page 3

2K 100 1
                                    

*NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

                🌱 *3* 🌱

Tad'an jujjuya wuyanta alamun tanaso taji idan kanta yana nan daidai, don azahirin gaskiya tasha uban mari.
Murmushi tayi tace "Ni ka mara?" Ta fad'i haka tana mai girgiza kai.

Zuwa caan bayan data lumfasa aiko ta d'aga hannu zata sharara masa mari Yawale ya dakatar da ita ta hanyar rik'e hannun.

"Haba Maijiddah bansanki da haka ba, koba komai Khalil ya girme ki sosai ya cancanci girmamawa daga gareki, daga yau inaso ko maida magana karki k'ara yi masa".

Habaaa ai kafin ya rufe baki tace "kam!! Baba me kace? Aiko kasan halina tsaf ciki da bai, wlh Baba bazan girmama wanda besan girma ba, wannan iccen har mutun ne?" Ta fad'i haka tana mai nuna Khalil da hannu tun daga sama har k'asa.

Sannan ta cigaba da cewa "Wallahi Wallahi Wallahi kaji na rantse sai kasan wa ka mara, kan uba, to aini a tarihin rayuwata ban tab'a cin karo da wanda ya mugun ciman fuska irinka ba"

Bud'ar bakin Khalil sai cewa yayi "kad'an kika gani indai nine (idiot, Village girl kawai)".

Maijiddah tace "uhhmm to gal d'in ni ina ruwana, kai kasan wannan ni abunda nasani shine saika tantance aya da tsakuwa domin niba kanwar lasa bace".

Khalil yaja wani mugun tsaki ya koma cikin gida. yana wucewa tace "kutumarr..... Wallahi Baba saina rama", Yawale zeyi magana tayi gaba itama ta shige ciki.

Shikam yau yaga (haza) donko ya d'auko masu annoba don yasan halin y'arsa sarai.

Khalil ya shiga d'aki yanata k'unk'unai yana zage-zage, "wannan wace iriyar yarinya ce aka kawo mana? Nifa wallahi ina iya kasheta wata rana, y'ar iskar yarinya sai rashin kunya, isa da gadara sai kace gidan ubanta, aiko zan koya mata hankali" maganar da yayita yi shi kad'ai kenan.

A b'angaren Maijiddah ma hakanne.

"Allah wannan mutunen idan shi d'an iska ne zan nuna masa ya had'u da y'ar tasha, shid'in banza arzikinsu na banza, ni ina ruwana da kud'insu ko d'an k'aruna ne ubansa babu abunda yasha min kai, ai ba rawa sukayi Allah ya basu ba, kuma niba sakarai bace wallahi saidai na koma k'auye amma gidannan bazan yadda wani ya takani ba saboda nima mutunce, aiki suka ce inzo inyi bawai nazo a rik'a juyani kamar waina ba" itama kunji irin nata bayanin.

*****************

"Ke bakisan ana yiman shara bane duk safiya?" Khalil ya tambayi Maijiddah yayin daya ganta tana gyaran parlour.

Maijiddah ko kallon inda yake bata yiba tace "au ai bansan mata aka auro maka ba sai yau, lallai ko d'akinka ze zama bola"

"(God forbid, wife? who? you?) Lallai kina hauka ya kamata kije asibitin mahaukata a duba ki.

"(🤣🤣🤣) to ai kaine mahaukacin bani ba tunda nace maka yaren da kake bansan shi ba, kaga ko ka shekara kanayi saidai kayi a banza, sannan d'akinka ka shirya nema masa mai gyara ta musamman amma ba Maijiddah ba".

"Na lura baki da kunya amma zan gyara miki zama" inji Khalil.

Wata iriyar shewa Maijiddah tayi tace "tabd'i kaji wai shege keyi sa mai zina, rashin kunya ai sammin kayi kad'an daga cikin taka, kuma ni zamana daidai nayisa baya da buk'atar gyara, idan kuma zaman kakeso ka gyara da gaske kaje ka fara gyara naka".

Khalil kam ya tsani Maijiddah kamar yadda ta tsane shi, idan so samu ne, to lallai zeso ya bud'e ido yaga ta had'a yanata-yanata tabar gidan amma da kamar wuya gurguwa da auren nesa, dukda dai itama wasu abubuwan tana had'awa da gayya ne don a maidata gida.

Tsaki ya sake ja kamar yadda ya saba ya wuce ya bata wuri.

Itako ta cigaba da aikinta, tanayi tana wak'a.

*****************

Washe garin ranar.

Khalil ya shigo d'akin Hajiya Uwa, tasha tabarau tana karanta jarida, ko sallama beyi ba ya fara masifa.

"Wai Uwa dan girman Allah meye na d'auko yarinyarnan ne? Ni na tsaneta duk tabi ta raina mutane bata ganin girman kowa, gaskiya tazo tabar gidan nan"

Hajiya Uwa tace "babu inda zataje, marar mutunci duk wa ya ja inba kai ba, mun kusa shekara babu mai aiki gidan nan kuma duk don saboda halinka, duk inda mukaje neman me aiki sai anje an zigesu, kokuma da sunzo sau d'aya basu sake dawowa, duk don fitsara irin taka, ina sane da laifukanka sharewa kawai nake don naga kowa ya juya maka baya amma nasan abunda kake baka kyautawa, idan zaka natsu ka natsu kaji ko? Nan da kazo kanamin magana saman kai so kake naje na koreta? Idan na koreta sai na cigaba dayi maku aikin gidan ko? Wallahi ka fita a idona in rufe Auta kaji na fad'a maka"

Hajiya Uwa tayi masa tatas, ya juya ya fice yana maganganu k'asa-k'asa.

**********

"Zo kije kikai markad'en gyad'ar nan Maijiddah, muyi kunun gyad'a da soyayyar doya yau, ina fatan kina lura da duk yadda nake wasu abubuwan, dakuma yadda nake kunna kayayyakin aikin?" Inji Hajiya Uwa.

Majiddah tace "Eh ina ganewa, ina ne gidan da ake markad'en?" Ta tambaya.

"Kinga idan kika fita titin gidannan sai kiyi hannun damarki, ki mik'e sosai kafin kisha kwana zakiga wani gida me gate (k'ofa) ruwan k'asa nan zaki shiga, kiyi sauri don Allah saboda inaso mu gama da wuri akwai inda zanje"

Bud'ar bakin Maijiddah sai cewa tayi "ai kiyi tafiyarki kawai Hajiya zanyi komai"

Hajiya Uwa batasan sanda dariya ta kufce mata ba, don lallai tasan idan har ta barma Maijiddah girkinnan za'aci abinci mai shegen dad'i.
A fili ko sai tace "a'a ba damuwa kedai jekiyo markad'en ki dawo"

Maijiddah ta amsa da "to".

***********

Tunda Maijiddah ta mik'e hanya bata tsaya ba kamar yadda Uwa tayi mata kwatance, saida tazo daidai wani gida mai gate ruwan k'asa aiko taci burki nan, gidan ya fitinu har yafi gidansu Khalil kyau.

Ta rik'a k'wank'wasawa da k'arfin gaske hada d'aukar gwangwarmemen dutse, sai karnuka ke haushi amma ko a jikinta.

Maigadin gidan ya bud'e ransa b'ace don ba'a tab'a masu irin wannan knocking d'inba asali ma basuyin bak'i hakanan saidai su yo waya, ansan da zuwansu.

Ga mamakinsa sai yaga halitta tsaye tasha kayanta daban-daban da koren slippers ga wata y'ar iskar Hijabi duk d'inkin zare da allura, yace "haba ai wallahi inajin k'wank'wasawar nasan bamu bane sune"

"Su suwa" Maijiddah ta tambaya.

"K'auyawa mana, wama kike nema ne? Don ni shekara aru-aru ina aiki gidannan ban tab'a ganin masu kamanninki sunzo nan ba"

Maijiddah ta kallesa sama da k'asa tace "ooowooo sai masu kamanninka ko? Sannu babban d'an sarauniyar ingila, dallah malam bani wuri in wuce ni markad'e na kawo, ba mamaki shiyasa Allah ya barka haka, fuska kamar an latse dawo", ta wani bankad'e shi tayo ciki, aiko karnuka sukayo mata caaa saida maigadin ya kora su.

Yace "ke wai ke mahaukaciyar ina ce ne? Wannan gidan yayi miki kama da gidan da ake markad'e?

Maijiddah tace "gidan sana'a daman har kama gareshi? Nidai ai nan akayiman kwatance kuma gani a ciki"

"To banan bane ba'a markad'e anan gidan, da kinsan mai gidan ma wata k'ila da sai kin kwanta k'asa kina bashi hakuri don cin fuska ne ace kamar shi ana markad'e gidansa" maigadin ya fad'i haka.

Maijiddah tace "yanzu kayi magana amma da ka tsaya kana surutu, bakasan daka fad'a saina mayar ba?"

Nandai ya nuna mata wani gida gabansu yace ta shiga k'ila nanne, ya samu ya rabu da k'aya.

Taci sa'a ko gidanne, ta shiga babbar d'iyar matar gidan itace ta karb'i markad'en tanayi mata, bata wuce sa'arta ba.

Kunsan mata da saurin sabo, nanfa suka hau fira, har aka gama markad'en da jimawa tana nan tana zuba kamar kanya mai y'ay'a.

Nanfa yarinyar mai suna MARIYA bayan da taji cewa Maijiddah daga gidan Alhaji Abdullahi take, tahau bata labari.............

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now