*NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *12*🌱
"Hmmm kedai bari" ta fad'i hakan tana mai gyara zama.
"dama Bilki tace kullun idan aka aikota wurina idan bana nan sai yayita jawota yana nuna mata gabansa wai tazo ta tsotsa, ita kuma sai tak'iya ta gudu, to ranar nan sai wata k'anwarsu dake aure can k'auyen Marufi ta haihu, akace za'ayi zuga atafi gaba d'aya y'an uwa, ni bana ma jin dad'i sai nace bazan iya zuwa ba aiko saida ya tilasta min lallai sai naje, na daure na shirya yabani kud'in mota na tafi can gidansu inda zamu had'u da sauran y'an uwa, to anan nefa ya samu damar aikata abunda yaso, a yadda Bilki dakuma k'awarta suka ce wai sunzo wucewa ta hanyar gidana ne sai suka gansa k'ofar gida sai ya kira Bilki yace wai tazo ina nemanta, zasu shiga tare da k'awar tata yace karta shiga tayi gaba idan Bilkin ta fito zata sameta a hanya, yarinyar tace to ta tafi, Bilki na shiga gidan ya turo k'ofa ya rufe ya sunkuce ta sai d'akina bisa gado, aiko garjejen k'aton la'anannen mutunen nan ya afkamata, tana ihu amma saida ya mata lilis"Maijiddah tace "wa'iyyazubillah amma yayi asara"
"Babba ko ba k'arama ba, aiko ina fad'a miki, dayake Allah ya nufa sai asirinsa ya tonu, gidansu da naje nandanan zazzab'i ya rufeni na rik'a kwarara amai, Ummarsu tace k'annensa su rakani gida infasa zuwa sunan tunda ba dole bane, aiko hada yayarsa su uku suka rakoni, muna zuwa gida muka ga gida a rufe muka bubbuga shiru, nace su duba y'ar jakata (purse) akwai makulli su d'auko k'ila ya fita ne, aka d'auko makulli aka bud'e muka shiga, muna shiga muka rik'a jin kukan yarinya sama-sama kamar mai hararramin mutuwa, ni bani ma da k'arfin rugawa, k'annensa da yayarsa sune sukayi saurin lek'awa d'akin domin ganin waye a ciki, nan nefa suka ci karo da wannan mummunan tashin hankali, dangin miji da ba'a iya masu yauda ace ni kad'ai na gani suna iya cewa sharri muka yima d'an uwansu, nanfa suka hau sallallami, inajin haka na tak'ark'ara na k'arasa cikin d'akin, take a wurin na suma bayan ganin wannan aika'aika, suka kwasheni sukayo waje, suka d'auko Bilki itama dak'yar take lumfashi, saidai na farka na ganni asibitin hayi, hmmm ai Maijiddah naga k'addara aiko banga ta zama ba wannan aure dole aka raba shi, ke haryanzu fa ba'a gama shari'a ba don mun maka shi kotu (court)"
Maijiddah ta rik'e baki gami da cewa "ummmm, ke duniya ina zaki damu? Wannan ai dole sai haka, Allah yayi masa abunda yayi maku"
Suka yita jimami, sannan Maijiddah tayita bata hak'uri da lallashinta, amma fa har cewa take "hmm har na hango k'anwata aka yima wannan ai inaga yasin saina kashe ka saidai bayan na kashe ka a kashe ni kan Uba, wai meke damun wasu mazan ne? To mema ze d'iba a jikin wannan taliliyar y'ar?"
Asabe tace "hmm jiki da wata magana, aka yima jarirai fyad'e ma bare tsararrakin su Bilki, ai kedai kawai rayuwar nan ta yanzu saida kula dakuma addu'a"
Bayan wannan saida suka sha firarsu har Maijiddah taba Asabe labarin birni dasu Khalil suka sha dariya sannan daga bisani ta mik'e zata tafi, Asabe tasa mayafi ta fito rakiya.
Suna tafiya suna k'ara zantawa sai ga wani nigan k'auye ya taho yanata bouncing ga wani uban tabarau yasha, yasa jeans da tsanwar riga, gashi bak'i na mutunci sai ya k'ara rinewa cikin kayan, ya wani sha gaban su Maijiddah yace "y'an mata ji mana"
Maijiddah ko kallon inda Allah ya ajesa batayi ba, sai Asabe ce tayi k'ok'arin cewa "kai lafiya, dawa kake ne?"
Yaja wani guntun tsaki sannan yace "baki ganni bane? Ai kinsan kalata, don haka bada ke nake ba" ya maida dubansa kan Maijiddah ya cigaba da cewa "to yane y'ammata minti biyu mana"
Ga mamaki na sai naga Majiddah ta tsaya, a zatona ko ta samu zab'inta ne, ta k'ura masa ido yanata santo haukarsa idan ya kama waccan tashar sai ya saki ya d'au wata, taga dai beda niyar gama wa, ta dakatar dashi ta hanyar nuna masa tafin hannu tace,
