21

1.3K 76 7
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Wannan shafin na sadaukarwa dukkan makaranta littafinnan, Allah yabar k'auna, kusa aranku y'ar mutan machika na yinku iya wuya🤝🏼*

*Ina marubutana suke? SAMEENA ALIYOU (My Commander), AYSHA A.R MACHIKA (Aunty Aysha),  SAFIYA BALA (Tawan) da AESHAB, ina maku fatan alkhairi kuma Allah yabar zumunci, i heart u guyx so vry mch.*

                🌱 *21* 🌱

Murmushi Maijiddah tayi gami da sakin wani d'an guntun tsaki sannan tace "kai amma fa ke da abun dariya kike, wato kina d'aya daga cikin mahaukatan makaranta littafannan, masu ganin labarin cikin littafi a zahiri, ko kuma nace masu kallon abu a film su rik'a ganin kamar ze iya faruwa da gaske, da Allah kinga mu canza fira don da alama kinyi hauka tad'an guntun lokaci"

"Haka zakiyi tinani, irin wad'annan abubuwan mamakin da al'ajabi a fina-finai da littafai kawai muke tinanin ana samunsu, amma a zahirin gaskiya suna faruwa, faruwar da suke yi ma ne yasa marubuta har suke tubutu akansu" inji Mariya.

Aisai Maijiddah ta gyara zama itama cike da mamaki tace "mijin yaya fa ke neman k'anwar matarsa?"

"K'warai kuwa fad'i ki k'ara, nauyin abun yasa har yanzu kowa ya kasa tofa ma yayar abunda ke faruwa, kuma kowa na tinanin idan ya fad'a cikin biyu za'ai d'aya kodai tak'i yadda tace sharri ne kokuma ta yarda, shikenan an raba aure kuma"

Maijiddah tace "kan uba, to dama meye amfanin irin wannan auren? Tirr da hali irin na wad'annan la'anannun Allahn, ace mijin yayata uwa d'aya uba d'aya na rik'a tarayya dashi, haba don girman Allah wannan wace irin rayuwa ce fisabilillahi? To idan ya gaji da yayar ai gara ya saketa su kuma iyayen idan sakarkaru ne irinsu  sai su bashi k'anwar tunda ita yakeso"

Mariya tace "a'a haka kukayi dashi? Ce miki yayi ita yakeso? Kawai tsabar biyewa zuciya ne da hud'ubar shed'an, don ina tabbatar miki yanzu dai ace ya saki yayar ya auri k'anwar baze yi ba, ai kedai kawai duniyar nan k'unshe take da abubuwa da dama, wanda dai ka gani shi kasani, amma da zakiji wasu abubuwan sai k'wak'walwarki ta dena aiki zuwa wani d'an lokaci, to sufa a nasu wawancin gani suke kamar mutane basu sani ba, masu aikin gidan su suka fara b'isa maganar, shi a ganinsa na amanarsa ne ma'aikatan gidan, yana toshe masu baki da kud'i besan cewa shi laifi idan kana yinsa inhar baka dena ba, to lokaci guda idan Allah ya tashi ze toni asirinka ne kowa ya gani"

"Ya Allah ya tona asirinsu matsiyata kawai,  su dikansu sunada laifi amma ba kamar k'anwar, tsabar cin amana ace kifin dake iyo a rafin yayarki shine zaki kamo domin yayi iyo anaki rafin? Duniya ina zaki damu?" Maijiddah ta k'arasa maganar kamar tayita kifa ma Mariya mari don takaici.

Yaudai basuyi wani karatun komai ba, firar duniya ce zallah suka yita yi, har ta tashi tafiya.

Da suka fito daga gida Maijiddah tace Mariya ta rakata chemist ta had'o maganin zazzab'i daman ta fito da wasu y'an kud'i, Mariya tace to, suka karya corner suka tafi suna fira.

****************

Tana shigowa gate taga Khalil zaune bisa kujera yanata murza yatsu, yace "daga ina kike? Anata nemanki wa kika cema zaki fita?"

Kallo d'aya tayi masa tak tayi shigewarta cikin gida domin baze ji dad'in amsar da zata fito daga bakinta ba dukda cewa ya saba.

Da sauri ya biyo ta ya fizgo ta baya yace "ba magana nake miki ba"

Maijiddah taja tunga ta rik'a kallonsa sama da k'asa sannan tace "malam Khalil Autan Hajiya Uwa, idan kaga kayi magana na share ka ban kula ka ba don girman Allah ka rik'a k'yaleni domin shirun komin zafinsa yafi sanyi akan amsar dazan baka, sau nawa zan fad'a maka babu me iko dani acikin gidan nan eh? Kuma ma ace duk cikar gidan nan da batsewarsa arasa wanda ze rik'a yiman irin wannan tambayoyin sai kai, mezanyi maka idan na zauna? Sannan me na rageka dashi idan na tafi?, kaga don Allah ka shafa min lafiya, ka fita daga harkata, to ko aurena kake ai bazaka rik'amin wannan abun ba bare kuma babu goro babu dabino bare kud'i"

"Inada ikon da zansan inda kike zuwa, saboda k'ark'ashin mu kike idan wani abu ya sameki mu za'a tuhuma" cewar Khalil.

Maijiddah ta linke hannuwa tace "haba? Har yaushe ka fara jin tsoron tuhumar ka akan wani laifi? Daga bakin wani maganar nan ya kamata ta fito ba daga bakin Khalil Abdullahi ba, kabari wanda basu da abun fad'a suyi magana amma bakai ba, an fad'a maka kowa irin ka ne? Don na fita waje shine me? Bashine yake nufin naje yawon iskanci ba...."

Tana aje kalmar taji saukar mari bayan daya mik'e yayo kanta, ya karkad'a yatsu sannan ya nunata da d'an yatsa d'aya yace "ki iya bakinki yarinya, kisan irin abunda zaki rik'a fad'aman" ya koma kan kujera ya zauna.

Murmushi kawai Maijiddah tayi ta shige cikin gida.

Karo na farko kenan da Khalil yake jin babu dad'i don ya daki Maijiddah, kasa zama yayi gaban gate d'in ya koma cikin gida.

Duk abunda suke Yawale najinsu yana d'akinsa amma bece komai ba, idan da sabo gidannan ya isa ace sun saba da fad'an Khalil da Maijiddah.

Parlour ya zauna ya kasa ya tsare yana jiran ganin fitowarta, domin a zahiri duk ya damu, yana jin motsin k'ofa ya juya da sauri, Hajiya Uwa ce ta shigo parlourn, kallo d'aya yayi mata ya kauda kai, sai ma ita ce tace "Auta su Fahad shiru basu dawo ba dai ko? Allah yasa lafiya"

"Lafiya k'alau" ya amsa a tak'aice"

Hajiya Uwa ta sake cewa "kayi Hak'uri auta game da marinka da nayi jiya, na tsorata ne don nasan halin d'ana komai yana iya faruwa"

Yace "ya wuce Uwa, kema kiyi hak'uri, kiyi hak'uri da irin tashin hankalin da nake saka ki aciki"

Kafad'arsa kawai ta shafa gami da murmushi, tsabar farincikin da taji yanzu kasa cewa komai tayi, domin atarihin rayuwarta da Khalil be tab'a bata hak'uri kokuma nadama akan wani laifi da yayi ba sai yau.

Daga wannan be sake cewa komai ba, saidai da yaji motsi sai ya juya da sauri kamar sabon b'arawo.

Kamar jira take yabar parlourn, yana fita ta shigo, ta tambayi Hajiya abunda za'a dafa yanzu, Hajiya tace "ki dafa faten wake, ki duba cikin drawers d'in nan na kitchen akwai inda aka aje bushashshen kifi, ki d'auka ki had'a dashi, ki duba a freezer kiga naman nan ze isa, idan baze isa ba sai aje a k'aro wani" Maijiddah ta amsa da to, ta mik'e ta tafi.

********************

Misalin k'arfe tara na dare, Maijiddah ta fito daga kitchen zata koma d'aki, shi kuma Fahad ya fito daga d'aki ze d'auko charger parlour suka had'e,

Murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa, suka gaisa sannan yace "naga alama tsoron allurata kike don duk yau bansaki a ido ba sai yanzu, rufe d'akin ki ma kikayi d'azu da safe, har muka fita baki bud'e ba, allurar da zafi ne ko?"

"Kai haba a'a wallahi babu zafi, kawai dai banason allura ne amma bawai don zafinta ba, naji dad'i da muka had'u kafin ku wuce gobe don inaso nayi maka godiya game da kulawarka akaina jiya, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" maijiddah ta k'arasa maganar tana murmushi.

Fahad yace "da Allah kibar fad'ar haka, kamar nayi miki wani abu? Ai hak'k'ine akan mu tunda muna kusa, naji kince kafin mu tafi gobe kina nufin bazamu had'u ba gobe?"

Maijiddah ta gyara tsayuwa ta jingina da bango sannan tace "eh wai ina tinanin haka ne shiyasa na fad'a"

Ya mik'a mata wayarsa yace tasa masa number ta, ta k'arema wayar kallo sannan tace "tabd'i ai ban iya wannan wayar ba kuma ni banma haddace number ta ba, saidai ka rubuta taka a wayata sai na kira kaganta"

Yayi dariya sannan yace "eh to kawo wayar taki"

Maijiddah ta koma d'aki ta d'auko wayarta, K'arar k'ofar Maijiddah da Khalil yaji, shi yasa shi fitowa daga d'akinsa da sauri.

Daidai lokacin Maijiddah ta mik'ama Khalil wayarta, ya rubuta number sa ya kira, yayi murmushi yace "yauwa gashi nan ta shigo nagode, zan tada ki koda kina bacci idan zamu wuce sai muyi bankwana" ya mik'a mata wayar.

Itama fuskarta cike da fara'a ta karb'a wayar tace "to ba damuwa, sai Allah yakaimu goben, saida safe"

Shima yace "saida safe"

Har suka bar wurin Khalil nanan tsaye jikin k'ofarsa kamar an watsa ma candle ruwa..........

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now