cream ne, wannan kuma burger kenan, kardai kice baki tab'a ci ba?" Ya tambaya.
Ta gyad'a masa kai.
"Amma da mamaki, Khalil nacin burger sosai, be tab'a siyo maku ba?" Ya sake tambaya a karo na biyu.
Maijiddah tace "tabd'i, aikodai ko yana ci k'ila a d'akinsa yake ci nidai ban tab'a gani ba" ta fad'i maganar fuskarta a yamutse kamar wadda tasha bauri.
Murmushi Kamal yayi sannan yace "kici kiji akwai dad'i"
Maijiddah ta bud'e robar ice cream taga abu shiba kumfa ba shiba k'ank'ara ba, tasa cokalin abun ta d'iba tasha, wani sanyi da dad'i taji ya gangaro tun daga mak'oshinta har zuwa kaf ilahirin jikinta, tana sha Kamal na binta da Ido yana dariyar yadda yaga tana murza baki.
"Bari kiga yanzu picx d'inmu zasu shiga social media, bari na fara sawa a WhatsApp" ya fad'i haka yana danna wayarsa.
Maijiddah ta dakata da cin burger ta rik'a kallonsa domin bata gane me yake cewa ba ma sam, da taga ba ita yake kallo ba bare ya tambayeta lafiya sai ta bud'e baki ta tambayesa,
"Wane irin yare kayi yanzu? Don wallahi ban gane komai acikin abunda ka fad'a ba, nadaiji kamar kayi hausa, sai kuma naji kace pis (picx) da social mida (social media) da wani ko wassap (Whatsapp)"
A wannan karo Kamal beyi dariya ba saidai yad'anyi murmushi sannan ya maida dubansa gareta.
"Picx da kikaji nace ina nufin 'pictures' ma'ana hoto, social media kuma yana nufin 'kafofin yad'a labarai kokuma yad'a zumunta na jama'a', shi kuma Whatsapp yana d'aya daga cikin wannan kafofin, yanzu dana d'ora hotunan mu abokai na zasu gani suyi magana kuma sannan ina iya kiran waya ina kuma iya yin video duk a wannan kafar, matso na nuna miki ki gani"
Maijiddah ta matsa kusa dashi tasa idanuwanta akan wayar, ta rik'a kallon abun al'ajabi, shiko ya cigaba da nuna mata yana mata bayani.Khalil har yaje ya cire manyan kayan dake jikinsa yasa guntaye ya dawo suna nan suna hidimar gabansu, basu ma lura da shigowarsa ba.
"To nuna min a wayata ingani" Maijiddah tace ma Kamal bayan daya gama nuna mata da wayarsa"
"Ina wayar take, wannan world sound studio d'in har waya ce" Khalil ya fad'i haka yana mai wata irin kafirar dariya.
Tare Kamal da Maijiddah suka d'ago kai domin basu ma san dawowarsa wurin ba.
Kamal yad'an tsawata masa cikin ruwan sanyi.
"Meyasa kake haka ne? Ka dena tononta da Allah"Sai ya maida dubansa ga Maijiddah daketa faman hararar Khalil yace "Irin wayarki batayi ki bari idan kinyi babbar waya zan nuna miki"
Maijiddah ta amsa da to.
**************
Khalil ya rage rashin ji sosai ba kad'an ba, domin a yanayin daya tsinci kansa yanzu ko fita bayason yi, yafison ya zauna yana gadin Maijiddah da yayansa Kamal, idan idansu biyu shima haka, idan sukayi bacci nanne ze samu ya rintsa. (Aiki ya sameka chief security of d year)
Fahad ya damu matuk'a da irin yadda Maijiddah keyi masa kwanannan, hakan yasa ya kira Khalil domin neman taimakonsa ya bincika masa meke faruwa, Khalil saidai yace masa to amma a zahirin gaskiya bawai ma yaji dad'in maganar da fahad d'in yayi masa bane, ma'ana 'koda yanada hanyar taimakon bazeyi ba'.
***********
"Kamal kasan Sulaiman?" Hajiya Uwa ta tambaya.
Kamal dake zaune gefe d'aya kan kujera yana danna waya, ya matso gaba kad'a gami da ajiye wayar yace "wane sulaiman Uwa?"
"Sulaiman dai yaron wajen Alhaji Sabe Custom"
"Okay yh nasan shi wanda ke zaune nan bayan mu ko? Nasan shi" ya fad'a cikin matsuwa.
"D'azu nake jin labari marar dad'i daga wurin Hajiya Laure wai matarsa ta kamasa da k'anwarta a d'akinta ta tara masu jama'a, yanzu haka ma ta kaishi k'ara kuma tanaso a raba auren, sam banji dad'in wannan labari ba, duniya dai kaga ana wasu irin abubuwa gasu nan dai, kamar kace k'arya ne amma ba dama tunda dagaske anyi" Hajiya Uwa ta k'arasa maganar tana jimamanin abun.
"Wa iyyazubillah, assha abu be dad'i ba kam, ina hankalin sulaiman ya tafi? Wace irin mummunar k'addara ce wannan? Allah ya k'ara tsare mana imanin mu"
Hajiya Uwa ta amsa da Amin.
Bayan sun gama firar su Sulaiman sai ta fara yi masa maganar aure, cewa ya kamata yazo yayi aure hakanan, tare da fad'a masa, yayansu da sukayi waya da ita jiya yace ayi masa tayin K'anwar matarsa idan tayi masa, tanada natsuwa, take a wurin Kamal yace a'a, shi shize zab'a ma kansa matar daze aura adai tayasa da addu'a.
**********
Maijiddah fa dagaske take domin kuwa tanata zuwa koyon d'inki da turanci, saboda iyawa ma yanzu ta hana Mariya ta rik'a yi mata magana da hausa, dukda cewa dai be yiyuwa amma suna k'ok'artawa kam.
Tsananin Hajiya ya dawo tun bayan tafiyar Alhaji, saidai ansamu canji sosai yanzu domin ko Khalil baya biye mata kuma yana hanawa wasu lokutan idan yana nan, Kamal ko shi dama ba'a magana don be baro komai game da halayyar mahaifinsa ba.
*************
Tsintsiya Maijiddah taga Kamal ya d'auko ya wuce da ita ta k'ofar d'akinta ze nufi nasa d'akin, da sauri ta dakatar dashi gami da tambayarsa abunda zeyi da tsintsiya, ya amsa mata da cewa shara zeyi yaga d'akin nasa ne yayi datti, sam tak'i bari yayi sharar nan ta karb'a tace ita zatayi, yace ta barshi ba damuwa ze share, Maijiddah fa tace inaaa a'a gaskiya, haka dai ya hak'ura ya bata tsintsiyar ya koma parlour ita kuma ta k'arasa d'akin nasa ta fara gyarawa.
Kamar an jefo Khalil, yazo ze shiga d'akinsa sai ya hango ikon Allah, a hankali ya rik'a tafiya har yakai k'ofar d'akin Kamal, ya kalli Maijiddah ya k'ara kallonta ya saki wani murmushin takaici sannan yace "to shi kuma wannan gyaran d'akin da kike auransa kike? Shi aka d'auko ma ke aiki? kilbibi ne koko na neman gindin zama ne? Saboda tunda nake dake a gidannan baki tab'a gyaramin d'aki ba sai sau d'aya da nayi ciwo"
"Da kayi hauka dai ta soshe-soshe" ta fad'a tana mik'ewa tsaye, sannan ta cigaba da cewa.
"Babu ko d'aya cikin abubuwan daka lissafa yallab'ai, don haka kana iya tafiya""Bazan tafi ba, wai tsaya ma don Allah na tambayeki, Son Kamal kike ne?................
