17

1.4K 70 1
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                🌱 *17* 🌱


"Hmmm naji zan gyara, kuma ai nama gyara kune baku gani" inji Khalil.

Hadiza tace "eh ai dayake mu makafi ne shiyasa bamu gani ba, nidai kaji abunda na fad'a maka"

Yadai ce mata "to" (ai bata kisa)

Bayan sun gama wannan maganar suka d'au wata firar kuma ta daban.

***************

Khalil yazo wucewa yaji k'ira'a na tashi, muryar gwanin dad'i kamar ya zauna yayita sauraro, Maijiddah ce take karanta Suratul yusuf cikin natsuwa.

Yana nan yayi tsaye dai-dai d'akinta kamar gunki saiga su Minal, Safwan yace "Uncle k  wat re u doing here?"

Minal zatayi magana Khalil yayi sauri yace "shhhhh did u hear dat?"  Ya fad'i haka yana mai kare kunne da tafin hannunsa d'aya, alamun yanason sauraron wani abu, sukayi shiru gabaki d'ayansu kamar ruwa ya shanye su.

Sunsha uban tsayuwa, har saida ta fito daga d'akin domin yin wani abu a waje, aiko sai taci karo dasu tsaye cokar-cokar gaban d'akinta.

Tace "kai lafiyanku, meya faru haka?"

"Karatunki muke saurare tun d'azu, Aunty Jiddah mu koma ki cigaba muryarki mai dad'i" inji Minal,  Safwan ma yace "eh Aunty Jiddah muje kiyi mana kinji plzz?"

Khalil saidai ya saki baki yanata raba ido kamar yayi k'arya, Maijiddah tace "kai kuma fa ya akai, ko kayi makuwa ne?"

Girgiza kai kawai yayi ya wuce, Maijiddah itama sai ta bisa da kallo cike da mamakin rashin kulata da beyi ba, don ta saba koyaya ne sai sunyi cacar baki, a k'arshe ta tab'e baki tace "can da yawarka" taja su Minal suka koma cikin d'akin nata suka cigaba da karatu.

Hadiza ta shigo d'akin Maijiddah taga yaran nata karatu, tayi murmushi tana kallon su.

"Jiddah kenan Auntyn yara, sannunku ashe haka kike da k'ok'ari?" Inji Hadiza.

Murmushi itama ta mayar mata kafin nan tace "kaiii Maman yara wai k'ok'ari, munadai dagirawa da ikon Allah"

Cikin yabawa Hadiza tace "to ai haka akeso, dama ni keda k'ira'arki da naji dad'i, Allah yasa yarana suyi kamarki nan gaba", Maijiddah ta amsa da Amin tana mai murmushi, sannan Hadiza ta cigaba da cewa "uhm dama Maijiddah inata so na baki hak'uri game da abubuwan da suka faru tsakanin mu gidannan kafin mu tafi, kiyi hak'uri, zama dake ya k'aramin ilimin wasu abubuwa da dama na game da zamantakewar rayuwa, kiyi hak'uri don Allah"

Maijiddah tace "kibar cewa haka, kunya ma kike bani, ai rashin fahimta ne kuma gashi yanzu mun fahimci juna, nima kiyi hak'uri da irin yadda nake miki keda yaranki, nidai gani k'arama kuma ba kowa ba amma banason raini ko wulak'anci, bana jure su, kiyi hak'uri kema"

Hadiza tace "babu komai"

Suka ba junansu hak'uri sannan suka cigaba da karatunsu ita kuma Hadiza tana binsu da kallo cike da ban sha'awa.

Bayan wasu awanni.

Hadiza ta koma d'akinta sakamakon kiranta waya da wata mak'ofciyarta tayi.

Tana cikin wayar ne Hajiya Uwa ta shigo sai ta nema wuri ta zauna.

Saida ta gama Hajiya tace "wai keda waye ne, ince dai ba wannan jahilan matan kike biye mawa ba?"

Hadiza tace "kai haba Uwa wallahi sam bana ma da ra'ayi, masu saida magungunan mata kodai bokaye, kinga wata mak'ofciya ta ce wallahi bata ma gajiya, kullun sai tayiman tallar kayan bokancinta da take kira maganin mata kuma bana saye, wallahi Uwa idan kika gansu sai sun baki tsoro da k'yama, dakin gansu kinsan babu Allah aransu, maganin kad'ai suke bautawa, shi suke ganin ze iya masu komai"

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now