🌱 *34* 🌱
Tasha dariyarta mai isarta sannan ta natsu.
Tanajin tafiyar mutun alamun za'a shigo d'akinta tayi sauri ta k'udundune wuri guda, Kamal ya shigo cikin sallamarsa, ganinta da yayi a yanayin da yayi kama dana marar lafiya yasa yaji gabansa ya fad'i rass.
K'asa-k'asa Maijiddah ta amsa sallamarsa domin tasan tatsuniyar bata wuce gizo da k'ok'i, abincine bata yi ba kuma bazata yi komai ba a gidannan yau, batayi niya ba, tasan yazo ne yace mata a sama ma Hajiya abunda zata ci, mafarin tayi wannan kalmashewar kenan.
"Ya Ilahi, Maijiddah lafiya, badai kema baki lafiya ba?" Ya tambaya cike da kulawa.
Maijiddah ta nak'ushe murya tace "wallahi bana d'an jin dad'i ne cikina kemin ciwo"
"Garin yaya? Kinci wani abu ne? Kuma shine baki kirani ba? Uwa ma yanzu bada jimawa ba muka dawo da ita daga asibiti, tashi muje na kaiki asibiti" inji Kamal.
Maijiddah ta nannad'e fuska tana dariyar mugunta tace "a'a basai naje asibiti ba da sauk'i nasha magani daman nakanyi haka"
Kamal sai ransa ya basa ko MP ne, saidai kawai yace da ita "ok, sannu Allah ya k'ara sauk'i, bari na fita na siyo abinci to, sorry, sannu kinji".
Ya fita cikin hanzari, Maijiddah ta k'ara fashewa da dariya hada rik'e ciki dan mugunta.
Data tabbatar yabar gidan sai ta fito ta shiga d'akin Hajiya Uwa, ta ganta kwance duk tayi yaushi tanata bacci, a cikin ranta tace " kalleta kamar ta k'warai, ace shi mutun inbanda Masifa da bak'in hali babu abunda ya iya, aiko kin had'u da daidai ke" wani d'an iskan murmushi ya bayyana a fuskarta bayan data gama maganar zuci.
Ta juyo zata koma d'akinta kenan saiga Khalil ya shigo, habaaa aisai ta duk'e ta dafe ciki tana "hmm wai Allah na"
Shi kuma salman khan d'in cikin hanzari ya k'araso inda take ze dafata tayi sauri ta dakatar dashi da hannu tace "karka tab'ani"
"Ya zakice kar na tab'aki bayan gashi naga baki iya tafiya? Taso muje na kaiki asibiti" ya sake kai hannu a karo na biyu"
Ta kauce, ta wani tashi a dudduk'e har takai d'akinta shiko yana binta a baya cike da tausayawa.
Suka shiga d'aki yace shifa wallahi saita shirya sun wuce asibiti, Maijiddah sai tahau raba ido, taga dai dagaske yake sai tace "ai na warke"
"Banyadda ba Allah, malama ki tashi mu tafi asibiti ko na sab'e ki a kafad'a kinji ma na fad'a miki"
Sam babu fa wasa a cikin lamarin Khalil, sai Maijiddah ta masa wayo tace "to jeka daga waje na canza kaya" ya amsa da to.
Yana fita ta maida k'ofa ta rufe hada sa makulli, yayita bubbugawa tak'i bud'ewa, tasan halinsa sarai ba kunya ce ta ishe sa ba yana iya sungumarta yakai mota.
Ya gaji da k'wank'wasawar ya wuce d'akinsa don bema san Hajiya Uwa batajin dad'i ba.
Haka yayita zarya don ganin ko Maijiddah ta bud'e k'ofa amma ina, idan yaje ya k'wank'wasa tak'i bud'ewa sai yace "to yiman magana naji idan kinada sauran rai" ita kuma sai tace "da raina mutuwa ba yanzu ba tukun insha Allah" (🤣🤣🤣).
Har Kamal ya dawo Hajiya na bacci, hakan yasa ya d'auko ma Maijiddah ledar abincinta ya wuce mata dashi d'akinta, yana zuwa yaji k'ofa rufe, ya k'wank'wasa tak'i bud'ewa sai zuwa can yaji tace "kaga Khalil don Allah ka rabu dani ka ishe ni wallahi, nace maka naji sauk'i haba don Allah"
"Ba Khalil bane Kamal ne" ya fad'a atak'aice.
Tanajin muryar Kamal tayi sauri ta tashi taje ta bud'e, tana wani mammatse fuska, shiko sai cewa yake"sannu ya cikin da sauk'i ko?" Saidai ta gyad'a kai.
