page 5

1.8K 94 4
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                 🌱 *5* 🌱

Caaan cikin bacci Khalil yaji yana shak'ar wani numfashi mai mugun azaba, ba shiri ya bud'e ido yana wani irin tari mai ban tsoro, hayaki ya gani ya turnik'e d'akinsa, idanuwan nasa ma dak'ar yake bud'esu saboda yaji, yarik'a laluben hanyar fita amma ga mamakinsa yana zuwa dadai k'ofa sai yajita a rufe, shikam yasan a bud'e yabar k'ofarsa, wata iriyar zufa yarik'a had'awa ga azaba jikinsa kamar anai masa wankan bark'ono, ya jijjiga k'ofar amma inaaa, makullin k'ofar ma daya laluba be jisa ba.

Maijiddah ta lek'o domin tabbatar da tarkonta yayi kamu, aiko taga hayaki na fitowa ta k'asan k'ofar kamar band'akin sabuwar maijego, wata dariyar mugunta tayi marar k'ara sannan ta sad'ad'o a hankali taje ta k'asan k'ofar ta tura makullin tayi sauri ta koma d'akinta ta zauna tana sauraron sakamako.

A b'angaren Khalil kuwa zamu iya cewa yayi lilis, ya rik'a jijjiga k'ofa amma babu wanda yajisa, sai wata dabara ta fad'o masa da sauri ya nufi saitin window, ya samu dak'yar ya bud'e gashi windows d'in sunada k'arafa da net bare ya dira tanan, saidai ya rik'a k'wala ma Yawale k'ira.

"Yawale! Yawale! Yawale, wai baka jina ne? Da Allah kazo ka taimakeni gobara a d'akina zan mutu"

Haka yayita fad'i har Allah ya taimakesa Yawale ya shigo cikin gate don dama baya cikin gidan yad'an lek'a waje wurin wani abokinsa maigadin mak'otansu, aiko yana shigowa ya hango window ga kuma Khalil nata tsuwa kamar rub'ab'b'iyar mota.

Da sauri Yawale ya k'arasa jikin window d'in yana fad'in "Khalil lafiya?" Ai inaaa sai Khalil ya sulale k'asa ba lumfashi, ba shiri Yawale ya shiga cikin gida yanata k'wallama Hajiya Uwa kira, itama ta fito da sauri don daga jin kiran bana lafiya bane.

"Hajiya Khalil" yawale ya fad'i haka.

Hajiya tace "Khalil kuma, meya same shi?"

Ai bai samu bata amsa ba yayi hanyar d'akinsa tana binsa a baya, suna zuwa suka ga wannan ikon Allah, ga k'ofa a rufe, suka jijjiga k'ofa amma tak'i bud'ewa, Hajiya Uwa fad'i take "na shiga ukku d'ana ze mutu Yawale b'alle k'ofar kawai idan zaka iya"

Hayaniyar da Maijiddah taji ya sata fitowa da sauri irin kamar batasan meke faruwa ba, tana isowa wurinsu cikin tashin hankali da damuwa tace "Anbani Hajiya mezan gani haka? Meke faruwa?"

Hajiya Uwa tace "Wallahi bansani ba Maijiddah kindai gani, Allah ka tsareman yaron nan kome kuma ya faru oho?"

Hajiya ta fara tari sama-sama itama, don hayak'in beda dad'in shak'a ba sauk'i acikinsa, nandanan suka dod'e hanci hada ita shak'iyyar wato Maijiddah.

Dak'yar Yawale ya b'alle k'ofar nan, zasu shiga yace su dakata, shi kad'ai ya shiga ya d'auko Khalil a sume (Dambanzan can yaci ataaaa), sukabi ko ina aka bubbud'e domin iska ta samu shigowa.

Hajiya Uwa tayo kan d'an nata tana jijjigasa tana kuka, shi kuma Yawale ya koma cikin d'akin domin ganin ta ina wannan wutar ta kama kuma wane irin hayaki ne wannan mai yajin gaske.

Shidai kam a iya dube-duben sa babu wata wuta daya gani, ya fita gami da sanar da Hajiya shifa bega wuta ba.

Hajiya tace ya d'auko Khalil idan ze iya su wuce asibiti, Yawale ya tsaya gardama kan cewa Khalil fa suma yai a d'ebo ruwa asa masa ze farfad'o, aifa tahau fad'a,

"Ana maganar autana ya suma yana cikin wannan yanayin kana zancen ruwa, dallah mallam kamoshi mu wuce asibiti, ya Allah ka yayeman wannan damuwa, kome ya faru oho" ta k'arasa maganar tana zubar da hawaye sannan ta k'ara da cewa,

"Ke kuma Maijiddah ki zauna gida ki gyara d'akin da duk inda yakeda buk'atar gyara"

"To Hajiya amma an kira isha'i dadai kun tsaya kunyi tukunna" inji Maijiddah.

Tsaki kawai Hajiya Uwa taja suka fice.

Tanajin fitar motarsu daga gate aiko ta fashe da wata iriyar kafirar dariya, sai bayan da tayi mai isarta sannan ta dakata tace "to Allah dai yasa kar ya mutu"

Barin Maijiddah a gida yabata damar gyara duk wata b'araka da tayi, tare da wanke kanta daga cikin duk wani zargi daze iya biyo baya.

Ta shiga d'akin ta kauda Burner d'innan ta mayar da ita inda ake ajewa tare da goggogeta ciki da bai, ta karkad'e zanin gadon nan tayi shinfid'a, ta bubbud'e windows ta k'ure fanka, hancinta a rufe take wannan aikin, wurin shara ko saida ta sharo kwalaben kayan maye masu tarin yawa dadai sauran tarkace da suka shafi shaye-shaye, taga makullin k'ofar data turo ta k'asa, ta d'aukesa ta maida jikin k'ofa ta ciki, tana shara tana Allah wadai da halinsa, saida ta gyara d'akin nan tsaf sannan ta fita takuma bar k'ofa bud'e don asamu wadatattar iskar da zata kori wannan k'aurin marar dad'i, tayi wucewarta d'aki ta fara sallah. (🤣 damarki ce Jiddah).

*******************

Caaan wuraren k'arfe goma suka dawo da almirin duk yayi laushi, da sauri Maijiddah ta tarbesu parlour tace "ya jikin nasa Hajiya?"

Hajiya ta amsa "da sauki Alhmdlh"

Ya wuce hanyar d'akinsa, Hajiya tabi bayansa, Yawale zeyi ma Maijiddah magana itama tabar wurin ta tafi d'akinta, don batason yima babanta magana yanzu, y'arb'oye ma take dashi.

Hajiya Uwa saida ta rakasa har d'aki, Khalil ya rik'a kallon d'akin nan lungu da sak'o yanaso ya gano wai meye ya faru ne? (D'an banza ido yayi luhu-luhu kamar banufe 😎 nufawa kunsan ku bayinmu ne don haka bana tsammanin zaku iya maida martani ga iyayen gidanku 😁) ga mamakinsa sai yaga key a jikin k'ofa, sai abubuwan suka fara yi masa kamar irin yayi mafarkinnan ya tashi, "shin kodai aljanu ne" tambayar da yayi kenan a zuci.

Hajiya Uwa ta jawo Khalil ta zaunar dashi bakin gado kamar zatace wani abu mai dad'i sai ji yayi tace,

"Auta ya kamata kayima kanka fad'a, wannan shaye-shayen bashi da wani amfani, shiru dai kawai nayi amma ni nasan tatsuniyar gizo bata wuce k'oki, wani abun ka kunna ya nemi halaka ka, ka duba kaga fa cikin awanni k'alilan yadda ka sauya kamanni, ka taimakeni don girman Allah ba don niba ka dena kaji Auta"

Mamaki ya kama Khalili, fuskarsa ta bayyana hakan, kamar ze kuka yace wallahi Uwa ni ban sha komai ba, ban kuma kunna komai ba, wallahi inaga akwai aljanu d'akinnan don ni ganin abubuwan nake kamar nayi hauka"

"Babu wasu aljanu kaine aljanin kanka, kuma hauka da kake ganin kamarta idan baka dena abunda kake ba watarana haukar zakayi tuburan kuma muna gani babu yadda zamuyi" tana kaiwa nan ta mik'e tace,
"Allah ya bamu alkhairi Allah kuma ya k'ara kiyayewa" ta wuce d'akinta.

Ya tashi yaje yayi wanka ya had'a sallah magrib da isha'i ya rafke lokaci guda.

Mamaki kam ya bak'unci zuciyar Khalil, bacci saidai b'aro amma idonsa kyam bai runtsa ba gashi har lokacin idonsa na masa zafi.

**************

Washe gari yana fitowa daga d'aki yaci karo da Maijiddah tanata faman masa murmushin munafurci, ya harareta yace "ke kuma meye kiketa wani murmushi kamar tab'ab'b'a?"

Bud'ar bakinta sai cewa tayi "ai itace, au ashe fa kai baka sani ba uhmm, Allah sarki aida ka bak'unci lahira jiya da ka tabbatar da tsantsar rashin hankalina, to Allah yasoka kanada sauran kwana, koda yake daman banyi don ka mutu ba, nayi ne don ka wahala, don girman Allah gobema ka k'ara kwatanta mari na kaji Autan Hajiya"

Khalil ya yamutse fuska yace "wat? Wat do u mean? So it was ol u?"

"Tabd'i jam ai kaji inda ake yinta, kaima u, saika rik'a min yare to duk abunda kace kaima haka, idan ma zagina kayi kai kad'ai kaji don ni Hauwa'u bansan kanayi ba wai akace harara a duhu"

Ta juya zata wuce, da k'arfi yace "ke Jiddah" gami da fizgota baya, tayi taga-taga kamar zata fad'i tayi sauri ta dafe bango, maimakon taji tsoron yanayin data gansa sai kawai ta fashe da dariya hada d'an rufe baki sannan tace me yaci *Mai* d'in? Sunana Maijiddah ba *Jiddah* ba malam, fad'i ina jinka ko wani marin ne?"

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now