NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *14* 🌱
Khalil yayi shiru yanata faman raba ido, Maijiddah tace "dakai da kilbabbar y'ar taka idan baku da abun cewa sai ku matsa ku bani wuri zanyi shara"
Minal ta kalli Khalil irin kallon nan mai nufin 'bazaka ce mata komai ba?' tana jiran yace wani abu taga ya kalleta shima ya tab'e baki gami da girgiza kai sai kawai ta wuce d'aki, domin hakan da yayi yana nufin 'babu abunda zan iya yi akai'
Itama Maijiddah tayi masu wani jahilin kallo mai nufin 'dadai kun kyauta ma kanku'.
Khalil hankalinsa yayi mugun tashi don wallahi ko a mafarki be tab'a zaton Maijiddah zata dawo cikin gidannan ba amma sai gashi ya ganta garau, Maijiddah har ta bud'e baki zata sake magana kenan sai Allah ya taimakesa yabar wurin.
Yana zuwa d'akin Hajiya Uwa ya iske tana bacci sai kawai ya juya ya tafi d'akinsa, su Autan Hajiya da har anje aji yadda akai haka ta faru.
Koda ya koma d'aki kasa komawa bacci yayi don yasan hawan jininsa da ciwon zuciyarsa ta dawo.
Maijiddah ta gama aikinta kaf, ta fad'a kitchen, ta gama dube-dube tanaso taga me za'a dafa yau? Da taga ta rasa abunda zata dafa sai kawai ta fara fere dankalin Hausa, ga garin kunu nan zatayi masu kunu kuma, ta fere me d'an yawa yadda ze ishe su, ta zuba manta ta d'ora a wuta, ta yayyafa ma dankalinta gishiri kad'an yadda bazai fito ba amma ze kame, bayan da man yayi zafi sai ta zuba dankalinta, ta d'ora ruwan zafin da zatayi kunun tsamiya dashi ta zuba kayan yaji su citta kanunfari daduk wani abu da take buk'ata na kayan kamshi sannan ta maida ta rufe, tana juya dankali tana yanka lemon tsami tare da matsewa, bayan ta matse daidai wanda ze ishe ta, ta d'auko y'ar mitsitsiyar rariyarnan da akayita daman don tace abubuwa irin haka, ruwan tsamin tasa a robar da zata had'a kunun, ta d'ebo gari tasa acikin ruwan lemon sannan ta d'an k'ara ruwa kad'an ta jujjuwa kamar irin ruwan talgen nan, dankalinta ya soyu dai-dai lokacin ta kwashe ta k'ara sa wani, ruwan kunun ma yanata tafasa kayan yajin nata dahuwa sai k'amshi ke tashi, saida ta tabbatar yajin ya kama ruwan sannan ta d'auko rariyar k'arfe tasa kan robar had'a kunun domin tanason tace kayan yajin ne, ta d'aga tukunyar ruwan zafinnan ta shek'a cikin robar gari da ruwan tsaminnan da aka tare da rariya, saida ta zuba dai-dai yadda take tinanin kaurin kunun yayi mata saita cire rariyar ta rik'a juya kunun har ya tik'e, kunun yayi kyau sosai ko a ido, basu sa sugar a abu saidai mutun ya zuba daidai taste d'insa don haka shi yasa bata sa ba.
Ta bud'e freezer domin duba ko akwai naman da zata iyayin farfesu saiko taci sa'a akwai ma farfesun kaza warming d'insa kawai zatayi, ta fiddo tasa a tukunya ta d'ora a wuta, ta d'auko kununta duk ta d'urasa a tea flask.
Haka dai tayita girkinta har ta kammala, ta zuzzuba a inda ya dace kamar yadda ta saba, ta zubama Yawale nasa, taje ta jerasu a dining table sannan ta fita ta gaida Baban nata ta bashi abincinsa ta koma d'akinta ta kwanta.
D'an kwanciyar da tayi har bacci ya kwashe ta, caaan cikin bacci taji anata dukanta ana tadata, tana bud'e ido taga d'an halitta gabanta (Safwan 🤣) tace "ya kai kuma dame kazo? Wanene ma ya baka lasisin shigomin d'aki?"
Safwan cikin tsoro yace "Hajiya tace i should call u, kuma Mami tace kizo kiyi mana wanka"
"Wan... Me? a'a ba wanka ba ta manta wanki zanyi maka, nama wanka mata tafi yasin, gara ma da banji sak'on farkon ba, shima k'ila na rainin wayon ne tunda naji kace Hajiya, fita ka bani wuri wanka aka d'auko ni yi ko aikin gida, a'a tama ce nice na haifeku kawai"
Har Safwan ya juya ze fita tace kai zo nan, ya dawo daka gansa kasan a tsorace yake, tace "hala da baku wanka sai yanzu da kuka same ni zaku fara?" Shikam hausar ma ta masa tsauri bece da ita komai ba, tace "zonan, hawo nan kan gado kayi bacci kuba y'an gayu bane masu baccin safe, zoka kwanta kayi bacci idan ta gama yima sauran wanka tazo ta d'auke ka kaima tayi ma"
![](https://img.wattpad.com/cover/168174266-288-k797868.jpg)