22

1.3K 72 1
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

               🌱 *22* 🌱

Caaan cikin bacci Maijiddah tajiyo k'arar jackiechang d'in wayarta, ta amsa kiran, tana sawa a kunne taji muryar namiji aisai tayi sauri ta tashi zaune, saida ya k'ara magana sannan ta gane ashe Fahad ne.

"Ki tashi kiyi sallah asuba tayi, don har mun shirya, da mun idar da sallah insha Allah zamu tafi"

Maijiddah tana murza ido tace "kai haba tun da wuri haka? To bari na tashi na dafa maku wani abu ku samu kuci kafin ku wuce"

Fahad ya hanata yace basai ta wahalar da kanta ba, zasuci a hanya kuma ga Khalil ya kawo masu ruwan zafi yanzu.

A haka suka datse kiran, ta tashi taje tayo alwala suma suka fara sallah.

Sun firfito gaba d'ayansu tare da Khalil saiga Maijiddah ta fito itama, wani irin mummunan kallo da yayi mata har saida nima na b'oye kar a had'a dani marubuciyar.

Itako gimbiyar ko ajikinta, ta gaisa dasu gabaki d'ayansu, sauran suka d'anyi gaba suka barsu sud'an zanta, Khalil ko yayi masu tsaye saida wani a cikinsu ya jashi tukunna.

Fahad wanda fuskarsa ke cike da annuri tun isowar Maijiddah wurin yace "Jiddah sorry na tadaki bacci ko? Ya jikin ki?"

"Kai haba, ai ba komai ka kyauta daka tadani saboda lokacin sallah yayi dama, jikina kuma naji sauk'i sosai ai inashan magani" cewar Maijiddah.

Fahad yaji dad'i sosai dajin hakan, batajin son Fahad aranta koko don batasan ya ake ji ba amma taga take-taken sa shi so yake yace yana sonta (batama san ya riga ya furta ba), saidai tanajin nauyinsa tana kuma ganin girmansa.

Khalil ya kasa d'auke idanuwansa daga kallonsu, isowar su Alhaji wurin yasa shi maida hankalinsa inda suke, suma su Fahad da Maijiddah k'arasowa sukayi wurin.

Suka gaggaisa dasu Alhaji da Hajiya, Alhaji yayita sa masu albarka yana godiya, Hajiya tayi masu fatan isa gida lafiya, sannan tace da zarar sun sauka su kirasu.

Wani irin kallo na soyayya Fahad ke yima Maijiddah, itako sai yak'e take kamar ragon suna, duk abunda suke ciki Khalil na kallonsu.

Da suka shiga mota Fahad yayima maijidda nuni da hannu alamar dake nufin "Sai munyi waya" ita kuma ta gyad'a masa kai gami da murmushi, Yawale ya bud'e masu gate suka wuce.

Su Hajiya suka koma cikin gida, Maijiddah ta gaishe da Mahaifin nata sannan ta shige ciki itama.

Yawale yaga Khalil yayi tsaye ya fad'a wani dogon tinani, sai yace dashi "Sannu Auta, antashi lafiya"

Sai alokacin hankalinsa ya dawo jikinsa "Yauwa" amsar da Khalil yaba Yawale kenan atak'aice sannan ya koma cikin gida shima.

Maijiddah bata koma d'aki ba, sai kawai ta kunna karatun Qur'ani a wayarta ta cigaba da aikin gida.

****************

Bayan wasu y'an kwanaki.

Waya Maijiddah da Fahad sukeyi sosai, a rana sai suyi sau kamar biyu ko Uku, da idan suna waya yakan d'an rika jefo mata kalmomin turanci amma sai Maijiddah ta sanar dashi itafa bata ganewa saidai idan ya fad'a ya rik'a fassara mata ko ta d'an k'aru dashi, ya amince da hakan, to haka fa suketa wannan soyayya, koda yake shi kad'ai ke yinta.

Shiko Khalil ya zama Yawalen Maijiddah, Ma'ana 'Maigadin Maijiddah' duk inda tayi yana biye kamar bindi, da an kirata a waya kome yake sai ya dakata yaji ko waye, sai idan yaji daga k'auye ne sannan hankalinsa ke kwanciya, idan ko aka kirata ta shiga d'aki sai yaji kamar ya bita d'akin.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now