23

1.3K 65 0
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

               🌱 *23* 🌱

Wannan kace nace dai yak'i ci yak'i cinyewa, har saida labari ya isarma gidan yayar wannan budurwa, aiko ta ziri mayafi suka fito tare da mijinta don ganin abunda ke faruwa.

Wannan saurayi me mota yace shi wallahi yau sai yaga wanda ya isa ya rabashi da wannan yarinyar y'ar gidan uban waye ita?, shi bema tab'a ganin koda mai kama da ita ba.

Bayan ganin Yayar wannan budurwa da mijinta a wurin da Maijiddah tayi, memakon bakinta ya mutu sai kuma ta juya kansu "oooo ashe ba wancan d'in bane kaine, kaine mijin yayar tata kenan?, ai na zata wancan ne, ashe kaine maci amanar, Yayar ta matso gaba tad'an ja hannun Maijiddah dake mak'ale a k'ugunta tace "ke me kike cewa ne? Ban fahimce kiba"

"Dama yaza'ai ki fahimce ni tunda ana abu a gidanki, tsabar so da yadda yasa kin makance kin kasa bud'e ido kiga wutar dake ruruwa a gidanki, to wancan abun da kuka taho dashi ba mijin aure bane, maci amana ne, fasik'i ki ne, munafiki ne, saboda ya rasa dame ze saka ma iyayenki dashi bayan bashi aurenki da sukayi, sai ya zab'i ya had'aku biyu yana kashe wutar gabansa, ya kwanta dake ya kwanta da k'anwarki gatanan tsaye kuma tanaji tasan ba k'arya nake mata ba, ya fita da ita suje suyi holewarsa sannan idan baki nan ya kawota gidanki ta maye gurbinki, shima gashinan tsaye idan k'arya ake mas... Matar nan ta tattakura ta kifa ma Maijiddah mari kafin takai Aya, aiko itama kafin ta aje hannu taji saukar mari, sannan Maijiddah ta nunata da d'an yatsa tace "kinci sa'a bansan inda zan k'ara had'uwa dake ba amma daban rama marin nan yanzu ba, na rama ne saboda kisan cewa ni bana barin kota kwana, gaskiya wadda mutane da dama ke shakkar fad'a maki don gudun hukunci irin wannan da kika d'auka ni kuma na fad'a, saura ya rage naki ki d'auka ko karki d'auka duk d'aya, kuma ki sani dukda na rama ban manta marin nan ba.
lokaci guda zufa ta fara keto ma Mijin, ya fara b'ab'atu kamar ze daki Maijiddah "ke ubanwa ya tsaya miki a garin nan? Da mutunci na zaki zubarmin dashi a gaban d'inbin jama'a, mak'aryaciyar banza kawai, anya ba mahaukaciya bace ke?"

"Mutunci? Ai baka masan meye mutunci ba, domin da kasan meye mutunci da bazaka cigaba da tinanin naka yana nan a hannunka ba saboda ya riga ya zube, a idon kowa ma baka da k'ima, kana ma mutane kallon biri su kuma suna maka kallon Ayaba, babu ubanda ya tsayamin nina tsaya ma kaina, kune kuke shakkar yin abu don baku da magoya baya, ni indai kan gaskiyata ko y'ancina ne bana jiran goyon bayan wani face Allah" yayo kanta aka rirrk'esa hada matar, shikam saurayin yarinyar ma sai ya tsaya yanata kallo da sauraron ikon Allah, saida wani mutun yace Alhaji ya kamata muje akai yaron nan wurin me kamu don ya bugu gaskiya, da alama k'afarsa akwai rauni k'ila ma karaya, suka shiga da yaron motarsa yaja suka tafi yabar Maijiddah nan tsaye da yaya, k'anwa da maigidansu (🤣🤣🤣 saidai ace maigidansu kam).

Mijin wannan mata yace shifa wallahi sai yaga wanda ya tsaya ma yarinyar nan, me rabasu sai shari'a (kuji k'arfin hali wai akace sata lahira, dakuma nad'e tabarmar kunya).

K'anwar wannan mata tayi tsuru-tsuru alamar rashin gaskiya, kunsan ance shi marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, shiko mijin dayake kunsan maza sunfi mata iya k'iri-k'iri sai bambami yake shi da bala'i anyi masa k'azafi, itako maijiddah sai kad'a k'afa take gami da murmushin rainin wayo tana fad'in ni nafiso aje ga hukumar ma, don bincike ai bebar komai ba, anan za'a gane waye Abu waye Garba.

Wannan mata sai tama rasa abun cewa ta rasa wace magana zata kama, don dukkan alamu sun nuna Maijiddah iyakar gaskiyarta take fad'a domin babu shakkar ko tsoro atattare da lamurranta, to amma a wani b'angaren kuma ta kasa yadda gaskiya ne don irin yaddar da tayima mijinta, asalima ko k'awayenta babu ruwansa dasu saidai gaisuwa, bata ganin yana kula mata, ko a gabanta ne yake nuna hakan? oho, sannan tana ganin babu yadda za'ai y'ar uwarta uwa d'aya uba d'aya tayi mata haka, shiyasa ta zab'i tayi shiru domin k'wak'walwarta ta samu tad'an yi nazari.

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now