25

1.2K 72 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

               🌱 *25* 🌱

"Mtsw kefa wallahi ba'a iya maki, ta yaya za'ai na siyar dake?" Ya tambaya cikin fushi.

"A'a wallahi idan ma kaga laifina to da gangan tunda dai wani abu ne wanda bansaba jiba, haka kawai yau rana tsaka kace inzo mu fita?" Inji Maijiddah.

Khalil dai yaga sai zuba take kuma bata da niyar zuwa su tafi yace "kinga malama zaki je ko bazaki je ba?"

"Kuttt karen mahaukata ya cijeni ne? Allah ya raka taki gona, Allah ya tsare adawo lafiya amma ita dai Maijiddah kam tana gida, idan ma wani abu ka shirya to ya k'are maka can".

Khalil ya sake sakin wani guntun tsaki gami da cewa " Allah ya kyauta" sannan ya fice.

Maijiddah fa tama kasa cigaba da aiki don tsananin mamaki, abunka da ba'a saba wa, wai ta raka shi cikin gari (koni marubuciyar danaji saida na jinjina bare ita uwar gayyar.

**************

Tunda Kamal ya dawo ita dai Maijiddah sai taga be damu da kallo a parlour ba saidai koda palourn ze fito zaka ganshi da laptop d'insa a hannu yana kallon fina-finan turawa, ita kam tana mamakin yadda akai har yake gane abunda suke cewa, hardai tagaji wata rana suna parlour zaune tace "Waini don Allah kana gane abunda suke cewa koko dai kallonsu kawai kake?"

Yayi dariya mai isarsa sannan ya tsaida kallon da yake ya juyo gareta.
"Ina fahimtar yaren, na iya ne kuma ina ganewa sosai sosai, kema idan kika dage zaki iya, turanci ne suke ai"

"Tabd'i ta ina zan iya, shiwai turancin nan inaga kala-kala ne ko? Saboda nidai turawannan sai na gama kallonsu har na tashi banji sun fad'i kalma d'aya irin namu turancin ba, shiyasa wani lokacin sai naji kamar suna wani yare, kokuma ni sai naga kamar ba dai-dai muke turancin ba"

Kamal ya sake yin dariya a karo na biyu.
"Aiko irinsa ne Maijiddah, sai akwai bambanci wurin fad'i ta fatar baki, mafi yawancin mu bamu iya karya kalmomin irin yadda su sukeyi saboda ba yaren mu bane, amma dukda haka wanda Allah ya bashi baiwar iya turancin zakiga yanayi kamar bature, amma inajinsu sosai kamar yadda nake jin hausa"

"Dagaske?" Maijiddah ta tambaya cike da mamaki.

Khalil yana daga gefe yana kallonsu, shikam yana mamakin yadda Maijiddah ke sakin jiki da Kamal haka, idan yaga suna fira suna annashuwa sai yaji haushi, sai ya rik'a jin dama shida ita ne haka.

Kamal ya cigaba da cewa "alamu sun nuna kinason boko kuma kamar bakiyi karatun boko ba, amma meyasa bakiyi boko ba?"

"Hmm wallahi duk laifin Baba ne, wai bayason muyi karatun boko, nikam ina mutuwar son naga ina turanci" ta amsa.

"Turanci kad'ai? to ai turanci ba boko bane, turanci yare ne, kamar yadda kike ganin yaren fulani, hausa, yoruba, igbo, kanuri dadai sauransu, haka shima turanci, idan kika sa kanki kuma kikayi dace da wanda ya k'ware zaki iya dai-dai gwargwado, baza'a ce dika ba tunda misali ko hausa da take yarenki yanzu na tabbata akwai abubuwa da yawa wanda baki sani ba saidai idan hausar kike karantawa a makaranta zaki rik'ajin kamar baki tab'a iya hausa ba ma, kamar ba yarenki da kika sani ba"

Ya tsaida kallonsa ya biye mata sunata fira, shiko Khalil ya k'ura ma TV ido amma hankalinsa gaba d'aya yana wurinsu.

***********

Yawale na zaune inda ya saba zama gaban gida Kamal yaje ya samesa.

"Baba Yawale nayi kewar firarmu dakai, saboda kana koyaman wasu abubuwa na rayuwa, tarihi, aladu da wasanni na hausa da bansani ba cikin hikima, ina tarihin Bala d'an Musa da muka fara dakai shekarar data wuce kafin nayi tafiya?, ya yak'are da annamiman fadawan sarkin nan kuwa?"

Yawale ya gyara zama yace "nayi kewarka Kamal, kullun kana cikin raina don inajin dad'in zama dakai, kai mutunen k'warai ne ka cigaba da haka Allah nasan mutane irinku, baka da matsala nidai a iya sani na"

Suka cigaba da firarsu har akayi kiran sallar Magrib suna nan zaune, sannan suka tashi domin zuwa yin sallah. Ashe Maijiddah ta mak'ale saitin window tana lek'ensu tana murmushi, Khalil ya isketa a haka, sai ya matso saitin kanta domin lek'en abunda take kallo, koda yaga Kamal da Yawale ne zaune suke fira sai yaja tsaki ya juya, da sauri ta juyo domin ganin daga inda tsakin ya fito don bata ma san zuwansa wurin ba, har ze fice tayi sauri tace "y'allab'ai, tsaka sarkin tsaki, me nayi maka da zaka zo saitin kunne na kajamin tsaki?"

Ya k'ara jan wani tsakin ya wuce.

"Kai ma mtswww" Maijiddah ta fad'a tana murgud'a baki bayan daya wuce.

Da daddare bayan isha'i, Maijiddah ta gama girkin dare, Kamal ya fito da carpet hannunsa da system da wayarsa, Maijiddah tace "Ina zaka je ga abinci an gama?"

"Babu inda zanje inaso na zauna tsakar gida ne, plz taimaka min da abincin ki kawo man waje" ya fad'a yana wucewa waje.

Maijiddah taje ta zubo masa abincin ta kai masa, har zata koma cikin gida ya tsaida ta.

"Ki zauna muyi fira mana, ki bani labari ko tatsuniya"

"Tatsuniya kuma, haba dai sai kace yaro?" Maijiddah ta fad'a tana dariya.

Shima dariyar yayi kafin yace "nima ai yaro ne ki zauna" ya fad'i haka yana d'an matsawa gefe gami da jawo abinci gabansa.

Batayi gardama ba ta nema wuri ta zauna.

Tana masa shirme yana dariya, duk abunda tayi burgesa take, bakamar idan yayi magana sai tace "kaii haba dai".

Be tab'a jin ta kira sunansa ba, hakan yasa ya tambayeta ko meye dalilin dayasa bata fad'in sunansa? Sai ta sunkuyar da kai k'asa tana murmushi tace " babu komai ina fad'i baka ji ne"

"To fad'i inji" ya kafeta da ido.

Aiko ta tuntsure da dariya tace "kai don Allah"

Tana rufe baki wayarta ta tsandara uban k'ara alamar shigowar kira, tana ganin Fahad ne ta kifa wayar tak'i d'auka, Kamal ya tambayeta "meyasa bazaki d'aga ba? Hala sirikin mu ne ya kira?" Da sauri ta girgiza kai tana murmushi.

Haka suka yita fira, Maijiddah batasan dalili ba, amma tanajin dad'i da natsuwa aduk lokacin da take tare da Kamal, acewarta "yanada kirki" to nima dai sheda ce akan hakan.

Hajiya Uwa fa tana ganin ikon Allah wurinsu, yanayin yadda Kamal ke sake ma Maijiddah bata jin dad'i, har kiransa tayi ta fad'a masa yarinyarnan bata da kunya bata da mutunci ya dena wasa da ita idan ba haka ba zata raina shi.
Sai dai yace "Kai Uwa nikam banga aibun yarinyar nan ba"

Taji haushin amsar sa tace to shikenan yaje shiya sani.

Malam Khalil fa Kamal yana shigar masa hanci da k'udundune, saidai shid'in ya kasa gane dalilin da yasa yake jin zafin hakan.

A b'angaren Fahad kuwa yadena samun magana da Maijiddah akai-akai kamar yadda ya saba tun bayan dawowar Kamal.

***********

Sukayi bankwana da Alhaji kamar karya tafi, yayita sa masu albarka, yace da su Khalil da Kamal "ga k'anwar ku nan da Mahaifiyarku akula dasu, a kula da gidan nan, don Allah Khalil banda rashin ji"

Alhaji na fad'in haka Khalil ya juya yaga ko Maijiddah na kallonsa, aiko sukayi ido hud'u, haushi ya kamasa shi wai karta raina sa (har na nawa kuma), aiko hada murmushin munafurci ta sakar masa.

Alhaji ya shiga mota Kamal ya tafi kaishi airport.

**************

Yau Juma'a mazan gidan nata shirye-shiryen tafiya  masallaci, bayan sun shirya tsaf suka fito zasu wuce, Maijiddah tana share parlour lokacin, Kamal yace da ita "ya nayi kyau?" Ya tambaya yana murmushi.

"Sosai ma" ta fad'a a tak'ace, itama murmushin take.

Khalil na bayansa suka fita tare, har zasu shiga mota Khalil yace da Kamal "don Allah ina zuwa" Kamal ya shiga motar ya zauna yana jiransa.

Kamar yayi mantuwa zeje ya d'auko.

Ya shigo parlour yace ma Majiddah "Jiddah ya nayi kyau?"

Saida ta gama kallonsa sama da k'asa sannan tace "ina ruwana da kyanka da rashinsa, gasa ce wannan ko kilbibi?..........

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now