page 10

1.8K 86 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                 🌱 *10* 🌱

"Ni banga wani abu a ciki ba Uwa, wallahi gara ma ta tafi, ni dama idan ta tafi tayi zamanta karta dawo" cewar Khalil.

Kallonsa kawai Hajiya Uwa tayi batare da cewa komai ba, sai ta maida dubanta zuwa k'ofa, shiru bata zo ba, ta sake k'walla mata wani kiran.

Maijiddah ta shigo tace "gani Hajiya"

"Hajiya Uwa ta wurga mata wata arniyar harara sannan tace "ke gaki isassa ko? Baki iya fad'aman zakije gida shine sai kika je kika fad'a ma Alhaji, to tsakanin nida Alhaji waye ya kawoki gidannan?"

"Ke kika ce inzo amma nina kawo kaina tun daga Rimin Gado har cikin gidannan babu wanda ya kawo ni" inji Maijiddah.

Hajiya Uwa taja tsaki tace "ji wani dak'ik'anci, dama tambayarki wanda ya kawoki nayi? Wanda ya d'auke ki aiki nake nufi"

"Ke kika ce a kawo miki ni amma bansan waye ya d'aukeni aiki acikin ku ba, sannan yanzu fisabilillah Hajiya don na nema izini wurin Baba kan zanje gida laifi ne? Na d'auka dake dashi duk d'ayane, sannan dani dake da duk wani wanda ke cikin gidannan ai k'ark'ashinsa muke saboda shine Maigida".

Ran Hajiya Uwa ya k'ara b'aci tace "a'a kima ce matsayin mu d'aya dake acikin gidannan kinji uwata?  don naga take-taken ki nema kike ki fara gogayya dani acikin gidannan kamar wata kishiyata"

Maijiddah tace "ta yaya zance matsayinmu d'aya dake a gidannan, ai bema yiyuwa, Hajiya bari na tafi had'a kayana nake yi don gobe da wuri nakeso na tafi kuma inaso na shiga gidan su Mariya nayi mata sallama"

Ta mik'e zata wuce Hajiya ta daka mata tsawa,
"Gidan ubanwa zaki nace ki tashi ne? Kuma babu wani gidan su Mariya da zaki je"

Murmushi Maijiddah tayi sannan tace "Hajiya ina ganin girmanki, saboda haka don girman Allah kada kisa ya zube a idona, domin aduk lokacin da kikace uban wa ko uwar wa taushe zuciyata kawai nake, amma da za'a bud'e maki zuciyar kiga abunda ke ciki da baki k'ara zagi na, banyi miki komai ba don haka banaso ki rik'a yiman komai, domin nima ba komai ne na dace na samu daga gareku ba, zuwa gida ne na tambayi Baba, shi kuma Baba ya sanar miki to meye aciki? Bekai matsayin daze yanke hukunci bane shida gidansa kuma ikonsa?, gidan su Mariya kamar naje na gama jikina ne kuma ra'ayi na ne, a k'arshe Rimin gado ne shima sai naje kuma saina dawo" bata jira mai Hajiya Uwa da Khalil zasu ce ba tayi wucewarta"

"Eyyyyyeeeeee, lallai kam samun wuri, to zanga yadda za'ai wannan y'ar iskar yarinyar ta dawo cikin gidannan"

Duk wannan abun da ake Khalil na gefe bece k'ala ba don yasan shida banza duk d'aya ne a wurin Maijiddah, saima dad'i dayaji don koba komai a ganinsa zaman Maijiddah a gidan yazo k'arshe.

***************

Da Maijiddah ta gama gyara kayanta ta sab'i hijabinta ta fita sai gidan su Mariya.

Tana zuwa k'ofar gidan taga Yawale, sai ta masa wani irin kallo tace "yada zuwa kuma nan Baba?"

A daburbuce yace "a'a babu komai Maijiddah daman rigar d'aya daga cikin yaran gidan ne nagani can tsallake dazan wuce shine nad'an mik'o masu"
K'anin Mariya ne tsaye a k'ofar yana karb'ar rigar, yace da Maijiddah "ina yini"

Bata ansa masa ba sai ta juya tace da Yawale "ashe duk kasan kayan yaran gidannan Baba?"
Suka kalli juna shidai be sake cewa k'ala ba ita ma haka, sai daga bisani tace "ni na shiga ciki saina dawo", ya amsa da "to" shima ya wuce.

A caan bayan gida Maijiddah ta iske Mariya jikin wata bishiyar mangwaronsu dake gidan, Mariya na ganinta ta fara washare baki tana "ga d'alibata ga d'alibata, itako ta turnik'e fuska.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now