NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *6* 🌱
Huci kawai yake ransa yakai mak'ura a b'aci.
Maijiddah tace "hmmm nifa daka ganni turmi guda ce ba k'yalle ba kuma kowa yaci tuwo dani miya yasha, wannan kad'an kagani acikin irin hukuncin dazan rik'a d'auka yayinda kace zaka rik'a shiga gona ta, kabar ganina y'ar k'auye kuma k'arama a ganinku, kamar bansan komai ba *"duk mace, mace ce"* kota birni kota k'auye abunda yayi farida shi yayi fadila.
(👌🏻k'urunk'ussss, tabbas duk mace mace ce saidai wadda tayo rakiya)Khalil kam baki ya rufe kamar wanda akai ma wankan super glue, saidai ya kafe ta da ido kamar makahon daya warke, itakam ganin baya da abun cewa sai kawai ta k'ara ma bujenta iska.
Khalil be zame ko ina ba sai wurin mahaifiyarsa, yana zuwa ba gaisuwa ba komai ya fara cewa,
"Wallahi Uwa nace miki banyi komai ba jiya a d'akin nan, gashi nan yanzu gaskiya tayi halinta"
Hajiya tace "ban fahimce ka ba Auta"
"Eh mana ashe duk abunda ya faru wannan kidahumar, dak'ik'iyar jahilar bak'auyarce tasa, Jiddah ita ta zuba wani abu a d'akina Uwa, wallahi kuwa yanzu ta fad'aman"
"Wace Jiddah kuma? Wai Maijiddah?"
Khalil yayi sauri ya gyad'a kai yace "eh ita mana ni sunanta ma tsawo yake min, banson yarinyar ni dama tun ranar da na fara ganinta, wallahi idan baku koreta ba watarana saita kashe mu gaba d'aya don bata da hankali"
Suna haka sai ko gata ta shigo da sallamarta, ta gaishe da Hajiya.
Hajiya uwa ta amsa sannan tace "Maijiddah nakejin wata magana a bakin Khalil amma ban fahimta ba shin ko zaki iya yiman bayani sosai yadda zan gane?"
"Yi hak'uri Hajiya nima ban fahimce ki ba wlh, bayanin me?"
Khalil da sauri kamar ze mareta ya matso kusa yana nunata da yatsa yace "U bloody liar, hey re u kidding me? wat re u trying 2say, u no nothing? Gushhh y cnt i jst......damn it" Ya wani dunk'ule hannunsa ya yarfa k'asa gami da cije baki.
Hajiya Uwa ta rik'a kallonsu d'aya bayan d'aya, ta bud'e baki zatayi magana kenan Maijiddah ta tarbi lumfashinta....
"Hajiya nasan tunda nazo gidannan Khalil baya sona, ba kuma zan tilasta masa ya soni ba domin a so ba'a dole, haka zalika nima kamar yadda baya sona nima ko bana sonsa kiyi hakuri nace banason d'anki a gabanki kamawa tayi domin inaso kiyiman katangar k'arfe dashi, k'iyayyar da nake masa batakai girman da har zan iya yunk'urin ganin k'arshen lumfashinsa ba" ta juya ta kalli Khalil tace dashi,
"Baka sona na fahimci wannan, gidanku nazo nasan wannan, k'ark'ashinku nake na yadda da wannan, amma banyadda ka wulak'antani ba domin niba wulak'antacciya bace, idan kana neman wadda zata jure wulak'ancinka ne to ba Maijiddah bace saidai wata, sannan idan kanason zaman lafiya to ka fita harkata ka kuma barni nayi abunda ya kawoni, domin niba misayar k'iyayya ta kawoni nan ba aiki nazo yi, a k'arshe" ta kalli Hajiya "inaso ki sani bani da masaniya akan abunda kike neman cikakken bayaninsa, hukunci ya rage naku, kubarni na cigaba da aiki gidannan kokuma ku koreni na koma k'auyen mu, ni a wurina duk d'aya ne" (duk d'aya wai mamaci ya karye 🤷🏻♀, ina yinki Jiddah👍🏻).
Shiru Hajiya tayi tana mamakin baki da rashin tsoro irin na wannan yarinyar.
Shiko Khalil tsoro ma ta fara bashi, domin yanajin labarin kaidin mace amma be tab'a cin karo da koda k'waya d'aya ba sai yau, amma a zuciyarsa sai yace "bakisan dawa kike ba, indai wannan ne kinzo gidan lallai zan miki illa bazaki tab'a mantawa dani ba, ni dangarama ne mai kwashe kowa da kowa, ba'amin wargi"