NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *8* 🌱
Tsaki kawai yaja ya juya ya cigaba da kallo.
Ta gama bad'e sa da hayak'i sannan ta fita daga parlourn.
Khalili acikin ransa ji yake dama da yadda zeyi ya kori wannan yarinyar daya yi don ta zame masa k'arfen k'afa, gata bata da kunya ko kad'an, bata tsoronsa bata girmama sa, a cewarsa.
Yana nan zaune wani abokinsa ya shigo, suka wani kashe irin gaisuwarsu ta y'an duniya, bayan ya zauna sai yace,
"Mah guy wai yana ganka cikin wannan hayakin kamar wanda za'a turara?
"Mtswww kaima dai ka gani Zaks, wallahi wata jahilar y'ar aiki aka kawo mana na tsaneta, ta mugun rainani, u need 2 c her zaks i so much hate her wt passion"
Zaks yace "den wat re u waiting 4 guy? Get rid of her kick her out ko gidan ubanta ne? or u gv her wat she deserve"
Khalil ya yamutse fuska sannan yace "wat do u mean?"
"I mean wat u think guy, ka bata abunda ka saba bama sauran, haba karka bani kunya mana har akwai macen da ta isa ta ja da d'an Hajiya, kira mata ruwa kawai zata tafi don kanta"
Khalil yace "kaman fa ka shiga raina, amma fa yarinyar nan tasha banban da sauran yammatan daka sani, aljanar kanta ce yasin, amma............."
Ya bud'e baki ze cigaba da magana kenan hakimar (Maijiddah) ta shigo, ko kallonsu batayi ba ta nema kujera ta zauna abunta tana kallon abunda suke kallo, Zaks da Khalil suka k'urama juna ido tsabar mamaki, sai Zaks yayi ma Khalil nuni da hannu alamar wacece? Khalil ya mayar masa da 👩🏻👈🏻👌🏻, Zaks yad'an zaro ido ya gyad'a kai ma'ana ya fahimta.
"Ke baki ganin nayi bak'o zaki wani zo ki zauna mana?" Cewar Khalil.
Wani irin juyowa Maijiddah tayi da kanta tace "tambayarka amsarka, kuma koda na ganku aini ba wurinku nazo ba kallo nazo yi, a iya sani na nan ba d'akinka bane, da d'akinka na shigo sai ka tambayi dalili"
Ta kalli abokinsa tace "sannu abokinsa anzo lafiya?"
Ai bema samu amsa ta ba sai binta daya rik'ayi da ido cike da mamaki.
Haka sukayi zaune kamar kurame sai kallon kallo da ake, itadai ta maida hankalinta da dubanta gabaki d'aya kan TV kunsan mutanen mu akwai son kallo (ba saban ba).
Zaks dai ya gaji da ganin wannan sarautar Allah ya mik'e yace da Khalil "Zan wuce".
Khalil ya fito raka sa.
"Guy ai da gani babu tambaya wannan yarinyar tayi kama da labarin daka bani, kuttt kalli fa yadda take isa kamar gidan ubanta wai Hajiya bata nan ne da tabar ta take wannan abubuwan koko batasan tanayi ba?"
Khalil yace "tasan wasu, batasan wasu ba, wallahi Zaks ranar nan ma kashe ni taso tayi, da saidai kuji labarin mutuwa ta, ai kaidai abun ba kyau kaji"
"Kashe ka kuma? Nifa abun yana bani mamaki Allah, dama ana samun mutane irin haka? Bt seriously Guy u need 2 end ds ka bata sugar kawai, gata ma tubarkallah kamar ba y'ar aiki ba, hukunta ta kawai kafin ta wuce Alhajina"
Khalil yayi y'ar iskar dariya yace "trust me on dat, baka da matsala zakaji yadda movie d'in ya k'are"
"Dats mah Guyyyyyyyyy, nizan fasa sai ka fito ko? don akwai kaya"
Khalil ya amsa da "ok bye saina fito d'in.
****************
Alhaji Abdullahi ya iso lafiya, Kyakkyawan dattijo ne mai arzik'i, daga ganinsa kasan yasamu hutu kud'i sun zauna.
![](https://img.wattpad.com/cover/168174266-288-k797868.jpg)