16

1.3K 67 1
                                    

*NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                 🌱 *16* 🌱

Nunata da d'an yatsa Khalil yayi yace "ki shiga taitayinki na fad'a miki, ya kamata kisan iyakar ki, i can see dat u re taking more dan u can chew, if u dnt hv respect i wl teach u some, Village illiterate kawai"

Maijiddah ta tab'e baki tace "oho dai ansha kirci sai kace me k'azuwa, niko nasha dariya iya yadda nake so, ai hakan shine daidai dakai"

Yamutse fuska yayi gami da kashe ido d'aya ya matso daf ta ita yasa idanuwansa cikin nata kamar zeci ubanta yace "now tell me, waya samin k'aik'ayi a jikina kece ko?"

"Ah to ai malam ba tambaya bace wannan, ina zanga jikin naka da har zan zuba maka k'ai-k'ai? Hala ni matarka ce bani da labari? Ce maka akai nikuma bani da wani aiki sai farautarka? Kaidai kasan inda ka kwaso k'ai-k'ai amma bani ba, au yi hak'uri fa duk wannan fushin nasan na rashin sosa maka ne dabanyi ba, to yana iya tunda naga Hajiya nata faman karta"

Ta juya ta cigaba da aikinta tana wata wak'a ta zamanin da da akayi acikin film d'in *JEEF* wadda ake cewa *'Kaf jikina na k'aik'ayi masoyi kazo ka sosamin, yaka jeef, yaka jeef, ka tausaya min ka agazamin sonka yasani d'imuwa'* 🤣🤣

Shidai gogan nawa yasan dashi take amma sai kawai yayi tsaki ya wuce, itako ta dakata da wak'ar ta cigaba da b'ab'b'aka dariya.

***************

"Hadiza maganar gaskiya mijinki yayi min bazata, Abdulhamid ba, tabbas yaban mamaki domin sam beyi kama da irin mazan nan da sukayi k'awa da duniya ba, kuma wannan ba k'aramar magana bace ya kamata Babanku ya kirasa ya tambayesa dalilin abubuwan da yake miki, ace miji kawai sai yabi ya kulle matarsa ta waje har yaje inda zeje ya dawo, sai kace shi kullesa kikai? To abun Allah ya kyauta idan wani abun fita ya faru fa kokuma wani abun ceton rai saidai ki mutu aciki? Ya kamata yazo ya fuskance mu, mu tambayesa muji shin yadda dake ne beyi ba koko ya akai?" Inji Hajiya Uwa.

Hadiza tace "wallahi Uwa nima abubuwan na damuna, kuma ace kana magidanci kaje ka yini ka kai dare a waje, ai yakuma kamata ace idan ka dawo ka tsugunna gida kabama iyalinka hak'k'insu, to saidai fa ya cigaba da danna waya yana chat da yammatansa, niko ko oho, haba don Allah Uwa ai ba'a haka"

"Sosai kuwa, sosai kuwa, inafa ake haka ai saidai a wurinsa shi sakaran, Hadiza banda abinki ai ko a k'auye an dena yaji, zama kake cikin gidanka kayi yak'inka ka kwashe shararka kai kad'ai, ke yanzu anma zo wani zamani da za'a saki mace tak'i zuwa ko ina, ta zauna tayi iddarta gidan mijinta kamar yadda musulunci ya tsara, haba Hadiza, kiyi hak'uri zan sami Babanku zamuyi magana idan ta kama a kirasa zamu kira, kamar yadda na fad'a miki, duk wanda kika gani a gidan aurensa hak'uri yake, ki cigaba da hak'uri dakuma addu'a, kardai ki gaji da kyautata masa har Allah ya ganar dashi gaskiya, zamanin ne ya b'aci abun babu babba babu yaro, da maza sun kama y'an canji a hannu sai kika mummunan halinsu nata bayyana wasu daman talauci ke b'oye asalin suffarsu, wasu ko acikin talaucin ma nunawa suke, babu wanda yake d'ari bisa d'ari, dole kowa da inda Allah ya ragesa, ki zage damtse wurin kula da buk'atun mijinki dakuma kula da gidanki gaba d'aya, karki manta da addua domin itace makamin mumini"

Hadiza tace "to insha Allah Uwa"

Nandai Hajiya Uwa ta cigaba da kwantar mata da hankali tana kuma bata shawarwari.

*******************

Bayan kwana hud'u.

Khalil na parlour daga caan dining area, hakima sarauniya Maijiddah kuma nakan kujera zaune ta hard'e k'afa ga remote a hannunta tanata kallo, Khalil saidai yad'an saci kallonta ya yayi dariya, don dariya take basa yadda tayi zaman kamar wata maigidan, kamar Hajiya Uwa.

Minal da Safwan suka  shigo, minal ta kalli TV ta kalli Maijiddah sai tace "could u plz change d station 4 us, we wanna watch cartoon and it's tym alrdy?"

Safwan yace "yes plzzz"

🤣🤣🤣🤣🤣

Ko kallon inda suke Maijiddah batayi ba, saboda bataji komai acikin turancin ba sai cartoon, saiko kalmar 'plzz' dataji Safwan ya fad'a.

Khalil dake can gefe ya fashe da wata iriyar dariya amma marar k'ara batare da sunji ba, saida yayi mai isarsa sannan yace "eh ehmm, U knw wat kids?"
Suka juya dubansu garesa gami da girgiza kai.

Shi kuma ya cigaba da cewa "y not u try speaking Hausa 2her instead? coz u c, dat lady sitting down there doesn't understand English"

Minal tace "bt Uncle K Our nanny does"

"Yh dats only coz she's ur nanny, bt dat lady isn't ur nanny, so 4rm now on i wnt u 2b speaking Hausa 2her and i also wnt u 2b calling her Aunt ok? dat way ur Uncle K wl b so  happy wt u, i wl even buy u ice cream, i promise"

Gabaki d'ayansu suka ce "Ok Uncle K"

Ita dai d'imasa'un (Maijiddah) babu abunda yasha mata kai kallonta kawai take domin bataji me suka ce ba.

Safwan yace "Aunty Jiddah don Allah ki canza mana station munaso mu kalli cartoon"

Minal ma tace "eh don Allah Aunty
Jiddah sun fara tun d'azu"

Maijiddah tabisu da ido, acikin zuciyarta tace "wai su wannan y'an birnin meke damunsu ne? Me yaci *Mai* d'in da basu iya cewa Maijiddah sai Jiddah? Kuma wai nice Aunty anya bawani makircin suka k'ulla ba don dama naji sunyi turanci, amma kuma Auntyn da dad'i har naji kaina yayi k'ato"

Saida Safwan yad'an tab'ata sannan hankalinta ya dawo, ta mik'ama Minal remote d'in tace sukai inda suke so, sai tama tashi tabar parlourn, sukayita tsalle suna jin dad'i.

Murmushi Kawai Khalil yayi, ya cigaba da latsa waya.

******************

Abdulhamid ya iso gida kamar yadda Alhaji da Hajiya suka Umarcesa, suka tarasu dashi da ita Hadizar, suka yi masu nasiha mai shiga jiki sosai, Abdulhamid ya ba Hadiza Hak'uri tare dayi masu alk'awarin ze gyara insha Allah, amma fa yananan akan bakansa na cewa bazatayi aiki ba, su Alhaji sun kuma yadda da hakan. Duba da irin yadda su Safwan basuson tafiya gashi kuma hutu suke yasa yace suyi zamansu sai next wk sai su tafi gaba d'aya.......

********

Ance mai yaro sakarai, wata shak'uwa ta bazata ta fara shiga tsakanin Maijiddah da yarannan, duk inda take suna nan, idan basu d'akinta to suna tare da ita parlour, Minal kam har kitchen take bin Maijiddah tana tayata aiki, ita kuma tana  kokkoya mata girki, dukda cewa k'aramar yarinya ce amma koma menene dai ai mace ce, da rarrafe akan fara tafiya sannan shi icce tun yana d'anye ake tank'wasa shi, ba laifi bane don ka shiga da yaronka kitchen, wasu sunada saurin fahimta, suna lura da duk yadda kake abubuwa, hakan ma wani mataki ne maikyau na koya ma yaranmu mata girke-girke.
Wannan shak'uwar ce tasa Hadiza ta fara son Maijiddah, don wasu lokutan hatta Aila hannun Maijiddah take zama suyita wasa da yaran.

Khalil yana masifar son zama ya rik'a kallon su idan suna annashuwa abun burgesa yake, har ya rik'a mamakin "dama haka Jiddah take?"

***********

Hadiza tace "Khalil duk duniya baka da wanda suka fimu, haka kuma baka da wanda zasu iya baka shawara maikyau sama damu, shin wai ko baka tinanin aje naka iyalin ne arayuwarka? Wasu abubuwan naka sukan bani mamaki, to inaso kasani dole saika saki komai ka kuma saki kowa ka kama Allah dakuma kanka, dukiyar wani ba taka bace, ka tashi ka nema naka tun kanada hanya mafi sauk'i ta aikata hakan, ina nufin tun iyayenmu na raye basu mutu ba, kakai girman daya kamata ka fara tinanin kanka, ka fara aiki ko sana'a, kayi aure, ka hayayyafa kamar kowa"

Khalil yace "naji bank'i ta taki ba, amma meyasa bazaku fara yima Kamal fad'a ba ya fara yin aure tukunna? Ai shine sama dani"

"Eh shine sama dakai amma ai ba zaune yake ba, kuma ba halinku  d'aya dashi ba, yasha boko ya k'oshi sannan business d'insa yake, idan yanzu ya gadamar aure zeyi kuma ze zauna lafiya da iyalansa batare daya nemi taimakon kowa ba, domin ko ya tsaya da k'afafunsa, kai kuma fa? Don Allah ba don muba, ka duba soyayya da sadaukarwa irin wadda Uwa take maka, kayi k'ok'arin saka mata da alkairi tun tana raye domin basai mun fad'a maka ba kasani cewa Uwa bata had'a kowa dakai ba, ka k'ok'arta Khalil, there is nothing wrong in changing 2 a beta person, plz do dat 4 our mother's sake and 4 us ol".........

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now