NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *27* 🌱
"Ji wata tambaya to sai ink'i sonsa hakanan? ina sonsa sosai da sosai mana, kanada magana ne?" Maijiddah ta amsa masa.
Khalil yace "uhmm naga alama, a soye lafiya, idan kin gama ga d'akina can aje a gyara min nima" be jira me zata ce ba ya wuce yana dariya don yasan bak'ar magana zata mayar masa.
Ita kuma ta hararesa gami da sakin guntun tsaki, ta cigaba da shara.
******************
"Wallahi Maijiddah kina k'ok'ari sosai, inajin dad'in koya miki abubuwa saboda kina saurin d'auka, yanzu d'inkinnan idan ba an fad'a ba babu me cewa y'ar koyo tayi, sai kawai ki dage ki siya keken d'inki" inji Mariya.
Maijiddah dake kan keken d'inkin Mariya tayi murmushi tace "to ai nid'in y'ar baiwa ce, amma fa nagode sosai mariya, baki da bak'inciki ko hassada, inajin dad'in abubuwan da kike koyamin domin koda kud'ina ba lallai bane asamu wanda ze rik'a koyamin irin haka ba, Allah ya biyaki, inada tinkiya mai ciki idan ta haihu zan baki d'a guda d'aya"
Mariya ta kwashe da dariya, suka cigaba da abunda suke, sunayi suna fira kamar kullun.
*****
Maijiddah na dawo wa gida a gate ta iske Hajiya Uwa nata fad'a.
"Inbanda iskanci, tasan tanada aiki sai kawai tasa k'afa ta fita harkar gabanta, ko gidan ubanwa ma take zuwa oho, nifa na fara gajiya da iskancin yarinyar nan" Yawale dai yayi shiru, yana gudun ya tanka tashi tafi zafi.
Tana ganin Maijiddah, ta cigaba da zazzaga mata masifa, Albarkacin Kamal Hajiya Uwa keci yanzu, shi kad'ai ke hana Maijiddah maida ma Uwa magana don koba komai yana ganin girman Mahaifinta.
Saidai Maijiddah tayi shiru, bata bada hak'uri ba kuma batace komai ba, ta gama balbala masifar ta shige, Maijiddah ta bita a baya ta shiga ciki itama.
Yau sam Kamal bega walwala a tare da Maijiddah ba, sai duk yaji babu dad'i don be saba ganinta acikin wannan yanayin ba, shiko Khalil daya ga shirun nata yayi yawa, sai ya fara tinanin ko zazzab'i take don ya fahimci ciwo kad'ai ke ladabtar da ita, beyi k'asa a guiwa ba wurin tambayarta.
"Jiddah baki lafiya ne?" Khalil ya tambaya.
"Mukayi dakai?" Ta maido masa wata tambayar cikin harara.
Yace "Allah ya baki hak'uri almasifatu".
Kamal dake gefe dariya ta kufce masa, drama Khalil da Jiddah na bashi dariya sosai, besan ya akai suka raina juna haka ba.
****
Tana d'akinta zaune bisa sallaya tana karatun Qur'ani murya k'asa-k'asa, sai Kamal yayi sallama ya shigo da leda a hannunsa, ta kallesa tayi murmushi sai ta rufe Qur'anin ta juyo.
"Sannu da zuwa Yaya" ta fad'a tana kallonsa.
"Wow Yaya? Godiya nake da wannan suna, dagaske dai baki iya fad'in sunana daman nace ai, kikace ba haka bane, fad'aman meye sirrin sunana arayuwarki kodai kodai sunan sirikina ne? 😊"
"Kai don Allah, aa wallahi babu komai, kawai dai ina ganin girmanka ne bana iya kiran sunanka kai tsaye gaskiya" ta fad'a kanta a k'asa tana murmushi.
Yace "to nagode, ga wannan duba ki gani" ya mik'a mata leda.
Tana dubawa ta zaro ido tace "laaaa kamar waya nagani?"
"Fidda kamar, wayace k'arama na siyo miki saboda kema ki shigo yayi" Kamal ya fad'a